Hauwa Maina
Hauwa MainaMaina, Marigayiyar tsohuwar ’yar fim ce kuma furodusa ce, an haife ta ne a garin Biu da ke Jihar Borno. Ƴar wasan kwaikwayo ce a Hausa fim. Hauwa Maina ta fara fim ne a shekarata alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa'in da takwas (1998). Ba ta da sha'awar yin wasan kai tsaye.
Hauwa Maina | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jihar Borno, |
ƙasa | Najeriya |
Mutuwa | jahar Kano, 2 Mayu 2018 |
Karatu | |
Makaranta | Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna |
Harsuna |
Turanci Hausa |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi da producer (en) |
Tarihin rayuwa
gyara sasheAn haifeta a garin kaduna, Amma asalin ta ta fito daga garin biu dake Jihar Borno, Najeriya.
Ta kammala karatunta a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kaduna, inda ta karanci fannin Ma’aikata.[ana buƙatar hujja] [1]Bayan samun difloma na ƙasa, Hauwa ta yanke shawarar aiki a matsayin 'yanci. Hakan ya kasance kafin ta haɓaka sha'awar zane-zane da wasan kwaikwayo. Tana da mutum na musamman da za ta gode wa saboda yadda ta ba ta aikin wasan kwaikwayo ta turawa,sanan jarumar yar kabilar pabur ne[2]
Aure
gyara sasheJarumar tayi aure tana da yarinya mace me suna ahalan, tayi aure da yaro ɗaya kafin rasuwar mahaifiyar ta.
Sana'ar fim
gyara sasheHauwa Maina, ta shiga masana'antar fim tun a shekarar 1998 zuwa 1999. Inda ta fara da wani fim mai suna "TUBA" a matsayin jaruma, kuma a mafi yawan fina-finan ta, ta fi mayar da hankali ga bangaren da ke nuna jajircewar diya mace.
Fim ɗin ta na farko shine Tuba, sai ta fito a fim ɗin bayajidda-wani fim na tarihi da ake amfani da shi wajen koyar da yara a makaranta a yau.[3]
Tana da kamfanin kashin kanta, kamfanin mai suna Ma'inta Enterprises Limited kuma kamfanin ya shirya fina-finai da suka haɗa da Gwaska, Sarauniya Amina da sauran su.[4][5][6]
Fina-fina
gyara sashe- Tuba
- Queen Amina of Zazzau[5]
- Bayajida
- Sarauniya Amina
- Gwaska
- Maina
- Dawo dawo. Da sauran su
Nominations and awards
gyara sasheMutuwa
gyara sasheA ranar Laraba 2 ga watan Mayu, shekarar 2018 ne Hauwa Maina ta rasu a asibiti a Kano bayan doguwar rashin lafiya.[8][9] ta fara kwanciya a asibitin Dake Kano ,ta shafe wata uku tana jinya sannan Anan ta rasu, anyi Jana,Izar jarumar a ranar alhamis a mahaifarta watau jihar Kaduna, Sannan ta rasu tana da shekara hamsin a duniya[10]
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ https://www.bbc.com/hausa/labarai-43996281
- ↑ https://www.bbc.com/hausa/labarai-43996281
- ↑ Liman, Abubakar Aliyu (5 September 2019). "Memorializing a Legendary Figure: Bajajidda the Prince of Bagdad in Hausa Land". Afrika Focus. 32 (1). doi:10.21825/af.v32i1.11787.
- ↑ Blueprint (2014-03-24). "We want to tell our African stories in Hausa movies – Hauwa Maina". Blueprint (in Turanci). Blueprint Newspapers Limited. Retrieved 2022-08-05.
- ↑ 5.0 5.1 "Hail of tributes trail late Hauwa Maina, Kannywood celebrated actress". Vanguard News (in Turanci). 2018-05-04. Retrieved 2022-08-05.
- ↑ 6.0 6.1 Edubi, Omotayo (2018-05-03). "Kannywood actress, Hauwa Maina, is dead". The Sun Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-08-05.
- ↑ "Kannywood actress Hauwa Maina is dead". TheCable Lifestyle (in Turanci). 2018-05-03. Retrieved 2022-08-05.
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/entertainment/kannywood/266989-breaking-kannywood-actress-hauwa-maina-is-dead.html
- ↑ Lere, Mohammed (2018-05-02). "Kannywood actress, Hauwa Maina, is dead". Premium Times Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-08-05.
- ↑ https://www.bbc.com/hausa/labarai-43998583