Christopher Nwankwo
Christopher Nwankwo (an haife shi a ranar 30 ga watan Satumban, shekara ta alif ɗari tara da arba'in da daya 1941A.c) Sanatan Najeriya ne, mai wakiltar gundumar Ebonyi ta Arewa a jihar Ebonyi. An zaɓe shi Sanata a zaɓen shekarar 2011, inda ya yi takara a kan tikitin jam’iyyar People’s Democratic Party.[1]
Christopher Nwankwo | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Najeriya |
Suna | Christopher |
Sunan dangi | Nwankwo (mul) |
Shekarun haihuwa | 30 Satumba 1941 |
Yaren haihuwa | Harshen, Ibo |
Harsuna | Turanci, Harshen, Ibo da Pidgin na Najeriya |
Sana'a | ɗan siyasa |
Muƙamin da ya riƙe | mamba a majalisar dattijai ta Najeriya |
Ilimi a | Jami'ar Najeriya, Nsukka |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheNwankwo ya sami takardar shedar Sakandare daga Kwalejin Iyali ta Holy Family a shekarar 1960 da Digiri na Farko daga Jami’ar Najeriya, Nsukka, a shekara ta 1965.[1]
Aikin Sanata
gyara sasheAn samu tashin hankali gabanin zaɓen Ebonyi ta Arewa a shekarar 2011 tsakanin magoya bayan jam’iyyar PDP da magoya bayan jam’iyyar All Nigeria People’s Party.[2] Christopher Nwanko ne ya lashe zaɓen gama gari.
An rahoto cewa Nwankwo ya fusata ne game da wani shiri na tituna da ya biyo bayan tsari da kuma jefa masu ababen hawa cikin haɗari.[3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 https://archive.ph/20130630075552/http://senatorchrisnwankwo.com/index.php?option=com_content&view=article&id=60&Itemid=27
- ↑ https://web.archive.org/web/20160305104043/http://www.citizensadvocatenews.com/index.php/politics/12-campaigns-in-ebonyi-become-tougher
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2018-04-06. Retrieved 2023-04-09.