Dogondoutchi ko Dogonduci[1] (Dogon Dutse a Hausa ta mutanen Najeriya) birni ne dake kilomita 300 daga gabashin birnin Niamey na kasar Nijer, kuma kilomita 40 daga iyakar Nijar da Najeriya. Birnin na kan babbar hanyar da ta hada baban birnin kasar da Maradi da Zinder har zuwa gabashi da Arewacin yankunan Tahua, Agadez da Arlit. Dogondoutchi cibiyar gudanarwa ta yankun rayawa na Dogondoutchi a Jamhuriyar Nijar. Yana kuma karkashin jahar Dosso kuma. Al'umar yankin zaikai kimanin 80,000.

Dogondoutchi


Wuri
Map
 13°39′00″N 4°02′00″E / 13.65°N 4.0333°E / 13.65; 4.0333
JamhuriyaNijar
Yankin NijarYankin Dosso
Department of Niger (en) FassaraDogondoutchi (sashe)
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 71,692 (2012)
Labarin ƙasa
Wuri a ina ko kusa da wace teku Dallol Maouri (en) Fassara
Altitude (en) Fassara 227 m
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Dogondoutchi, Nijar
kogin Dogondoutchi

Yanayin muhalli gyara sashe

Yankin Dogondoutchi gyara sashe

Daga Arewacin garin Dogondoutchi akwai manyan tsaunuka wanda daganan ne ma garin ya samo asalin sunan sa. Sannan kuma garina yana gefen kogi ne. Sannan garin yana a Kudu maso gabashin Nijar ne tsakanin Sahel da kudu yankin da ake samun wadataccen ruwan sama.

Akwai yanayin samun isasshen ruwan sama a yankin .

 

Ruwan sama da Zaizayar kasa gyara sashe

Yawan mutane gyara sashe

Mazaunan asali gyara sashe

 

Akwai mutane kimanin 80,000 (kidayar 2011) akwai akalla mutane 30,000 a yankin birni. Akwai yankunan rayawa guda 11 da kauyuka 17 da kabilun Fulani 5. Kabilin yankin sun hada da Hausawa da Fulani da Abzinawa da Djerma (zabarmawa). Dogondoutchi shine mahadar yamma ta al'umar Hausawa sosai, wadanda sune kabilu mafiya yawa a yankin.

Addini gyara sashe

Kaso 90% na mutanen Musulunci ne addinin su, sai kuma masu bin addinin gargajiya kamar Bori na wadansu Hausawa. Sannan kuma akwai adadin masu bin Kirista kalilan a birnin.

Ma'aikatun Gwamnati gyara sashe

Kiyon Lafiya gyara sashe

A shekarar 2015 Dogon Dutsi tana da asibitin gunduma guda daya (1), cibiyar kula da uwa da yara kanana guda daya (1), hadaddun cibiyoyin kiwon lafiya guda uku (3) da kuma dakunan shan magani da aka rarraba a kauyukan kewaye da birnin guda bakwai (7). Bacin wadannan akwai ma'aikata kamar likitoci 3, ma'aikatan jinya 14, ungozomomi 6, matkuna guda 4, shagunan sayar da magani (farmasi) 4 da wuraren ajiye magunguna guda 2. Yawancin haihuwa suna faruwa ne a cibiyoyin kiwon lafiya, abinda ya rage mace-macen mata da yara.[2]

Ilimi gyara sashe

Ana magana da yarukan Afirka guda 10 kowace rana a Nijar, aƙalla huɗu daga cikinsu ana anfani dasu a cikin Dogon Dutsi. Amma Faransanci shine harshen hukuma; wannan shine dalilin da ya sa ake fara koyawa yara Faransanci daga shekarar farko ta makarantar firamare inda suke share shekaru 6 na firamare suna amsar ilimi cikin yaren na Faransanci, za a ci gaba har zuwa karshen sakandare ana ba da koyarwa gaba ɗaya cikin Faransanci. A sherkarun 2015-2016, akwai makarantatun firamare na gwamnati guda 67 inda daya (1) daga cikinsu ta Franco-Arab (Faransanci-Larabci) ce; kuma azuzuwa kimanin 299 ne dalibai kusan 36 959 inda mata 17 597, maza 19362.[3]

Manazarta gyara sashe

  1. Ham, Anthony (2009). Lonely Planet; Dogondoutchi. ISBN 9781741048216.
  2. Institut National de la Statistique du Niger, "Annuaire Statistique 2013-2018", 2018
  3. Ma'aikatar kula da Ilimi ta kasa, 2016, Dosso