Niamey babban birnin ƙasar Nijar ne. Wannan birnin yana a matsayin babbar gundumar Birni kuma ya hada gunduma biyar ne. Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar 2011, jimillar mutane 1,302,910 (miliyan ɗaya da dubu dari uku da biyu da dari tara da goma). An gina birnin Niamey a farkon karni na ashirin bayan haifuwan annabi Issa. Babban kogin nan na "Niger" wanda cibiyarshi take tsakanin Sierra Leone da Guinée, ya ratsa birnin Niamey.

Niamey
Ɲamay (mis)
Yamai (ha)
ⵏⵉⴰⵎⵢ (mis)


Wuri
Map
 13°30′54″N 2°07′03″E / 13.515°N 2.1175°E / 13.515; 2.1175
JamhuriyaNijar
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 1,026,848 (2012)
• Yawan mutane 4,291.05 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 239,300,000 m²
Wuri a ina ko kusa da wace teku Nijar
Altitude (en) Fassara 207 m
Sun raba iyaka da
Tsarin Siyasa
• Gwamna Bibata Niandou Barry (9 ga Janairu, 2003)
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NE-8
niamey harobanda
Koris na Yamai kewaye da lambuna

Tarihi gyara sashe

Birnin Niamey ya fara ci gaba ne wajen shekarar 1900, a daidai wani waje inda Fulanin Koira, Gaweye, Kalley, Maourey, Zongo, Gamkalé da Saga suke a lokacin. Kabilar da tafi yawa sune Zabarmawa ko kuma Songhai. Turawa sun iso Niamey ne a makare saboda tana can yammacin kasar inda babu wani kasuwanci da akeyi. Mutanen Gurmance (Gourmantché) ne suka fara rayuwa a yankin Niamey. Amma, wadanda suka kafa kauyen Niamey, Arawa ne da suka zo daga Matankari.

 
Niger, Niamey, Place du Temple
 
Niger, Niamey, Place du Liptako-Gourma

Manazarta gyara sashe