Halima Tayo Alao
Halima Tayo Alao (an haife ta ne a ranar 6 ga watan Disamban shekarar 1956) tsohuwar mai tsara gine-gine ce 'yar Najeriya, kuma tsohuwar Ministar Muhalli da Gidaje a lokacin gwamnatin Shugaba n kasan Najeriya Umaru ' Yar'Adua .
Halima Tayo Alao | |||||
---|---|---|---|---|---|
26 ga Yuli, 2007 - 29 Oktoba 2008 ← Helen Esuene - John Odey →
2005 - ga Yuli, 2006 | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | 6 Disamba 1956 (68 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
Jami'ar Ahmadu Bello Jami'ar Ilorin | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | Masanin gine-gine da zane da ɗan siyasa |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Halima Tayo Alao a ranar 6 ga Disamban shekarar 1956. Ta samu digiri na biyu a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a 1981 a fannin gine-gine. Ta shiga aikin farar hula na jihar Kwara a shekarata 1982. Ta zama Babban Sakatariya a Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri, Ilorin, Jihar Kwara.[1] Ta samu digiri na biyu a fannin mulki, 2003 daga Jami'ar Ilorin . Daga shekarar 2005 zuwa Yulin 2006, ta kasance Karamar Ministar Lafiya ta Tarayya.[2]
Ayyuka
gyara sasheAlao ya shiga aikin farar hula na jihar Kwara a shekaran ta 1982.[3] Ta zama Babban Sakatare a ma’aikatun Kasa da Gidaje na jihar Kwara, sannan Ayyuka da Sufuri. Kafin wannan lokacin, ita kadai ce Shugaba / Shugaban Karamar Hukumar Ilorin ta Kudu kuma Sakatariyar zartarwa, Hukumar Kula da Mata ta Jihar Kwara. Daga watan Yunin a shekara ta 2005 zuwa wayan Yunin shekara ta 2006, ta kasance Karamar Ministar Ilmi ta Tarayya sannan daga baya, ta zama Karamar Ministar Lafiya ta Tarayya.[4][5]
An nada ta a cikin kwamitin UACN Property Debelopment Company Plc a ranar 13 ga watan Janairu, shekara ta 2010 a matsayin darekta ba zartarwa ba. Ta sauka daga shugabancin hukumar ne a shekara ta 2019 [6]
Ministan Muhalli da Gidaje
gyara sasheAlao ya nada Ministan Muhalli da Gidaje a ranar 26 ga watan Yulin shekara ta 2007 da Shugaba Umaru 'Yar'Adua. [7] amma an kore shi a cikin babban garambawul a majalisar zartarwa a ranar 29 ga watan Oktoba, shekara ta 2008. [8] An ce korar ta biyo bayan ce-ce-ku-cen da ta ke yi da Chuka Odom, karamin minista kuma wakiliyar jam'iyyar Progressive Peoples Alliance . [9] Wanda ya maye gurbinta shi ne John Odey, wanda aka nada a ranar 17 ga watan Disamba shekara ta 2008. [10]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Aziken, Emmanuel (8 July 2005). "Ezekwesili, Mimiko, 10 others on new cabinet list". OnlineNigeria Daily News. Archived from the originalon 3 March 2016. Retrieved 16 December 2009.
- ↑ Emmanuel Aziken (July 8, 2005). "Ezekwesili, Mimiko, 10 others on new cabinet list * Senate begins screening today". OnlineNigeria Daily News. Archived from the original on 2016-03-03. Retrieved 2009-12-16.
- ↑ Lall, S. (January 1956). "The International Civil Servant". Indian Journal of Public Administration. 2 (1): 12–17. doi:10.1177/0019556119560103. ISSN 0019-5561.
- ↑ "The Federal Republic of Nigeria". Worldwide Guide to Women in Leadership. Archived from the original on 2009-04-21. Retrieved 2009-12-17.
- ↑ "How bad politics killed our education". Vanguard News (in Turanci). 2011-08-16. Retrieved 2021-05-14.
- ↑ Gbadeyanka, Modupe (2019-10-23). "Former Minister Leaves Board of UACN Property | Business Post Nigeria" (in Turanci). Retrieved 2021-05-14.
- ↑ "Yar'Adua names cabinet". Africa News. 27 July 2007. Archived from the original on 28 September 2011. Retrieved 2009-12-15.
- ↑ Lucky Nwankere, Abuja (October 30, 2008). "BOOTED OUT! ...20 Ministers sacked, as Yar'Adua reshuffles cabinet ...Aondoakaa, Diezani Allison-Madueke, Ojo Maduekwe survive ...Modibbo, Daggash dropped". Archived from the original on August 17, 2010. Retrieved 2009-12-17.
- ↑ Empty citation (help)
- ↑ Nosike Ogbuenyi, Abimbola Akosile and Sufuyan Ojeifo (19 December 2008). "Yar'Adua Renews His Mission". ThisDay.