John Odey
John Ogar Odey (Nuwamba 1, 1959 – 7 Oktoba 2018)[1] an naɗa shi ministan yaɗa labarai da sadarwa na Najeriya a cikin watan Yulin 2007, kuma ya zama ministan muhalli a cikin watan Disambar 2008 bayan shugaba Umaru Yar’Adua ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul.[2][3]
John Odey | |||||
---|---|---|---|---|---|
17 Disamba 2008 - 29 Mayu 2015 ← Halima Tayo Alao
26 ga Yuli, 2007 - 17 Disamba 2008 ← Frank Nweke - Dora Akunyili → | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | 1 Nuwamba, 1959 | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Mutuwa | 7 Oktoba 2018 | ||||
Karatu | |||||
Makaranta | Jami'ar Calabar | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Tarihin Rayuwa
gyara sasheOdey ya kammala karatunsa na B.Sc. a banki da kuɗi daga Jami'ar Calabar a shekarar 1986.[4] Ya kasance mai aiki a kafafen yaɗa labarai, yana da muƙamai kamar babban manajan Sadarwa na Kudu maso Kudu da shugaban Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya.[3] An naɗa shi sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar PDP na kasa a cikin shekarar 2004.[4]
Ya yi ministan yaɗa labarai da sadarwa[5] sannan ya zama ministan muhalli a majalisar ministocin Umaru Yar’adua.[6] A watan Maris ɗin shekarar 2010, ya miƙa wa babban sakatare na ma’aikatar muhalli bayan da mataimakin shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya rusa majalisar ministocinsa.[7]
Mutuwa
gyara sasheOdey ya rasu a ranar Lahadi, 7 ga watan Oktoban 2018 a birnin Dubai na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, bayan ya yi fama da ciwon daji[8] wanda ya sa ya fita ƙasar waje neman magani.
Binne
gyara sasheAn kai gawar Odey gida a ranar Talata 6 ga watan Nuwamba, 2018, domin a huta a mahaifarsa, Okpoma, ƙaramar hukumar Yala a jihar Cross River, cikin hawaye da shedu. An kai gawar ne da misalin ƙarfe 5 na yamma, kuma an kai gawar zuwa Cocin Christ the King Catholic da ke Okpoma domin gudanar da taro domin karrama shi. An binne shi a Okpoma a ranar Laraba 7 ga watan Nuwamban 2018.
Manazarta
gyara sashe
- ↑ https://www.bodedolu.com/former-pdp-spokesman-john-odey-has-passed-away/
- ↑ https://web.archive.org/web/20110928064504/http://www.africanews.com/site/Nigeria_YarAdua_names_cabinet/list_messages/10239
- ↑ 3.0 3.1 https://allafrica.com/stories/200812190005.html
- ↑ 4.0 4.1 https://web.archive.org/web/20070711113054/http://odili.net/news/source/2007/jul/7/207.html
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/news/top-news/288963-breaking-ex-minister-john-odey-is-dead.html?tztc=1
- ↑ https://www.vanguardngr.com/2011/06/new-cabinet-ezekwesili-opts-out/amp/
- ↑ https://punchng.com/Articl.aspx?theartic=Art201003193573175[permanent dead link]
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/news/top-news/288963-breaking-ex-minister-john-odey-is-dead.html?tztc=1