Ibrahim Kazaure
Ibrahim Kazaure (an haife shi ranar 12 ga Nuwamba 1954) sanata ne a jamhuriya ta uku kuma jakadan Najeriya a kasar Saudiyya wanda ya kasance ministan kwadago da samar da ayyukan yi ta tarayya a takaice a shekarar 2010.[1]
Ibrahim Kazaure | |||
---|---|---|---|
10 ga Faburairu, 2010 - 17 ga Maris, 2010 ← Adetokunbo Kayode - Chukwuemeka Ngozichineke Wogu (en) → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Jihar Jigawa, 12 Nuwamba, 1954 (70 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Ƙabila | Hausawa | ||
Harshen uwa | Hausa | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da Mai wanzar da zaman lafiya |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Kazaure a jihar Jigawa a ranar 12 ga watan Nuwamba 1954, kuma ya sami takardar shaidar difloma ta kasa a fannin gine-gine da injiniyan farar hula.
Ayyuka da Siyasa
gyara sasheYa zama kwamishinan ilimi a jihar Kano a shekarar 1983. An zabe shi a matsayin ɗan majalisar dattawa a jamhuriya ta uku ta Najeriya, inda ya zama mai rinjaye. Ya kasance Jakadan Najeriya a Saudiyya tsakanin 2003 zuwa 2007.[2]
Shugaba Umaru 'Yar'adua ne ya naɗa shi ministan ayyuka na musamman a watan Disambar 2008.[3] An naɗa shi Ministan Kwadago da Ƙarfafawa a ranar 10 ga Fabrairun 2010, lokacin da muƙaddashin shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya mayar da Adetokunbo Kayode zuwa ma’aikatar shari’a.[4] Ya bar mulki a ranar 17 ga Maris 2010 lokacin da mukaddashin shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya rusa majalisar ministocinsa.[5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "How old is Ibrahim Kazaure". HowOld.co (in Turanci). Archived from the original on 4 December 2022. Retrieved 24 May 2020.
- ↑ OLAYINKA OYEBODE (2 December 2008). "Cabinet list: A president's search for the magic team". The Punch. Retrieved 14 April 2010.[permanent dead link]
- ↑ Abdul-Rahman Abubakar and Turaki A. Hassan (21 November 2008). "Senate Grills Akunyili, Ndanusa – Bilbis, Kazaure Have Easy Time".
- ↑ Okey Muogbo, Lanre Adewole and Taiwo Adisa. "Jonathan redeploys Aondoakaa: •Adetokunbo Kayode named new AGF •Police storm ex-AGF's office •Yar'Adua's kitchen cabinet in disarray". Tribune. Archived from the original on 19 April 2010. Retrieved 13 April 2010.
- ↑ Daniel Idonor (17 March 2010). "Jonathan Sacks Ministers". Vanguard. Retrieved 14 April 2010.