Fatimat Olufunke Raji-Rasaki
Fatimat Olufunke Raji-Rasaki (an haife ta a 1 ga Janairun 1957) ‘yar siyasan Najeriya ce, mai fafutika kuma tsohuwar ma’aikaciyar gwamnati
Fatimat Olufunke Raji-Rasaki | |||
---|---|---|---|
ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019 ← Adefemi Kila - Michael Opeyemi Bamidele → District: Ekiti central | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Jahar Ekiti, 1 ga Janairu, 1957 (67 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Ƴan uwa | |||
Abokiyar zama | Raji Rasaki | ||
Karatu | |||
Makaranta | Jami'ar jahar Lagos | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da civil servant (en) | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa |
Peoples Democratic Party All Progressives Congress |
Farkon rayuwa
gyara sasheAn haifi Raji-Rasaki a jihar Ekiti a ranar 1 ga Janairun 1957.[1] Ta tafi Makarantar Grammar Memorial ta Doherty a Ijero, kafin ta yi karatu a Jami’ar Legas.
An zaɓe ta a matsayin sanata ta jihar Ekiti.[2] Akwai sanatoci sama da 100 da aka zaba a majalisa ta 8 a 2015, amma shida daga cikin wadannan mata ne. Sauran su ne Stella Oduah da Uche Ekwunife waɗanda dukkansu ke wakiltar Anambra, Rose Okoji Oko, Oluremi Tinubu da Binta Garba.[3]
Aiki
gyara sasheTa kasance shugabar kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin kasuwanci da zuba jari a majalisa ta 8 da Bukola Saraki ya zama shugaban majalisar.[4]
Iyali
gyara sasheA shekarar 2016 tayi bikin murnar cika shekaru 40 da aure tare da mijinta, Birgediya Janar Raji Rasaki.[5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Hon. Fatimat Olufunke RajiI-Rasaki Archived 2017-04-26 at the Wayback Machine, Fatimat Olufunke RajiI-Rasaki, Retrieved 14 February 2016
- ↑ HON. FATIMAT OLUFUNKE RAJI-RASAKI, Nass.gov.uk, Retrieved 15 February 2016
- ↑ The 6 female senators in 8th National Assembly, Naij,com, Retrieved 15 February 2016
- ↑ "Saraki names 65 Senate committees". Latest Nigeria News, Nigerian Newspapers, Politics (in Turanci). 2015-11-04. Retrieved 2021-04-23.
- ↑ Ex-Gov. Raji Rasaki And Wife, Fatima Open Up On Their 40 Year Marriage Archived 2018-12-10 at the Wayback Machine, Tayo Fajorin-Oyediji, CityPeopleNG.eng, Retrieved 14 February 2016