Halima Atete
Halima Yusuf Atete Wacce akafi sani da Halima Atete (An haife ta ne a ranar 26 ga watan Nuwamba a shekara ta alif 1988) ƴar asalin jihar Borno ce dake Maiduguri,[1] shaharariyar yar wasan Hausa ce kuma mai tsara finafinai, wanda mafiya yawan fina finanta takan fito ne a fim na Annamimanci ko Kishi.[2]
Halima Atete | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Halima Atete |
Haihuwa | Maiduguri, 26 Nuwamba, 1988 (36 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan wasan kwaikwayo da jarumi |
Farkon rayuwa
gyara sasheAn haifi Halima Atete a ranar 26 ga watan Nuwanba a shekara ta 1988, a garin Maiduguri dake Jihar Borno a Najeriya.
Halima Atete tayi makarantar firamari ta, Maigari Primary School, sanan tatafi makarantar gwabnati ta Yerawa Government Secondary School. Jarumar bata tsaya a iya nan ba ta wuce makarantar gaba da sakandare inda ta samo kwalin National Diploma a Shari’a and Civil Law.
Sana'ar Fim
gyara sasheTauraruwar ta shiga kamfanin shirya Finafinan Hausa dake Kano a Shekara ta 2012,[3] yayin da ta fara shirya Fim ɗin ta na farako mai suna Asalina da uwar gulma[4]. Jarumar ta fito a Finafinai sama da guda Ɗari da Sittin (160).
Fina-finai
gyara sasheGa wasu daga cikin finafinan ta;
Suna | Shekara |
---|---|
Wata Hudu | ND |
Yaudarar Zuciya | ND |
Asalina (My Origin) | 2012 |
Kona Gari | 2012 |
Dakin Amarya | 2013 |
Matar Jami’a | 2013 |
Wata Rayuwa | 2013 |
Ashabu Kahfi | 2014 |
Ba’asi | 2014 |
Bikin Yar Gata | 2014 |
Maidalilin Aure | 2014 |
Soyayya Da Shakuwa | 2014 |
Alkalin Kauye | 2015 |
Bani Bake | 2015 |
Kurman Kallo | 2015 |
Uwar Gulma (Mother of Gossip) | 2015 |
Mu’amalat | 2016 |
Igiyar Zato | 2016 |
Bayan Fage
gyara sasheTana da ra'ayin cewa ba ta taɓa kwanciya da furodusa don a bata role ɗin da zata fito a fim ba.[5]
Kyaututtuka
gyara sasheShekara | Award | Category | Sakamako |
---|---|---|---|
2013 | City People Entertainment Awards | Best New Actress[6] | Lashewa |
2014 | City People Entertainment Awards | Best Supporting Actress[7] | Lashewa |
2017 | African Voice | Best Actress[8] | Ayyanawa |
2017 | City People Entertainment Awards | Best Actress[9] | Lashewa |
2018 | City People Entertainment Awards | Kannywood Face[10] | Lashewa |
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ "Halima Yusuf Atete [HausaFilms.TV - Kannywood, Fina-finai, Hausa Movies, TV and Celebrities]". hausafilms.tv. HausaTV. Retrieved 27 August 2019.
- ↑ Askira, Aliyu (1 December 2014). "It's all gossip; I am not having an affair with Ali Nuhu – Halima Atete". Blueprint. Retrieved 27 August 2019.
- ↑ "Who Is Halima Atete? Biography| Profile| History Of Kannywood Actress Halima Yusuf Atete - Page 2 of 2". Daily Media Nigeria. Daily Media Nigeria. 1 August 2017. Archived from the original on 27 August 2019. Retrieved 27 August 2019.
- ↑ Lere, Muhammad (31 May 2014). "My new film "Uwar Gulma" will be a hit - Halima Ateteh - Premium Times Nigeria". Premium Times. Premium Times. Retrieved 27 August 2019.
- ↑ Blueprint (2022-04-08). "I'll never sleep with producers to get roles – Halima Yusuf Atete". Blueprint Newspapers Limited: Breaking news happening now in Nigeria and todays latest newspaper headlines (in Turanci). Retrieved 2022-07-22.
- ↑ Aiki, Damilare (16 July 2013). "2013 City People Entertainment Awards: First Photos & Full List of Winners". BellaNaija. Retrieved 27 August 2019.
- ↑ Lere, Muhammad (1 January 2015). "Kannywood's finest, worst moments of 2014 - Premium Times Nigeria". Premium Times. Premium Times. Retrieved 27 August 2019.
- ↑ "Seven Kannywood stars to be honoured in London". Daily Trust. Daily Trust. 23 October 2017. Archived from the original on 27 August 2019. Retrieved 27 August 2019.
- ↑ Emmanuel, Daniji (18 October 2017). "Full List Of Winners At The 2017 City People Movie Awards". City People Magazine. Retrieved 27 August 2019.
- ↑ People, City (24 September 2018). "Winners Emerge @ 2018 City People Movie Awards". City People Magazine. Retrieved 27 August 2019.