Hijabi kalmace wacce aka arota daga larabci wato hijab, ma'ana (rufe abu) Hijab ko kuma Hijabi da Hausa kenan, kalmar hijab a larabci tana nufin kariya ko tsari ko shamaki ko kuma suturcewa. Amma a sharia'a duk wata sutura da mace zata yi amfani da ita don rufe baki ɗayan jikinta yayin fita ko kuma ganawa da wanda ba muharraminta ba. Ko Kuma Hijabi wata suturace wadda matan Musulmi suke amfani dashi don suturta baki ɗayan jikinsu, sai dai fuska da tafin hannun su. Shi kuma sanya hijabi wajibi ne ga ko wace Musulma balagaggiya, koda bata balaga ba idan takai wani lokaci yakan zama wajibi a gareta idan zata fita daga gida ta sanya hijabi, domin suturta jikin ta.[1] Koda a cikin gida ne zata sanya hijabi indai har wanda ba muharraminta zai shigo kuma zai ganta, ko kuma suna a gidan haya misali dole ƴa mace tasan kalan shiga da zata rinƙa yi acikin gidansu. Sanya hijabi da wajibi ne ba wai ra'ayi bane, Allah ne da kanshi ya wajabta wa matan Musulmi sanya shi.[2]

Hijab
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na Gyele
Facet of (en) Fassara hijab (en) Fassara
IPA transcription (en) Fassara ħi.d͡ʒaːb
Hashtag (en) Fassara hijab da hijabi
Amfani wajen hijabi (en) Fassara
hausawa sanye da hijabi
File:Female hijab in Islam.jpg
hijab
hijab
matan musulmi sanye da hijabi
hijab da niqab

Tabbas Hijabi wajibi ne ga ko wace Musulma kuma a ko wane zamani ne,[3] saboda haka ƴan'uwa mata musamman ƴan'mata da zawarawa da matan Aure da duk wata Musulma balagaggiya mai hankali sai ku kula hijabi ba ado bane a'a addini ne ya zo dashi, Allah shine ya wajabta maku shi kada ku biye zamani ku halaka,[4] wata babbar fitina da mata suke gani kamar ba komai bace, itace barin gashin kansu a waje, kisani idan kika bar gashin kanki a waje kika fita ko kika bari ajnabiyyin ki ya gani kina cikin azabar Allah sai dai idan kin tuba.

Sai kuma ƴa'nuwa mata ku sani gyalen da kuke lulluɓi dashi baya zama hijabi har sai ya rufe baki ɗayan jikinku kuma ba wanda yake yara-yara ba. Iyayemmu mata kuji tsoron Allah kubi abinda addinin ku ya koyar daku kuma kuyi wa Allah da Manzonsa ɗa'a, ku kuma koyawa ƴaƴan ku mata sanya hijabi tun suna ƙanana, Muma maza muji tsoron Allah mu sani cewa hijabi wajibi ne ga matanmu da ƴaƴanmu da ƙannemmu saboda haka kar mu hanasu sawa saboda namu ra'ayin, duk wanda yayi hakan to ya sani yana fito-na-fito da hukuncin Alqur'ani da hadisi wato da Allah da Manzonsa yake fito-na-fito kenan, maimakon haka sai mu dage mu matsawa matanmu sanya hijabi. Allah na nake roko da ya shiryar damu baki ɗaya ya bamu ikon bin dokokin sa. Allah shine masani.

Hotuna gyara sashe

Manazarta gyara sashe