Mata a musulunci suna da matukar daraja da kima a musulunci. wannan ne ya sa har (Allah SWT) ya saukar da Surah guda acikin littafi mai tsarki AlQur'ani wacce ta yi bayani dangane da sha'anin mata wato ; SURATUN-NISAA'I ma'ana: surar da ke magana kan sha'anin mata.

Mata a musulunchi
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na gender role (en) Fassara da female topic (en) Fassara
Amfani Good works in Islam (en) Fassara, Nikah da Polygamy in Islam (en) Fassara
Facet of (en) Fassara women and religion (en) Fassara
Significant person (en) Fassara Khadija Yar Khuwailid, Fatima da Maryam a Musulunci
Sana'a Ibadah (en) Fassara, Work in Islam (en) Fassara da Ilimi a Musulunci
Addini Musulunci da Sufiyya
Bisa women in the Qur'an (en) Fassara
Ta jiki ma'amala da Islam and children (en) Fassara da gender segregation and Islam (en) Fassara
Alaƙanta da Orientation of children in Islam (en) Fassara da parenting (en) Fassara
Abu mai amfani Islamic clothing (en) Fassara, Tasattur (en) Fassara da Hijab
Kiyaye ta God in Islam (en) Fassara
Including (en) Fassara ritual purity in Islam (en) Fassara, hayd (en) Fassara, Nifas (en) Fassara da Istihadha (en) Fassara

Tarihi gyara sashe

Kafin zuwan musulunchi mata sun kasance basu da wata kima a wajen mutane Kuma basu da wani 'yanci. Kafin zuwan musulunchi mutane suna kyamar mata matuka wannan ne yasa mutum baya son a haifar mishi jaririya mace idan an haifeta zai je ya haka rami ya binne ta da ranta. Kuma dai a wancen lokacin mata basu da wani hakki face yanda aka yi da su, basu da rabon gado saidai ma a gajesu Kamar wasu dawaki.

Da zuwan musulunchi mata suka Sami 'yanci suka zama 'yan gata ababan girmamawa ta yanda Allah ya dora nauyin kula da su daya hada da Ciyarwa,muhalli,Tufatarwa,kare lafiya, ilimantarwa, kyautatawa, da dai sauransu a kan mazaje. Musulunchi ya ba mata dukkan hakkin daya kamata a ba su hadi da kyautatawa ba tare da tozarta rayuwarsu ba. Musulunchi ya dora nauyin kula da mace a kan iyayenta lokacin da take karama, daga lokacin da ta girma ta yi aure to nauyin ya koma kan mijin daya aureta, da zaran Kuma ta tsufa to dole ne 'ya'yanta da mijinta su kula da rayuwarta. Musulunchi ya ba mata damar su gaji duniyar da iyayensu ko mazajensu suka mutu suka bari Kamar yanda addinin musulunchi ya tsara. Babu wani addini da ya girmama mata Kamar musulunchi domin kuwa shi ne addinin daya daukewa mata dukkan wahal-halun rayuwa na Neman abinci ko abinda Ya yi kama da haka, ya dora nauyin a kan maza su kuma mata aka ba su damar su zauna su huta Mike kafa a yi musu komai.

Manazarta gyara sashe