Glo (kamfani)
Globacom Limited, wanda aka fi sani da Glo (Global Communication), kamfani ne na sadarwa na ƙasa da ƙasa wanda Mike Adenuga ya kafa a ranar 29 ga Agusta 2003.[1] Tun daga watan Yuni 2018, kamfanin ya ɗauki mutane aiki sama da 3,500 a faɗin duniya.
Glo | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | kamfani |
Masana'anta | Masana'antar sadarwa da mobile phone industry (en) |
Ƙasa | Najeriya |
Mulki | |
Hedkwata | Lagos, |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 2003 |
|
Dubawa
gyara sasheGLO yana da masu biyan kuɗi (subscribers) sama da miliyan 45 (Disamba 2018), wanda ya sa ya zama kamfani na biyu mafi girma a cibiyar sadarwa a Najeriya.[2]
A shekarar 2011, kamfanin GLO ya zama kamfanin sadarwa na farko da ya ƙera kebul na fiber optic mai karfin dala miliyan 800 wanda aka fi sani da Glo-1, kebul na ƙarƙashin ruwa daga ƙasar Ingila zuwa Najeriya.[3] Ita ce tashar jirgin ruwa ta farko da ta yi nasarar zuwa Najeriya daga Burtaniya ta cikin ƙarƙashin ruwa.
Globacom yana da mabanbanta tsarin kasuwanci masu mahimmanci: Glo mobile, Glo Broad Access, Glo Gateway da Glo-1.
Mallaka
gyara sasheKamfanin GLO mallakar Mike Adenuga Group ne, wanda kuma mallakin kamfanin ya ƙunshi; (Cobblestone Properties and Estates), kamfanin raya gidaje da kadarori, Conoil PLC, kamfanin sayar da man fetur, da kuma Conoil Producing, kamfanin binciken danyen mai da samar da kayayyaki.[4]
Tsarin kasuwancin Kamfanin
gyara sasheGlo Mobile
gyara sasheGlo Mobile, wani reshe ne daga Globacom , Glo Mobile shine hanyar sadarwa na biyu mafi girma a Najeriya. A shekarar farko da kamfanin ya fara aiki, ya sami masu mu'amala dashi (subscribers) miliyan ɗaya a cikin garuruwa sama da 87 na Najeriya, gami da samun kuɗaɗen shiga sama da Naira biliyan 120.[5] A yanzu dai Glo Mobile ya yaɗu zuwa wasu ƙasashen Afirka, wato Benin [6] da Ghana.[7] Kawo ya watan Disamba, 2018 Masu amfani da layin Glo Mobile a Najeriya sun kai sama da miliyan 45.[8]
Glo 1 submarine cable
gyara sasheGLO-1 kebul ne na farko da aka yi nasara jawowa daga Burtaniya zuwa Najeriya, kuma GLO shi ne kamfani na farko a Afirka da ya fara gudanar da irin wannan aiki.[9][10]
GLO-1 yana da yuwuwar samar da sabis na intanet mai sauri, inganci da sauƙin samun sabis na sadarwa. Glo-1 zai iya sauƙaƙe saka hannun jari na waje da guraben aikin yi musamman ga 'yan Afirka.[11][12]
Kebul ɗin mai nisan tsayin kilomita 9,800 an jawo shi ne daga Bude a Burtaniya har izuwa bakin tekun Alpha da ke birnin Legas, inda nan ne aka gina tashar tsayawar sa.[13] Glo-1 kuma zai inganta (teleconference, distance learning, recovery and telemedicine) da kuma hanyoyin sadarwar zamani d.ss ga ƴan Najeriya da mutanen yammacin Afirka.[14]
Ƙasashe
gyara sasheNajeriya
gyara sasheA watan Agustan 2003, an ƙaddamar da layin Glo Mobile a Najeriya. Kamfanin Glo Mobile ya gabatar da rangwamen farashi, biyan kuɗi da kuma sauran ƙarin ayyuka masu ƙima. Duk da cewa Glo Mobile ne kamfani na huɗu na GSM da aka ƙaddamar a Najeriya, a cikin shekaru bakwai da fara aiki da kamfanin, adadin masu amfani da shi ya karu zuwa sama da miliyan 25.[15]
Benin
gyara sasheA watan Yunin 2008, an ƙaddamar da Glo Mobile a Benin. Kamfanin Glo Mobile ya nuna ci gaban da ba a taba ganin irinsa ba ta hanyar sayar da katin layukan (SIM) 600,000 a cikin kwanaki goma na farko da fara aiki.[16] Glo Mobile yana ba da (offered Per Second Billing), wanda ke cajin masu biyan kuɗi domin Kira (calling) lokacin da aka yi amfani da kuɗin (airtime) ayayi buga waya ko kira. Sun kuma kawo wasu ƙarin ayyuka masu ƙima a layin nasu su ne; MMS (Sabis na Saƙon Multimedia), labarai da bayanai na Glo Magic Plus, bin diddigin abin hawa, da kuma (musical ring-back tones da mobile banking).
Ghana
gyara sasheA watan Mayun 2008, kamfanin GLO ya sami lasisin aiki ta hanyar rukunin Glo Mobile a Ghana kuma yana shirin samun kashi 30% na cikin masu mu'amala dashi miliyan 11 a cikin watanni 18 da ƙaddamarwa.[17] Suna shirin cimma wannan buri ta hanyar ƙaddamar da (bundled voice da sabis na Intanet) ga mazauna ƙasar Ghana da kuma faɗaɗa ayyukan kamfanin a wuraren da kasuwancin bai kai a manyan biranen ƙasar Ghana guda biyu, Accra da Kumasi. An tsara assasa kamfanin Glo Mobile a Ghana a watanni uku na farkon shekarar 2010.[18] Duk da haka an ɗage kafawar zuwa tsakkiyar watannin shekara ta 2011, harwayau assasa kamfanin haƙa bata cimma ruwa ba domin kuwa an sake ɗage kafa kamfanin a wannan shekara izuwa shekara ta 2012. A watan Janairun 2012, kamfanin na Glo Ghana ya buɗe kamfen na "Reserve your number", kuma ba tare da bude hanyar sadarwa ba ko assasa kamfanin. A ranar 8 ga Afrilu, 2011 GLO ta ƙaddamar da GLO1, wani ɓangare na aikinta na farko a Ghana, don shigar da wani babban jigo a cikin masana'antar sadarwa ta Ghana.
A cikin watan Oktoba 2009, GLO ya sami izinin jawo kebul na ƙarƙashin ruwa da Sabis daga International Gateway a ƙasar Cote d'Ivoire.
Tarihi
gyara sasheA cikin 2005, Glo Mobile ya gabatar da Glo Fleet Manager wanda shine tsarin bin diddigin abin hawa. Tsarin Manajan Fleet na Glo yana taimaka wa masu sufuri/jiragen ruwa sarrafa jiragensu. Har ila yau, sun gabatar da sabis na intanet na Glo Mobile wanda ke ba masu amfani damar shiga yanar gizo waɗanda aka keɓance su don yin browsing ta wayar hannu.
A cikin 2006, Glo Mobile ya gabatar da BlackBerry. GLO ta fara ɗaukar nauyin kyautar gwarzon ɗan wasan kwallon kafa na Afirka na shekara. Kamfanin ya kuma fara ɗaukar nauyin gasar Half Marathon of Glo Lagos International.
A shekara ta 2009, Glo Mobile ya ƙaddamar da sabis na biyan kuɗi na Blackberry wanda ke ba masu biyan kuɗi zaɓi don biyan kuɗin yau da kullun, mako-mako ko kowane wata. Sabis na biya na Blackberry yana ba masu biyan kuɗi damar shiga yahoo mail kyauta da messenger blackberry kyauta. Kamfanin ya kuma ƙaddamar da ayyukan fasahar intanet na 3G mai saurin gaske ta hanyar sayar da modem ɗinsa na 3G. Ana samun hanyar sadarwar Glo Mobile a tsarin 3G a biranen Legas, Abuja, Benin da Fatakwal, (a wancen lokacin).
Tallafi
gyara sasheKamfanin GLO na ɗaukar nauyin wasanni.
A Najeriya, GLO ya ɗauki nauyin Gasar firimiya ta Najeriya a 2009, Kungiyoyin Kwallon kafa na Najeriya, Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF),[19] Glo Lagos International Half Marathon,[20] Glo People Police Marathon,[21] Eyo Festival, Ojude Oba Festival,[22] Eleghe Festival[23] da Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Afirka.[24]
A ƙasar Benin, GLO ne ke ɗaukar nauyin bada kyautar FITHEB da CAF na Gwarzon ɗan wasan Afrika.[25]
A Ghana, GLO ne ke ɗaukar nauyin gasar Premier ta Glo Ghana, da ƙungiyoyin kwallon kafar Ghana da kuma kyautar gwarzon ɗan wasan Afrika na shekara CAF.[26]
A cikin Nuwamba 2009, GLO ya zama hukuma ta musamman mai ɗaukar nauyin ƙungiyar kwallon kafa ta Manchester United. Tallafin ya kuma haɗa da matasan 'yan wasa daga Benin da Ghana da Najeriya da ke zuwa Manchester domin yin atisaye da kungiyar.[27]
Reshen kamfanin na Glo wato Globacom ne kaɗai mai ɗaukar nauyin shirin African Voice (Muryar Afrika) a gidan talabijin na CNN. Manufar shirin ita ce don a inganta wasa a nahiyar Afirka da kuma tallata tambarin 'Globacom' a duk duniya ta dandalin CNN.[28]
Nishaɗi
gyara sasheGLO ya yi haɗin gwiwa tare da MTV akan shirin The Big Friday a cikin shekarar 2012. Wannan ƙawance ya ƙara jawo masu sha'awar wasan kwaikwayon kuma ya ba masu kallo damar fitowa kai tsaye acikin shirin. Akwai fa'ida ga masu biyan kuɗi ko mu'amala da GLO ɗin kan iya samun nasarar lashe kyaututtuka da ake sakawa a kowanne sati/ mako.[29]
A cikin Afrilu 2013, GLO ya gabatar da wasan kwaikwayo na, X Factor zuwa Afirka. An gudanar da taron ƙarawa juna sani ne a Najeriya da Ghana, inda babbar kyauta a wajen taron ta kasance kyautar tsabar kudi har dala 150,000 da kuma kulla wata yarjejeniyar da kamfanin Sony Music.[30]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Kerry A. Dolan. " Fewer Billionaires, Poorer Billionaires On African Continent In 2019 ", Forbes, Jan 9, 2019.
- ↑ Ife Ogunfuwa. "Glo overtakes Airtel, emerges Nigeria’s second largest telco", Punch Newspapers, Dec 30, 2018.
- ↑ IT News Africa "Glo One Submarine Cable Debuts in Lagos", IT News Africa, 8 September 2009. Accessed 21 August 2015.
- ↑ "Glo makes test call"[permanent dead link], TeleGeography, 18 December 2007. Accessed 21 August 2015.
- ↑ "Globacom may acquire NITEL", Daily Champion, 16 September 2009. Accessed 27 August 2015
- ↑ Nkanga, Efem. "Benin: Glo Launches Network in Country Today", All Africa, 5 June 2008. Accessed 27 August 2015.
- ↑ Nweke, Remmy "e-Readiness: Nigeria ranks 94", Daily Champion, 25 June 2008. Accessed 14 September 2015.
- ↑ "Globacom Limited" (in Turanci). Retrieved 2020-05-28.
- ↑ "Glo One Submarine Cable Debuts in Lagos", IT News, 8 September 2009. Accessed 11 November 2015.
- ↑ "Glo 1 Submarine cable lands in Lagos", Vanguard, 6 September 2009. Accessed 11 November 2015.
- ↑ "Web Page Under Construction". Retrieved 27 December 2016.
- ↑ Eribake, Akintayo (6 September 2009). "Glo 1 Submarine cable lands in Lagos". Retrieved 27 December 2016.
- ↑ "Nigeria: GLO -1 Berths in Accra". 29 September 2009. Retrieved 27 December 2016 – via AllAfrica.
- ↑ "The Nation Newspaper Nigeria - Read Latest Nigeria News". Archived from the original on 26 July 2011. Retrieved 27 December 2016.
- ↑ Nkanga, Efem (14 September 2006). "Nigeria: Globacom is 100 Percent Nigerian Company - Jameel". Retrieved 27 December 2016 – via AllAfrica.
- ↑ "Cellular-News". Archived from the original on 12 March 2017. Retrieved 27 December 2016.
- ↑ "IT Edge News". Archived from the original on 2 December 2009. Retrieved 2 November 2009.
- ↑ "IT Edge News". Archived from the original on 2 December 2009. Retrieved 2 November 2009.
- ↑ "Africa: GLO Congratulates Africa On Ghana's Victory". 19 October 2009. Retrieved 27 December 2016 – via AllAfrica.
- ↑ "Glo Lagos Marathon". Archived from the original on 15 March 2009. Retrieved 27 December 2016.
- ↑ "Nigeria: Glo People Police Marathon - Fighting Crime Through Sports". 27 April 2009. Retrieved 27 December 2016 – via AllAfrica.
- ↑ "Ojudeoba Festival". Archived from the original on 10 April 2011. Retrieved 27 December 2016.
- ↑ This Day Online Archived 2007-06-21 at Archive.today
- ↑ "hotel luggage carts - Best Moving Equipment For Football Gear". Retrieved 27 December 2016.
- ↑ Giwa, Sherifat (1 April 2008). "Nigeria: Globacom Signs MoU With West Africa's Biggest Theatre Festival". Retrieved 27 December 2016 – via AllAfrica.
- ↑ Goal.com, 2009-11-02.
- ↑ Goal.com, 2009-11-02.
- ↑ "Glo Sponsors 'African Voices' On CNN". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 2018-08-15.
- ↑ "Glo, MTV Base partner on "The Big Friday Show" - Ghana Business News". www.ghanabusinessnews.com (in Turanci). July 2012. Retrieved 2018-08-15.
- ↑ "Glo brings 'X FACTOR' to Africa, with $150, 000 starprize". The New Times | Rwanda (in Turanci). 2013-04-22. Retrieved 2018-08-15.