Khairat Abdulrazaq-Gwadabe
Khairat Abdulrazaq-Gwadabe, (An haife ta a shekara ta alif dari tara da hamsin da bakwai, 1957) an kuma zabe ta a matsayin Sanata na yankin babban birnin Tarayyar Abuja,a Nijeriya a farkon Jamhuriya ta hudu ta Nijeriya,yar Jam’iyyar Democratic Party (PDP) ce. Ta rike ofis daga watan Mayu shekarar 1999 zuwa watan Mayu shekarar 2003.[1]
Khairat Abdulrazaq-Gwadabe | |||
---|---|---|---|
Mayu 1999 - Mayu 2003 ← Isah Maina District: FCT Senatorial District | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Ilorin, ga Afirilu, 1962 (62 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Yarbanci | ||
Ƴan uwa | |||
Abokiyar zama | Lawan Gwadabe | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Jami'ar jahar Lagos University of Buckingham (en) | ||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Khairat kanwa ce ga Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq kuma matar Kanar Lawan Gwadabe, tsohon gwamnan mulkin soja a jihar Neja.[2]
An haifi Khairat a garin Ilorin a watan Afrilun shekarar 1957.[3] Ta yi karatun lauya a Jami'ar Buckingham.[4] Bayan ta hau kan kujerar ta a majalisar dattijai an nada ta kwamitocin kan Muhalli, Lafiya, Harkokin Mata (shugaban), Hadin Tarayya, Yawon Bude Ido da Al'adu na Babban Birnin Tarayya. Ta kuma kasance memba na Kwamitin Binciken Kwastam da Haraji.[5]
Khairat ta kasance Yar takara a jamiyyar PDP a zaben sanata a shekarar 2003, to kuma amma ta fadi a zaben fidda gwani. Wannan na iya faruwa ne saboda goyon bayan da ta nuna a baya ga yunkurin tsige Shugaba Olusegun Obasanjo . A watan Janairun shekaran 2003 ta bayyana cewa ta koma jam'iyyar All Nigeria People's Party (ANPP) saboda rashin adalci da PDP ta nuna ma ta. kuma ta kasance daya daga cikin shahararrun mata yan siya na farko a Najeriya da kuma arewacin Nijeriya.[6]
A watan Agusta shekarar 2005, shekaru shida bayan aure, Abdulrazaq-Gwadabe ta haifi danta na fari, a wani asibiti a Miami, Florida, Amurka. Tana da shekaru 48. Mahaifin sabon jaririn, Kanar Lawan Gwadabe, ya kasance tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Neja.[7] Ya zuwa watan Disambar a shekarar 2011, Sanata Abdulrazaq-Gwadabe shi ne shugaban Majalisar Dattawa, ta inda tsofaffin sanatoci da masu ci suke raba iliminsu da gogewarsu.[8]
Manazartai
gyara sashe- ↑ "FEDERAL REPUBLIC OF NIGERIA LEGISLATIVE ELECTION OF 20 FEBRUARY AND 7 MARCH 1999". Psephos. Retrieved 2010-06-18.
- ↑ "All Governor AbdulRazaq's Men". The Informant247 News (in Turanci). 2021-02-24. Retrieved 2021-03-30.
- ↑ "What Manner of Lawmakers". ThisDay. 2001-12-08. Archived from the original on 2005-11-29. Retrieved 2010-06-18.
- ↑ Oma Djebah, Louis Achi and Utibe Uko. "2003: National Lawmakers Who Won't Return". ThisDay. Archived from the original on 2010-09-08. Retrieved 2010-06-18.
- ↑ Oma Djebah, Louis Achi and Utibe Uko. "2003: National Lawmakers Who Won't Return". ThisDay. Archived from the original on 2010-09-08. Retrieved 2010-06-18.
- ↑ Bature Umar (2003-01-27). "Senate: PDP's Loss, Other Parties' Gain". ThisDay. Archived from the original on 2010-09-08. Retrieved 2010-06-18.
- ↑ "Miracle Baby for Ex-Senator". ThisDay. 2005-08-30. Retrieved 2010-06-18.[permanent dead link]
- ↑ "MARK TASKS SENATOR'S FORUM ON NATION BUILDING". News Agency of Nigeria. December 18, 2011. Archived from the original on March 15, 2013. Retrieved 2012-07-18.