Gidan Arewa

cibiyar bincike a Kaduna, Najeriya

Gidan Arewa ko Arewa House da turanci, Cibiyar Bincike da Adana Kayan Tarihi ce karkashin Jami'ar Ahmadu Bello, gidan ta kasance tsohuwar gidan firimiyan Arewacin Najeriya ne, inda a nan ne Firimiya Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya zauna har zuwa lokacin da aka kashe shi a alif.1966. Gidan na nan ne acikin garin Kaduna, Jihar Kaduna, Najeriya. Dr Shu aibu Shehu Aliyu shi ne darektan gidan a yanzu.

Gidan Arewa
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJihar Kaduna
Coordinates 10°33′N 7°27′E / 10.55°N 7.45°E / 10.55; 7.45
Map
Heritage
Contact
Address No. 1 Rabah Road, Ungwan Sarki Muslimi 800283, Kaduna
Offical website
arewa hause
arewa house library kaduna

An gina Gidan Arewa a shekarar 1950 domin ta zama mazauni ga firimiyar Yankin Arewacin Najeriya, saï dai kash! A ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1966, wani matashi da Firimiyan Bello ya rika wato Chukwuma Kaduna Nzegwu ya jagoranci juyin mulki a lokacin yana Cadet a NDA, suka kifar da gwamnatin Abubakar Tafawa Balewa da kashe shi da kashe Firimiyan da wasu yan' siyasan Arewacin Najeriya. Wanda ganin gidan a zaune babu abunda akeyi aciki ne, saï gwamnatin wancan lokaci ta mikawa Jami'ar Ahmadu Bello yazama wani bangare na Jami'ar a shekarata 1970, lokacin da aka nemi kwamiti mai ba da shawara ya rubuta littafi game da tarihin Arewacin Najeriya.[1] An nada darektan farko na cibiyar, Marigayi Farfesa Abdullahi Smith, wanda ya fara aiki a Sashen Tarihi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya tare da sanya wa gidan suna Gidan Arewa, cibiyar bincike da kuma tattara bayanan tarihi da al'adun gargajiya na jama'ar Arewacin Najeriya. An yi amfani da gidan a matsayin cibiyar bincike tun daga shekarar 1970, bayan da aka ba kwamitin da aka sani da Kwamitin Tarihin Arewacin Najeriya alhakin rubuta littafi akan tarihin Arewacin Najeriya.[2]

Tsarin da amfani

gyara sashe

Gidan tarihi na Arewa House yana da kayayyakin tarihi, hotuna da littattafai waɗanda jama'a za su iya samu. Ya ƙunshi tauraron tauraron ɗan adam guda goma sha biyu waɗanda ke nuna al'adu da jama'ar Arewacin Najeriya da kuma tarihin rayuwar Ahmadu Bello. A yanzu haka shine cibiyar tattara bayanan tarihi da bincike na Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, Najeriya.

Bibliography

gyara sashe
  • Bashir Ikara (1988). Bayanin Arewa House: Matsayin Gudanar da Binciken Bincike da Ci gaba a Cibiyar Bincike da Littattafan Tarihi, Jami'ar Ahmadu Bello, Kaduna . Kamfanin wallafa wallafe-wallafen Arewacin Najeriya. ISBN   Bashir Ikara (1988). Bashir Ikara (1988).
  • Abdullahi Mahadi; George Amale Kwanashie (1 January 1999). Jagoranci, Lissafi, da Makomar Najeriya: Jagoranci na Arewa House a cikin Darajan Alhaji (Sir) Ahmadu Bello, Sardauna na Sakkwato, da Firayim na Yankin Arewa na Najeriya . Arewa House, Jami’ar Ahmadu Bello. ISBN   Abdullahi Mahadi; George Amale Kwanashie (1 January 1999). Abdullahi Mahadi; George Amale Kwanashie (1 January 1999).

Manazarta

gyara sashe
  1. Guest. "The Arewa House Museum". NigerianReporter.com: Nigeria, News, Politics, Africa (in Turanci). Archived from the original on 2018-06-01. Retrieved 2020-04-08.
  2. Akintayo Abodunrin (2 February 2016). "The Arewa House Museum". Nigerian Reporter. Archived from the original on 16 September 2016. Retrieved 4 September 2016.

Hanyoyin haɗin waje

gyara sashe

Coordinates: 10°33′11″N 7°26′45″E / 10.5531°N 7.4458°E / 10.5531; 7.4458