CNN (Cable News Network) tashar watsa labarai ce ta ƙasa da ƙasa mai hedikwata a Atlanta, Jojiya, Amurka.[1][2][3] An kafa ta a cikin shekarata 1980 ta hannun mai mallakar kafofin watsa labarai na Amurka Ted Turner da Reese Schonfeld a matsayin tashar watsa labarai na tsawon sa'o'i 24 a kullum, kuma a halin yanzu mallakar kamfanin na watsa labarai na hannun Manhattan, Warner Bros. Discovery.[4] CNN ita ce tashar talabijin ta farko da ta fara watsa labarai tsawon sa'o'i 24. Kuma tashar talabijin ta farko- da ta fara watsa labarai a Amurka.[5][6][7][8][9]

CNN
URL (en) Fassara https://www.cnn.com/
Iri United States cable news (en) Fassara, specialty channel (en) Fassara, news website (en) Fassara da film production company (en) Fassara
Slogan (en) Fassara Go There, This is CNN, More People Get Their News from CNN From Any Other Source, The World's Most Trusted Name in News, The Most Trusted Name in News, The Worldwide Leader in News, Facts First, Reporting From Around the World, The World's News Network da The World's News Leader
Bangare na WarnerMedia (en) Fassara
Mai-iko Warner Bros. Discovery (en) Fassara
Maƙirƙiri Ted Turner (en) Fassara da Reese Schonfeld (en) Fassara
Service entry (en) Fassara 1 ga Yuni, 1980
Wurin hedkwatar CNN Center (en) Fassara da New York
Wurin hedkwatar Tarayyar Amurka
Kyauta ta samu Peabody Awards (en) Fassara, Princess of Asturias Award for Communications and Humanities (en) Fassara, Golden Nymph for Best 24-Hour News Program (en) Fassara, Four Freedoms Award – Freedom of Speech (en) Fassara, George Polk Award (en) Fassara, Four Freedoms Award (en) Fassara, News and Documentary Emmy Award (en) Fassara da Walter Cronkite Award for Excellence in Journalism (en) Fassara
Twitter CNN, CNNOriginals, cnnbrk, CNNPolitics, cnni, cnnweather da CNNPR
Facebook cnn
Instagram cnn
Youtube UCupvZG-5ko_eiXAupbDfxWw

Tun daga watan Satumba na shekarar 2018, CNN tana da masu mu'amala (subscribers) da tashar mutane miliyan 90.1 a matsayin masu biyan kuɗi (subscriptions), kuma (kashi 97.7% cikin 100 na masu mu'amala da tashar, na da tashar acikin akwatunan telebijin nasu a gidajen su).[10] MSNBC, matsakaicin masu kallo 580,000 a ko'ina cikin yini, ya ragu da kashi 49% daga shekarar da ta gabata, a cikin raguwar masu kallo a duka hanyoyin sadarwar tashar (channels).[11] Yayin da CNN ke a matsayi na 14 a cikin jerin tashoshin watsa labarai a shekara ta 2019,[12][13] gidan telebijin ɗin yayi kukan kura inda ya zabura izuwa mataki na 7th daga mataki na 14 da yake abaya. Acikin manyan hanyoyin sadarwa da sukayi fice akwai; (Fox News a mataki na 5, da MSNBC a mataki na 6, a wannan shekarar),[14] ta koma mataki na 11 a shekarar 2021.[15]

A duk duniya, shirye-shiryen CNN ana watsawa ta hanyar CNN International, waɗanda masu kallo ke gani a cikin ƙasashe da yankuna sama da 212;[16] tun daga watan Mayu 2019. Gidan talabijin ɗin mallakar Amurka, ana takaita sunan da CNN (US), Bugu da ƙari tana watsa shirye-shiryen ta a Kanada, wasu tsibiran Caribbean da kuma a Japan, inda aka fara watsa shirye-shirye a kafar yaɗa labarai ta CNNj a shekara ta 2003, tare da fassarar lokaci guda cikin harshen Jafananci.[17]

Tarihi gyara sashe

Kana iya karanta cikakken tarihin CNN anan

See also: History of CNN

An kaddamar da Cable News Network da karfe 5:00 na yamma, a ranar 1 ga watan Yunin shekarar 1980. Bayan gabatarwa daga; Ted Turner, David Walker da matarsa Lois Hart sune na farko da suka fara jawabi/watsa shiri a tashar.[18] Burt Reinhardt, mataimakin shugaban zartaswa na CNN, ya ɗauki mafi yawan ma'aikatan tashar su 200 na farko, ciki aka watsa shiri na faro da aka ma shirin laƙabi da, news anchor wanda, ɗan jarida Bernard Shaw ne, ya gabatar da shirin.[19]

Tun farkon farawa, CNN ta faɗaɗa hanyar isar da shirye-shiryen ta izuwa sassa daban-daban ta hanyar tauraron ɗan adam, gidajen yanar gizo, da tashoshi na musamman na (kamar CNN Airport). Kamfanin yana da ofisoshi 42 (11 na cikin gida, 31 na ƙasashen waje),[20] fiye da tashoshin gida na haɗin gwiwar 900 (wanda kuma ke karɓar labarai da abubuwan da ke ciki ta hanyar sabis na labarai na bidiyo na CNN Newsource),[21] da kuma cibiyoyin sadarwa na yanki da na waje da dama a duniya.[22] Nasarar tashar ya dogara kacokan akan babban wanda ya kafa ta Ted Turner, kamfanin Time Warner ada ana kiranta da WarnerMedia sai yayi maja da Discovery Inc. aka samar da Warner Bros. Discovery) Wanda a ƙarshe y mallaki kafofin Watsa Labarai na rukunin Turner Broadcasting System a shekarar 1996.[23][24]

Shirye-shirye gyara sashe

Kana iya karanta cikakken jerin shirye-shiryen da CNN ke watsawa anan

See also: List of programs broadcast by CNN

Mako gyara sashe

Jadawalin ranar mako na CNN na yanzu ya ƙunshi mafi yawan shirye-shiryen labarai a cikin sa'o'i na rana, sannan kuma labarai masu zurfi da shirye-shiryen bayanai a lokacin yamma da sa'o'i na farko. Shirye-shiryen safiya na cibiyar sadarwa ya ƙunshi Early Start, shirin labarai na safiya wanda Christine Roman da Laura Jarrett suka shirya da ƙarfe 5-6 na safe agogon (ET), sai shirin CNN This Morning, dake biye a bayan shirin da ya gabata, shirin safiya morning show na cibiyar sadarwa, wanda Don Lemon, Poppy Harlow da kuma Poppy Harlow suka shirya. Shirin Kaitlan Collins a karfe 6-9 na safe a agogon (ET). Yawancin shirye-shiryen dare da rana na tashar CNN sun ƙunshi; CNN Newsroom, shirye-shiryen labarai na birgima wanda Jim Sciutto ke shiryawa da safe da kuma shiri da suka haɗa da; CNN anchor, Victor Blackwell, da Alisyn Camerota ko kuma maimaicin shirin CNN anchor da rana. A tsakanin wallafe-wallafe na Newsroom, At This Hour with Kate Bolduan da ƙarfe 11 na safe zuwa tsakar rana ET, sai kuma shirin Inside Politics, wanda John King ke shiryawa a tsakar rana-1, da rana.[25]

La'asar gyara sashe

Shirye-shiryen CNN daga la'asar zuwa maraice ya ƙunshi, shirin; The Lead with Jake Tapper a karfe 4-5 na yamma agogon (ET) da shirin The Situation Room with Wolf Blitzer a ƙarfe 5-7 na yamma ET. Brianna Keilar da/ko John Berman Sune ke gabatar da shirye-shiryen a wasu lokuta, da idan Tapper da Blitzer basu zo ba. Labaran maraice dama wasu shirye-shirye na musamman, sun haɗa da; Erin Burnett OutFront adaidai karfe 7 na yamma a agogon ET,[26] sai shirin Anderson Cooper 360° da karfe 8 na yamma ET, da shirin CNN Tonight ko wasu shirye-shiryen na CNN wanda Laura Coates, da/ko Alisyn Camerota ke gabatarwa da karfe 10 na dare ET.[Ana bukatan hujja]

Karshen mako gyara sashe

Lokacin farko na karshen mako-daga karfe 9 na yamma ET, ranar Asabar da 8 na yamma ET, ranar Lahadi - an sadaukar da shi galibi ga shirye-shirye na Jadawalin factual programming, da ya ƙunshi shirin; documentary da miniseries, da jerin shirye-shirye na reality (kamar shirin Anthony Bourdain: Parts Unknown da United Shades of America), da kuma fina-finai na gaskiya waɗanda ake haskawa a CNN Films. Shirye-shiryen safiya na karshen mako ya ƙunshi CNN Newsroom (simulcast from CNN International) da karfe 4-6 na safiyar kowace Asabar da 3-6 na safiyar kowace Lahadi agogon ET, wanda ke biyowa bayan an gabatar da shirin fitowar ta CNN This Morning, wanda Amara Walker da Boris Sanchez suka gabatar. wanda ake nunawa a kowace Asabar da karfe 6 – 9 na safe da Lahadi a karfe 6 – 8 na safe agogon ET, da shirin Asabar na cibiyar sadarwa Smerconish tare da Michael Smerconish a karfe 9 na safe ET. Jerin shirye-shirye na safiyar Lahadi ya ƙunshi, da farko shirin political talk shows, gami da Inside Politics Sunday, wanda Abby Phillip ya shirya a karfe 8 na safe a agogon ET, shirin [State of the Union]], wanda Jake Tapper da Dana Bash suka shirya a karfe 9 na safe, ET kuma ake maimaita shirin da rana ET,[27] sai kuma shirin al'amuran duniya Fareed Zakaria GPS, wanda Fareed Zakaria ya gabatar da karfe 10 na safe a agogon ET, kuma ana maimaita shi da karfe 1 na rana ET. Shirye-shiryen karshen mako ban da waɗanda aka ambata a sama, suna ciki jadawalin kundin CNN Newsroom wanda Fredricka Whitfield, Jim Acosta, Pamela Brown, da sauran ma'aikata ke gabatarwa.[Ana bukatan hujja]

A shekarar 2014-15, bayan soke shirin Piers Morgan Tonight (wanda, aka maye gurbin shirin mai tsawo, da shirin Larry King Live), CNN ta yi gwaji tare da gudanar da binciken ƙwaƙwaf ga shirye-shiryen karfe 9: 00 na yamma, masu tsawon awa ɗaya a agogon ET, kamar shirin da John Walsh ke gabatarwa na; The Hunt, This is Life with Lisa Ling, da kuma shirin da Mike Rowe yake gabatarwa na Somebody's Gotta Do It. Sai shugaban gidan jaridar Jeff Zucker ya bayyana cewa shirye-shiryen na kawo cikas don kawar da CNN daga dogaro da shirye-shiryen da suka shafi jadawalin shirye-shiryen (pundit-oriented programs), da kuma jawo hankalin matasa masu tasowa zuwa cibiyar sadarwar. Zucker ya bayyana cewa karfe 9:00 na dare, za a iya tafiya ɗan hutu na gajeren zango a yayin gabatar da manyan labarai don ƙarin lokacin alokacin shiri. Waɗannan canje-canjen sun zo daidai lokacin ƙaddamar da sabon kamfen game da hanyar sadarwa, mai ɗauke da taken "Go there".[28][29][30] A cikin watan Mayun shekarar 2014, CNN ta ƙaddamar da The Sixties, shirye-shiryen masu gajeren zango da Tom Hanks da Gary Goetzman suka samar (Produced), shirin ya ba da tarihin Amurka a shekarun 1960s. Sakamakon nasarar shirin, CNN ta ba da umarnin bin diddigin abubuwan da ke jan hankali a cikin shirin.[31][32][33][34] An ƙara tsawon shirin Anderson Cooper 360° izuwa sa'o'i biyu, daga karfe 8 na dare zuwa 10 na dare.[35]

A shekarar 2019, CNN ta samar da aƙalla shiri masu dogon Zango kwara 35. Tare da shirin Hanks/Goetzman franchise (ciki har da 2018 spin-off 1968), CNN ta watsa wasu shirye-shirye masu gajeren zango (miniseries) na labaran da suka shafi labarai da manufofin Amurka, irin su The Bush Years, da (Daular Amurika)-American Dynasties: Kennedys shirin CNN mafi girman akan kowane shiri mai dogon Zango na farko, har zuwa yau-(shirin na matsayin na ɗaya mafi girma), shirin na da makallata miliyan ɗaya da dubu ɗari bakwai (miliyan 1.7). Shirin Parts Unknown an ƙare shi, bayan da mai gabatar da shirin Anthony Bourdain ya kashe kansa a shekarar 2018; CNN ta ba da sanarwar sabbin shirye-shirye masu gajeren zango-(miniseries), da docuseries don shekarar 2019, haɗi da shirye-shiryen; American Style (wani shiri mai gajeren zango-(miniseries) da kamfanin watsa labarai na Vox Media ya samar),[36] The Redemption Project, tare da Van Jones, Chasing Life with Sanjay Gupta, Tricky Dick (wani shiri mai gajeren zango-(miniseries) na tarihin Richard Nixon), The Movies (wasan kwaikwayo masu gajeren zango na Hanks/Goetzman), da Once in a Great City: Detroit 1962-64.[37][38]

Bayan, kamfanonin Chris Licht da Warner Bros. Discovery, suke iko da CNN, an sanar a cikin watan Oktoban shekarar 2022 cewar CNN za ta rage farashin saye da kwamitocin daga wasu kamfanoni a matsayin ma'auni na rage tsada, amma Licht ya jaddada cewa "shiri mai tsawo ya kasance mai mahimmanci a sauran shirye-shiryenmu", yayin da tashar ta ba da sanarwar bada guraben shirye-shirye na shekarar 2023 wanda zasu haɗa da shirye-shirye na Giuliani: What happened to American's Mayor?, United State of Scandal, da The 2010s.[39][40]

On-air presentation gyara sashe

CNN ta fara watsa shirye-shirye a tsarin samfurin high-definition 1080i, a cikin Satumba 2007.[41] Wannan tsari yanzu shine daidaitaccen tsari ga CNN kuma ana samunsa akan duk manyan kebul da masu samar da tauraron ɗan adam.

 
Bus ɗin CNN, Mai suna Election Express, ana amfani da ita don watsa shirye-shirye

CNN tana ɗaukar hoto a tsarin HD (Wanda ake gani tartsatsai), an fara gabatar da bas ɗin CNN Election Express a watan Oktoban shekarar 2007. Motar (Election Express), na iya ɗaukar nau'in (HD kwara biyar a lokaci guda), an yi amfani da shi don muhawarar shugaban ƙasa ta CNN-YouTube na tashar da kuma tambayoyin ɗan takarar shugaban ƙasa.[42]

A cikin Disamban shekarata 2008, CNN ta gabatar da wani cikakken sake fasalin (on-air appearance), wanda ya maye gurbin salon da ake amfani da shi tun a shekarar 2004. Zane-zanen (On-air graphics) ya ɗauki tsari mai zagaye, lebur a cikin tsarin launi na baki, fari, da ja. da kuma gabatar da sabon akwati kusa da tambarin CNN don nuna tambura da ƙayyadaddun zane-zane na yanki, maimakon a matsayin babban allon talla (banner ) sama da ƙasan na uku. Sake fasalin ya kuma maye gurbin tikitin “flipper” a tsaye, wanda zai iya ko dai ya nuna kanun labarai (both manually inserted and taken from the RSS feeds of CNN.com), ko cikakkun bayanai na “topical” masu alaƙa da labari.[43][44]

An gabatar da babban sake fasalin CNN na gaba a ranar 10 ga Janairun shekarar 2011, tare da maye gurbin duhu, yanayin kamannin 2008 tare da tsarin launi mai sheki, shuɗi da fari, da matsar da akwatin tambarin na biyu zuwa ƙarshen allo. Bugu da ƙari, hanyar sadarwar ta fara samar da shirye-shiryenta kawai a cikin (16:9 aspect ratio), tare da amfani da letterboxed tsari na HD,[44] a ranar 18 ga watan Fabrairun shekarar 2013, an yi watsi da "flipper", asali yana nuna allon baya mai kalar shuɗih-(blue background) tare da farin rubutu, an gwada rubutun shuɗi akan allo baya mai kalar fari-(white background) don dacewa da kamannin 'flipper'.[45]

A ranar 11 ga Agusta na shekarar 2014, CNN ta gabatar da sabon fakitin zanunnuka. Yanzu yana musanya tsakanin kanun labarai na gabaɗaya da labaran kuɗi daga CNN Business, kuma an maye gurbin akwatin tambari na biyu-(Secondary logo box) tare da wani ƙarami, wanda ke nuna ko dai ;take-(tittle), hashtag, ko (Twitter handle).[46] A cikin Afrilu 2016, CNN ta fara gabatar da sabon nau'in kamfani, wanda aka sani da "CNN Sans", a duk faɗin dandamalinsa-(platforms). An sanar daga Helvetica Neue kuma an ba da izini bayan tattaunawa da (Troika Design Group), dangin (font) sun ƙunshi nau'ika 30 mabanbanta, tare da ma'aunin nauyi da faɗi daban-daban don sauƙaƙe amfani a cikin watsa shiri, talabijin, da hanyoyin dijital.[47]

A watan Agusta 2016, CNN ta sanar da ƙaddamar da CNN Aerial Imagery and Reporting (CNN AIR), aikin tattara labarai da jirgi marar matuki (drone), ya rahoto don haɗa hotuna da rahotanni a dukan rassan CNN da dandamali, tare da Turner Broadcasting da Time Warner.[48]

Ma'aikata gyara sashe

Manazarta gyara sashe

  1. Alfonso, Fernando (May 30, 2020). "CNN Center in Atlanta damaged during protests". CNN. Archived from the original on May 30, 2020. Retrieved January 16, 2021.
  2. "CNN Center". CNN. Archived from the original on January 21, 2021. Retrieved January 16, 2021.
  3. "About Us". CNN. Archived from the original on January 15, 2021. Retrieved January 16, 2021.
  4. "Time Warner: Turner Broadcasting". Archived from the original on January 22, 2011.
  5. Kiesewetter, John (May 28, 2000). "In 20 years, CNN has changed the way we view the news". Cincinnati Enquirer. Archived from the original on October 11, 2017. Retrieved January 24, 2009.
  6. "Charles Bierbauer, CNN senior Washington correspondent, discusses his 19-year career at CNN. (May 8, 2000)". CNN. Archived from the original on September 29, 2012. Retrieved October 12, 2013.
  7. "Reese's Pieces: Mr. Schonfeld, Forgotten Founder of CNN, Is a Man of Many Projects". Observer (in Turanci). January 29, 2001. Retrieved March 1, 2022.
  8. Stelter, Brian (July 28, 2020). "Reese Schonfeld, CNN's founding president, has died at 88". CNN. Archived from the original on July 29, 2020. Retrieved July 31, 2020.
  9. "CNN changed news – for better and worse". Taipei Times. May 31, 2005. Archived from the original on June 3, 2015. Retrieved January 24, 2009.
  10. "Nielsen coverage estimates for September see gains at ESPN networks, drops at MLBN and NFLN". September 10, 2018. Archived from the original on August 19, 2019. Retrieved July 18, 2019.
  11. Johnson, Ted (June 29, 2021). "Fox News Tops June And Q2 Viewership, But Plunge In Ratings Continues Across All Major Cable News Networks". Deadline. Archived from the original on July 7, 2021. Retrieved July 6, 2021.
  12. Andreeva, Nellie; Johnson, Ted (December 27, 2019). "Cable Ratings 2019: Fox News Tops Total Viewers, ESPN Wins 18–49 Demo As Entertainment Networks Slide". Deadline. Archived from the original on January 14, 2020. Retrieved January 16, 2020.
  13. Schneider, Michael (December 26, 2019). "Most-Watched Television Networks: Ranking 2019's Winners and Losers". Variety. Archived from the original on January 6, 2020. Retrieved January 16, 2020.
  14. Schneider, Michael (December 28, 2020). "Most-Watched Television Networks: Ranking 2020's Winners and Losers". Variety. Archived from the original on December 28, 2020. Retrieved May 2, 2022.
  15. Schneider, Michael (December 30, 2021). "Most-Watched Television Networks: Ranking 2021's Winners and Losers". Variety. Archived from the original on January 12, 2022.
  16. "CNN is Viewers Cable Network of Choice for Democratic and Republican National Convention Coverage" (Press release). Time Warner. August 18, 2000. Retrieved February 20, 2010.[permanent dead link]
  17. "CNN Partners". CNN Asia Pacific. Archived from the original on July 29, 2012. Retrieved May 4, 2020.
  18. Barkin, Steve Michael; Sharpe, M.E. (2003). American Television News: The Media Marketplace and the Public Interest.
  19. Wiseman, Lauren (May 10, 2011). "Burt Reinhardt dies at 91: Newsman helped launch CNN". The Washington Post. Archived from the original on July 18, 2019. Retrieved May 19, 2011.
  20. "Cable News: Fact Sheet". Pew Research Center's Journalism Project. June 15, 2016. Archived from the original on April 19, 2017. Retrieved April 20, 2017.
  21. "CNN Newsource". CNN Newsource (in Turanci). Archived from the original on April 21, 2017. Retrieved April 20, 2017.
  22. Sterling, Christopher H. (September 25, 2009). Encyclopedia of journalism. 6. Appendices (in Turanci). SAGE. ISBN 9780761929574. Archived from the original on April 14, 2021. Retrieved October 15, 2020.
  23. Tyree, Omar (April 27, 2009). The Equation: Applying the 4 Indisputable Components of Business Success (in Turanci). John Wiley & Sons. ISBN 9780470452837. Archived from the original on April 14, 2021. Retrieved October 15, 2020.
  24. "Ted Turner, the Lost Tycoon". The New Yorker. April 15, 2001. Archived from the original on February 24, 2017. Retrieved April 20, 2017.
  25. "Why a Sugar High is in the Making for Kate Bolduan's Daughter". TVNewser. Adweek Blog Network. Archived from the original on August 20, 2015. Retrieved August 20, 2015.
  26. Hall, Colby. "CNN Reveals New 7 pm Show Title: Erin Burnett: OutFront". Mediaite. Archived from the original on July 31, 2012. Retrieved September 23, 2011.
  27. Johnson, Ted (January 11, 2021). "CNN Announces Lineup Changes: Jake Tapper To Be Lead Anchor For All Major D.C. Events; Jim Acosta Takes On New Role With Weekend Show". Deadline. Archived from the original on April 6, 2021. Retrieved March 10, 2021.
  28. "CNN Keeps Burnett, Cooper in Primetime While Adding 'CNN Tonight' at 10 P.M." Variety. Archived from the original on April 13, 2014. Retrieved April 11, 2014.
  29. Flint, Joe (April 10, 2014). "CNN unveils new prime-time lineup, moves away from 9 p.m. talk". Los Angeles Times. Archived from the original on April 11, 2014. Retrieved April 11, 2014.
  30. "CNN Doubles Down on a Mix of Live News, Original Series and Films". TVNewer. Archived from the original on April 11, 2014. Retrieved April 11, 2014.
  31. de Moraes, Lisa (May 17, 2017). "CNN Adds Series On 1960s & '70s To Slate; HLN Adds 'Unmasking A Killer'". Deadline (in Turanci). Archived from the original on May 14, 2018. Retrieved May 13, 2018.
  32. Petski, Denise (April 11, 2018). "CNN Adds Six New Original Series To 2019 Slate; Projects From Sanjay Gupta, Vox Media, More". Deadline (in Turanci). Archived from the original on May 26, 2018. Retrieved May 13, 2018.
  33. "CNN To Follow 'The Sixties' Docu-series With 'The Seventies'". Variety. November 20, 2014. Archived from the original on March 20, 2016. Retrieved April 3, 2016.
  34. "CNN To Launch 'The Eighties' In March". Variety. February 25, 2016. Archived from the original on April 6, 2016. Retrieved April 3, 2016.
  35. "Ratings for Anderson Cooper's Karen McDougal Interview". TVNewser (in Turanci). Archived from the original on May 29, 2018. Retrieved May 28, 2018.
  36. "Vox Entertainment to Produce New CNN Original Series 'American Style'". TheWrap (in Turanci). April 11, 2018. Archived from the original on December 15, 2018. Retrieved May 5, 2019.
  37. Littleton, Cynthia (March 15, 2019). "CNN Original Series Ride News Tide to Multiplatform Success". Variety (in Turanci). Archived from the original on September 29, 2019. Retrieved May 5, 2019.
  38. Petski, Denise (April 11, 2018). "CNN Adds Six New Original Series To 2019 Slate; Projects From Sanjay Gupta, Vox Media, More". Deadline (in Turanci). Archived from the original on May 5, 2019. Retrieved May 5, 2019.
  39. Johnson, Ted (2022-12-13). "CNN Unveils 2023 Original Series And Films Slate: Projects Include 'Giuliani,' Jake Tapper-Hosted 'United States Of Scandal' And 'The 2010s'". Deadline (in Turanci). Retrieved 2022-12-13.
  40. Johnson, Ted (2022-10-28). "CNN To Scale Back Original Series And Films As It Looks To Move Longform In House". Deadline (in Turanci). Retrieved 2022-12-13.
  41. Robbins, Stephanie. "TV Week September 6, 2007 CNN HD Debuts". Tvweek.com. Archived from the original on October 15, 2013. Retrieved October 12, 2013.
  42. "CNN Rolls Out Election Express". Tvtechnology.com. October 17, 2007. Archived from the original on November 25, 2011. Retrieved October 12, 2013.
  43. Dickson, Glen (December 15, 2008). "CNN Gets New Graphic Look". Broadcasting & Cable. Archived from the original on February 6, 2009. Retrieved January 24, 2009.
  44. 44.0 44.1 "CNN Debuts New Graphics Package". TVNewser. Archived from the original on July 13, 2014. Retrieved September 3, 2014.
  45. Airens, Chris (February 18, 2013). "The Ticker Returns to CNN". TVNewser. Archived from the original on February 21, 2013. Retrieved February 19, 2013.
  46. "CNN Updates Graphics Package". TVNewser. Archived from the original on August 15, 2014. Retrieved September 3, 2014.
  47. "CNN customizes new company-wide font". PromaxBDA. Archived from the original on September 11, 2016. Retrieved September 22, 2016.
  48. "CNN is launching a drone-based news collecting operation". TechCrunch. August 18, 2016. Archived from the original on April 7, 2018. Retrieved January 19, 2018.