Harin Kano, 2014

Harin ƴan ta'adda a Kano, Nijeriya

Harin bam a Kano a shekarar 2014 wani harin ta'addanci ne da aka kai ranar 28 ga watan Nuwamba, 2014, a babban masallacin Juma'a na Kano, birni mafi girma a Arewacin Najeriya musamman Musulmi a lokacin da 'yan ta'addar Islama ke tada zaune tsaye a Najeriya. Masallacin yana kusa da fadar Sarkin Kano Muhammad Sanusi II, babban malamin addinin Musulunci na biyu a Najeriya, wanda ya bukaci jama'a da su kare kansu ta hanyar ɗaukar makamai domin yakar 'yan Boko Haram. Wasu ‘yan kuna bakin wake biyu ne suka tarwatsa kansu inda ‘yan bindiga suka bude wuta kan waɗanda ke ƙoƙarin tserewa. Kimanin mutane 120 ne suka mutu sannan wasu 260 suka jikkata.[1][2][3][4]

Infotaula d'esdevenimentHarin Kano, 2014
Map
 12°00′N 8°31′E / 12°N 8.52°E / 12; 8.52
Iri aukuwa
Bangare na Rikicin Boko Haram
Kwanan watan 28 Nuwamba, 2014
Wuri jahar Kano
Ƙasa Najeriya
Nufi Masallaci
Adadin waɗanda suka rasu 120
Adadin waɗanda suka samu raunuka 270

Wai-wa-ye

gyara sashe

A ranar 25 ga watan Nuwamba, wasu mata biyu ‘yan kunar baƙin wake sun kashe sama da mutane 45 a wata kasuwa mai cunkoson jama’a a Maiduguri, jihar Borno.[5] A ranar 27 ga watan Nuwamba, kusan mutane 50 ne mayakan Boko Haram suka kashe a Damasak.[6] An kuma daƙile wani harin bam a kusa da wani masallaci a Maiduguri sa'o'i kafin tashin bam a Kano. An saka wani bam a gefen hanya, wanda ake zargin an dakatar da fashewar sa.

Tashin bam

gyara sashe

Harin ya faru ne a ranar 28 ga watan Nuwamban 2014 a lokacin da ake gudanar da Sallar Juma'a. An tayar da bama-bamai uku a lokacin da aka fara Sallah. A cewar wani ganau, wasu bama-bamai biyu sun tashi ne a tsakar gidan, yayin da na ukun ya kasance a kan wata hanya da ke kusa.[7] Wani ganau ya ce, “Limamin yana shirin fara sallah sai ya hango wani a cikin mota yana ƙoƙarin tilastawa kansa shiga masallaci. Amma da mutane suka tsayar da shi, sai ya tayar da bama-baman. Mutane suka fara gudu."[8] Bayan fashe-fashen ne wasu ‘yan bindiga suka buɗe wuta akan mutane. A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan ƙasar, Emmanuel Ojukwu, fusatattun ’yan bindiga sun kashe ‘yan bindiga huɗu bayan harbe-harbe.[9][10]

Bayan haka

gyara sashe

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi Allah-wadai da hare-haren, ya kuma umurci jami'an tsaron ƙasar da su ƙaddamar da cikakken bincike, kuma kada su bari har sai an zakulo duk wani jami'in ta'addanci da ke zaluntar 'yancin kowane ɗan kasa na rayuwa da mutunci tare da gurfanar da su gaban kuliya.[8] A watan Disambar 2014, shugaban kungiyar Boko Haram ta Najeriya, Abubakar Shekau, ya zargi Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, da kaucewa Musulunci tare da yi masa barazanar kashe shi.[11] [12]

Rahotanni sun bayyana cewa, bisa buƙatar taimako daga Najeriya, Birtaniya na duba yiwuwar aikewa da masu horar da sojoji domin taimakawa sojojin Najeriya wajen daƙile hare-haren ta'addancin ƴan Boko Haram.[13]

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. AFP. "Suicide bombers, gunmen kill 64 at prominent Nigeria mosque". Retrieved 29 November 2014.
  2. "BBC News - Nigeria unrest: Kano mosque attack kills dozens". BBC News. Retrieved 29 November 2014.
  3. Al Jazeera and agencies. "Scores killed in Nigeria mosque blasts". Retrieved 29 November 2014.
  4. "Bombs, gunfire kill 81 at crowded mosque in Nigeria's Kano". Reuters. Retrieved 29 November 2014.
  5. "Northeast Nigeria bus station blast kills 40 people: sources". Reuters. Retrieved 29 November 2014.
  6. "Nigeria's face of terror: Boko Haram spreading fear, blood". Hindustan Times. Archived from the original on 20 March 2015. Retrieved 29 November 2014.
  7. "Triple bomb blasts kill 120 outside Nigeria mosque". The Telegraph UK. Retrieved 29 November 2014.
  8. 8.0 8.1 "Nigeria unrest: President Jonathan condemns mosque attack". BBC. Retrieved 29 November 2014.
  9. Scores killed in mosque attack in Nigerian city of Kano, FRANCE 24 with AFP and REUTERS, 29 November 2014. Archived from the original on 1 December 2014.
  10. "Nigeria attack: Over 100 reportedly dead as bombs, gunmen target crowded mosque in city of Kano". abc.net.au. Retrieved 29 November 2014.
  11. National Post: "Boko Haram kidnaps 191, murders dozens as the group threatens Muslim leader for telling Nigerians to fight back" by Mustapha Muhammad December 18, 2014
  12. Daily Post: "Kano blast: 150 worshipers killed in ‘Sanusi’s Mosque’ after he travelled to Saudi Arabia" by Ameh Comrade Godwin November 29, 2014
  13. "Britain plans more army trainers to help Nigeria fight Boko Haram". The Telegraph UK. Retrieved 29 November 2014.