Gombe Lawanti International Airport
Sani Abacha International Airport ( filin jirgin sama ne da ke aiki a Gombe babban birnin jihar Gombe ta Najeriya. An gina shi ne a kan hanyar Bauchi zuwa Gombe ta kauyen Lawanti da ke karamar hukumar Akko, Gombe. An fara shirin ne a cikin 2005 kuma an ba da takardar shedar tashi sama a 2008, jirgin farko na kasa da kasa zuwa Jeddah, Saudi Arabia. Filin jirgin saman Gombe na iya daukar jiragen dakon kaya, filin jirgin saman Gombe Lawanti yana da tsawon kilomita 3.5 kuma yana iya daukar jiragen dakon kaya a lokaci guda. Filin jirgin saman yana da cikakkun kayan aiki na zamani kuma yana da tsaro kuma yana da aminci ga tafiye-tafiye na gida da waje..
Gombe Lawanti International Airport | |
---|---|
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya |
Jihohin Najeriya | Jihar Gombe |
Coordinates | 10°17′56″N 10°54′00″E / 10.2989°N 10.9°E |
History and use | |
Mai-iko | Gwamnatin Tarayyar Najeriya |
Suna saboda | Lawanti (en) |
City served | Gombe, da Arik Air |
Contact | |
Address | 8W45+Q25, 771104, Lawanti, Gombe da Lawanti, Bauchi road |
|
Jiragen sama da wuraren zuwa
gyara sasheDaukar nauyin da gwamnatin tarayya ta dauka a filin jirgin
gyara sasheShugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da karbe filin jirgin saman Gombe Lawanti da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi . An bayyana hakan ne bayan ganawar da gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya yayi da shugaba Buhari a ofishin sa dake fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja.