Zinder Kuma ana iya fadin Zindar, shine birni na biyu mafi girma a kasar Nijar yana da yawan jama'a 170,574 (kidayar 2001). Amma zuwa 2005 adadin jama'ar ya karu inda alkaluma suka nuna ya zarta 200,000. Yana tsakanin babban birnin kasar wato Niamey kilomita 861 daga gabas da birnin na Niamey. Yana kuma tsakanin kilomita 240 daga arewacin birnin Kano na Najeriya.

Zinder
Zinder (fr)
Zinder (en)


Wuri
Map
 13°48′N 8°59′E / 13.8°N 8.98°E / 13.8; 8.98
JamhuriyaNijar
Yankin NijarYankin Zinder
Department of Niger (en) FassaraMirriah (sashe)
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 235,605 (2012)
Labarin ƙasa
Altitude (en) Fassara 479 m
Sun raba iyaka da
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Taswirar Zinder

Tarihin farko-farko

gyara sashe

Zinder ta fara ne daga dan karamin kauyen Hausawa zuwa cibiyar kasuwanci mai matukar muhimmanci a tsakani Yankasuwar Sahara. Ashekarar 1736 ne jama'ar Kanuri suka kafa daular Damagaram. Asannan ne kuma daular ta gina yankin da ayanzu ake kira Birni. Kuma Birni ya zama wata babbar mahada ta mutanen Kano da kuma na Borno da kuma Abzinawa wajen Kasuwanci.

A karni na 19, gabaki dayan yankin yana karkashin ikon masarautar Sarkin Musulmi ta Borno ne, amma daga bisani sai yankin ya samu cikken yanci ta hannun Rabah. A shekarar 1889 aka kashe wani Bafaranshe mai bincike mai suna Cazemajou.

Tarihi na wannan lokacin

gyara sashe

A shekarar 2003 ne layin wayar salula na farko wato CELTEL ya baiyana a birnin, tare da gina dogon benen na sayar da wayoyin hannu tare da layukan waya. Sakamakon wannan shigowar ta wayar hannu ya sauya tsarin isar da bayanai a birnin. Saboda yana bama yankasuwa damar isar da sakonni cikin sauri kuma ba wata wahala ko matsala, wannan na daga cikin abubuwan da kamfanonin wayoyin hannu sukayi wajen sauya duniya baki daya.

Birnin Zinder a wannan zamanin

gyara sashe
 
Zinder centre ville
 
Jami'ar Zinder

A yau Zinder ta kumshi wasu manyan bangarori guda uku wato Birni tsohon garin Hausawa kuma anan ne Gidan sarautar Zinder da babban Masallacin gari da kuma gidan adana kayan tarihi yake. Saikuma Zango ko kuma Zengou shine tsohon yankin da Abzinawa suke, amfi sanin yankin da Sabon gari. Tsakanin Birni da Zango akwai wata cibiyar kasuwanci wato babbar kasuwar Zinder. Birnin yanzu yana sairin bukasa ta bangaren Arewaci da Kudancin sa inda har ya kusa kaiwa ga wadansu garuruwa na makwabta kamar su Karkada, Garin mallam,Gawon kolliya. Akwai duwatsu a birnin sannan kuma birnin yayi kaurin suna wajen wahalar ruwa. Amma bayabayannan wani Kamfain kasar Sin ya samarwa da birnin hanyoyin ruwan sha na famfo daga yankin Arewaci. Dukda haka ana hasashen kara samun matsalar ruwa a birnin sakamakon karin hayayyafa. A shekarar 2011 ne aka samar da matatar mai ta farko a kasar Nijar kuma a birnin na Zinder.

Ginin tashar talabijin mai tsawon mita 250 a yankin Arewacin birnin shine gini mafi tsawo a Birnin Zender.

Yanayin Muhalli

gyara sashe

Birnin Zinder yana a gabas ga Maradi da nisan kimanin kilometa 236 kuma ya na nesa da babban birnin Niamey da kilometa 900. A Zinder yanayin zafi ya kai kimanin 30 na ma'aunin celsius (°C) a watanin disamba, Januari da kuma farkon Febrari. Kowace shekara akan yi ruwan sama masu kai kimanin milimita 411 (mm). Birnin ya kasu ne zuwa yankuna 5, Zinder 1, Zinder 2, Zinder 3, Zinder 4, Zinder 5.

Tattalin Arziki

gyara sashe
 
Kasuwar dole

Tattalin arzikin Zinder ya ta'allaka ne kan noma da kiyo. Kuma ya hada da kasuwanci da sufuri da en kere-kere. Babbar matatar man fetur guda tilo wadda Nijar ta mallaka kuma tana a kilometa 52 daga birnin Zinder. kashi 80 cikin dari wato 80% na mutanen Zinder suna aikin noma ne, kuma shi yasa kusan yawancin kaya da ke kawowa a kasuwannin Birnin Zinder kaya abinci ne. Babbar kasuwa a Zinder, ita ake kira Kasuwar Dolé wadda aka sake mata fasali na zamani a shekarar 2018.

Harkar Tafiye-Tafiye

gyara sashe
 
filin jirgin saman zinder na kasa da kasa

A kwai filin tashi da sukar giragen sama a kudu maso yammacin birnin (mai lamba ZND)

Zinder tana kumshe da al'adu da suka samu tushe daga tarihi da kuma zamantakewar mutanen Zinder. Wakokin galgajia ne suka fi samun karbuwa a Zinder, kamar kidan kalangu da busa. Salon waka wanda aka fi anfani da shi shi ne na gangara da kuma Rap. An samu mawaka en Zinder da suka shahara a Nijar da wajen Nijar kamar Sani Abussa, Dan Gana da kuma Ali Atchibili wanda shi ke tashe a yanzu. A fanin Rap kuma an samu mawaka kamar Black Power, DNR, Bach One da sauransu.

 
Stade de Zinder

Manazarta

gyara sashe