Kayode Olofin-Moyin (an haife shi ranar 13 ga watan Mayu, 1950) a jihar Ekiti. Tsohon jami'in soja ruwa ne.

Kayode Olofin-Moyin
Gwamnan jahar ogun

ga Augusta, 1998 - 29 Mayu 1999
Sam Ewang (en) Fassara - Olusegun Osoba
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Makaranta Jami'ar Tsaron Nijeriya
National Defence College, Nigeria (en) Fassara
Harsuna Turanci
Yarbanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da soja

Rayuwar farko gyara sashe

An haifi Kyaftin Navy Kayode Olofin-moyin a Ilawe-Ekiti, Jihar Ekiti, a ranar 13 ga Mayu, 1950.[1]

Karatu gyara sashe

Bayan kammala karatunsa na firamare, ya shiga makarantar Annunciation Catholic School, Ikere-Ekiti a shekarar 1965. Ya kammala a shekarar 1969 tare da kyakykyawar takardar shedar west african examinations council (WAEC).

Ya samu gurbin shiga makarantar horas da sojoji ta Najeriya a shekarar 1971 a matsayin dalibi kuma ya samu nasarar kammala kwas dinsa a watan Disamba 1972 sannan ya samu aikin sojan ruwan Najeriya. Bayan haka, ya ci gaba da samun ƙarin horo. ya bar Makarantar Sojoji ta Najeriya a watan Disamba 1972, lokacin da ya fara kwas a Midshipman a cikin jirgin NNS OBUMA (Tsohon NNS NIGERIA). Ya kammala horonsa a watan Oktoba 1973 [2]

Aikin soja gyara sashe

Kyaftin Navy Olofin-Moyin ya wuce babbar kwalejin Command and Staff College, Jaji a 1985, ya kammala a 1986. Daga nan ya halarci Kwalejin Yaki ta Kasa da ke Abuja tsakanin 1997 zuwa 1998.

Kyaftin navy Olofin-Moyin yafara ne a hankali. Daga Cadet a 1972, an ba shi matsayi na Midshipman a 1973; Karamin Laftanar (1973 – 1977); Laftanar (1977 - 1981); Laftanar Kwamanda (1981 - 1988); Kwamanda (1988 - 1994) da Kyaftin Navy (1994)

Wasu daga cikin Naɗin nasa sun hada da,

Commanding Officer, NNS HADEJIA (Patrol Boat), (1978 – 1979); Commanding Officer, NNS RUWAN YARO (Cadets Training Ship), (1984 – 1985); Commanding Officer, NNS ENYIMIRI (A Corvette on ECOMOG Operation), Liberia, (1992 – 1993) and Commanding Officer, Naval Air Station, (1996 – 1997).[3]

Kyaftin Navy Olofin-Moyin ya kuma gudanar da nadin ma'aikata kamar Jami'in Ma'aikata (Aiki), Rundunar Sojojin Ruwa ta Yamma (1986 - 1988); Base Commander, Nigerian Naval College, Onura, Port Hacourt (1990 – 1992); Babban Hafsan Sojan Ruwa, ECOMOG, Laberiya (1994 – 1995) da Daraktan Ayyuka, Hedikwatar Sojojin Ruwa, Legas (1995 – 1996).

Gwamnan Jihar Ogun gyara sashe

An naɗa Kayode Olofin-Moyin a matsayin shugaban mulkin soja a jihar Ogun ta Najeriya daga watan Agusta 1998 zuwa Mayu 1999 a lokacin mulkin Janar Abdulsalami Abubakar na rikon kwarya, inda ya mika mulki ga zababben gwamna Olusegun Osoba a farkon jamhuriya ta hudu ta Najeriya. Ya gina sabon masaukin gwamna a jihar Ogun, wanda aka bude ranar 27 ga Afrilu 1999 kafin mikawa gwamnan farar hula.

A watan Nuwamba 2002 gidansa da ke Victoria Island, Legas ya yi gobara.[4]

Manazarta gyara sashe

  1. https://military-history.fandom.com/wiki/Kayode_Olofin-Moyin
  2. https://guardian.ng/news/skewed-security-formation-responsible-for-herders-killings-says-olofin-moyin/
  3. https://www.wikiwand.com/en/Kayode_Olofin-Moyin
  4. https://archive.ogunstate.gov.ng/ogun-state/governors/kayode-olofin/ Archived 2022-08-08 at the Wayback Machine