Harkar Musulunci a Najeriya (Turanci Islamic Movement of Nigeria), kunguyar addini ce wadda Ibrahim Zakzaky ke jagoranta, manufarta shine kafa daular Musulunci a Najeriya. Zakzaky na goyon bayan kasar Iran kuma yayi watsi da hukumar Tarayyar Najeriya.[1] Kungiyar ta kafune akan mai tafiya batare da rikici ba kuma ta kafa Daular Musulunci a Najeriya. Kungiyar nada babban mazaunin ta a Husainiyya Baqiyatullah a garin Zariya, kuma akwai wakilai na kungiyar a ko'ina a Arewacin Najeriya dama wasu sassa na kudancin kasar wanda suka kai kaso 5% zuwa 17% na al'umar Musulmin kasar.[1][2] Babban aikin kungiyar shine koyar da ilimin addini da wayar da kan mabiya. Haka nan Zakzaky na karfafa guiwar mabiyan sa dangane da neman ilimin Boko da kuma aiyukan sadaka.[1] A yanzu shugaban kungiyar Zakzaky na daure a kurkuku, amma mabiyan kungiyar na shirya zanga zanga domin ganin gwamnati ta sake shi. Wanda hakan yasha haddasa rikice rikicen da yayi sanidiyyar rasa rayuka da dama harma da asarar dukiyoyi.

Harkar Musulunci a Najeriya
Bayanai
Shafin yanar gizo islamicmovement.org
taswirar musulmai a kasar

Ranar 26 ga Yuli 2019, Gwamnatin Najeriya ta haramta kungiyar tare da sakata cikin jerin kungiyoyin ta'addanci.[1] Haramcin yazo ne bayan wata zaga zanga da yayan kungiyar sukayi a Abuja wanda yayi sanadiyyar rasa rayukan mutum 11 masu zanga zangar, da dansanda 1 da danjarida 1.[3] Saidai kuma kungiyar tayi watsi da cewar gwamnati nasu yan ta'adda ne, inda sukace gwamnati na afkawa tare da kashe masu zanga zangar lumana ne kawai.[2] Daga cikin rikice rikicen da ya faru ga kungiyar akwai Rikicin Zariya na 2015 wanda fararen hula 348 suka mutu ciki harda yayayen shugaban kungiyar kuma gwamnati ta rushe mazaunin kungiyar na Zariya da makabarta da wajen ibada. Sai kuma Rikicin ranar Qudus a Zariya na 2014 wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 34 shima ciki da yayan shugaban kungiyar 3. Kungiyar kare hakkin musulmai tayi tur da gwamnatin Najeriya.[1] kungiyar kare hakkin dan'adam ta Human Rights Watch tace hakan take hakkin yan kasa ne.[3] Saidai kungiyar bata daina fafutika ba na ganin an saki jagoran nasu, inda suke cigaba da shirya irin wannan zanga zangar harma a shafukansu na yanar gizo.[4]

Sake karanta

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 Okoli, Al Chukwuma (2019-01-05). "ODR: An Islamic Jurisprudence Perspective". Conflict Studies Quarterly (26): 53–67. doi:10.24193/csq.26.4. ISSN 2285-7605.
  2. 2.0 2.1 Tangaza, Haruna Shehu (2019-08-05). "Why Nigeria has banned pro-Iranian Muslim group" (in Turanci). Retrieved 2019-11-07.
  3. 3.0 3.1 "Nigeria: Court Bans Shia Group". Human Rights Watch (in Turanci). 2019-07-30. Retrieved 2019-11-07.
  4. "Welcome to the Official Website of the Islamic Movement in Nigeria". www.islamicmovement.org. Archived from the original on 2019-11-11. Retrieved 2019-11-07.