Himalaya
Himalaya wani yankin tsaunuka ne dake a nahiyar Asiya. Karshen Himalaya daga yamma yana a kasar Pakistan. Tsaunukan sun shiga ne ta Jammu da Kashmir, Himachal Pradesh , Uttaranchal, Sikkim da Arunachal Pradesh a yankin Kasar Indiya, Nepal , da Bhutan. Karshen sa daga gabashi yaje har Tibet. Sun rabu zuwa yankuna 3 Himadri, Himachal da Shiwaliks. Tsaunuka 15 mafiya tsawo a duniya na a Himilaya. Daga ciki akwai tsaunukan Mount Everest, K2 , Annapurna, da Nanga Parbat . Mount Everest shine mafi tsawon tsauni a duniya da tsawon mita 8,849. Daga cikin dogayen tsaunuka kuma mafiya tsayi a duniya Tara na a yankin Himalayan Nepal. Kalmar "Himalaya" na nufin gidan kankara da yaren Sanskrit, tsohon yaren Indiya. Tsaunukan Himalaya sune suka raba al'adun Sinawa da Indiyawa na tsawon lokaci. Da yaren Sanskrit, tsohon yaren Indiya. Tsaunukan Himalaya sune suka raba,wanda yagano himalayas a shekarar Alib1733,Shine wani masanin yanayin da yasha fa Duniya(Jean-Baptiste),Dan kasar francar ne,Save Open… Zoom image… 179x127 4.4 kB JPEG.
Himalaya | |
---|---|
General information | |
Gu mafi tsayi | Mount Everest (en) |
Height above mean sea level (en) | 8,848.86 m |
Tsawo | 2,400 km |
Fadi | 250 km |
Yawan fili | 600,000 km² |
Labarin ƙasa | |
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa | 29°N 84°E / 29°N 84°E |
Bangare na |
Alpide belt (en) Larger Himalaya (en) |
Kasa | Nepal, Myanmar, Sin, Pakistan, Indiya, Afghanistan da Bhutan |
Geology | |
Period (en) | Eocene (en) |
Gandun daji
gyara sasheHimalaya waje ne da yayi kaurin suna sosai a tsakankanin yan yawon bude ido da shakatawa sabo da albarkar yanayin da ke akwai na gandun daji. daga cikin tsirrai da bishiyoyin dake akwai sun hada da Oak, Pine, Fir, Rhododendron , Birch, Juniper,da Deodar. Ire iren dabbobin da ke akwai a sassan dazuzzukan Himalaya sun hada da damusa, Shidiyar Tinkiya, Giwa, Kada da Kura. A yankin kudancin Himalaya kinda akwai yanayin Sanyi sosai, dabbobi basu cika zama a wuraren ba. Haka kuna su wadanda ma keep rayuwa a wuraren, lokacin sanyi sukanyi hijira zuwa yankunan da kuma sanyin ke da sauki. Wasu daga cikin guraren gandun daji masu jan hankali
- Jim Corbett National Park
- Namdhpha National Park
- The Royal Chitwan Park
- Kaziranga National Park
- Royal Bardia National Park
- Great Himalayan National Park
Hotuna
gyara sashe-
Sahara mai sanyi a arewacin Sikkim, Himalaya
-
Tsaunin Makalu (tsayin mita 8,463), Himalaya
-
Tsaunin Cho Oyu (tsayin mita 8,201), Himalaya
-
Nau'in Angulu da ake samu a yankin Himalaya
-
Kogin Palpa, Kali Gandaki, da ke a yankin Himalaya
-
Wasu matafiya a yankin mai cike da tsaunuka na Himalaya
-
Kogin Gokyo, Nepal Himalaya