Chike Obi
Chike Obi (an haifeshi ranar 17 ga watan Afrilu, 1921 - ya mutu a ranar 13 ga Maris na shekarata 2008) ɗan siyasan Nijeriya ne, masanin lissafi kuma farfesa.
Chike Obi | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Chukwunwike Obi |
Haihuwa | Zariya da Jahar Anambra, 17 ga Afirilu, 1921 |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa |
Harshen, Ibo Hausa |
Mutuwa | Onitsha, 13 ga Maris, 2008 |
Ƴan uwa | |
Yara |
view
|
Karatu | |
Makaranta |
University of Cambridge (en) 1950) Christ the King college Onitsha (1935 - 1939) Yaba College (en) (1940 - 1942) University of London (en) (1940 - 1946) Pembroke College (en) (1947 - 1950) |
Thesis | ' |
Thesis director |
John Edensor Littlewood (mul) Mary Cartwright (mul) |
Harsuna |
Turanci Harshen, Ibo Hausa |
Sana'a | |
Sana'a | masanin lissafi, maiwaƙe da ɗan siyasa |
Employers |
Jami'ar Ibadan (1951 - 1962) Jami'ar jahar Lagos (1970 - 1985) |
Kyaututtuka |
gani
|
Mamba | Makarantar Kimiyya ta Najeriya |
Sunan mahaifi | Cantamanto |
Imani | |
Jam'iyar siyasa |
Majalisar Najeriya da Kamaru Jam'iyyar Dynamic |
African Mathematics Union ta ba da rahoton cewa shi ne ɗan Najeriya na farko da ya fara karatun digirin digirgir a fannin lissafi.
Obi ya rubuta littattafai da dama da mukalu kan lissafi da siyasar Najeriya.
Karatu
gyara sasheObi ya yi karatu a sassa daban-daban na Najeriya kafin ya karanta lissafi a matsayin dalibi na waje a Jami'ar London. Nan da nan bayan ya gama digirinsa na farko, ya samu kyautar gurbin karatu don yin karatu a Kwalejin Pembroke, Cambridge, sannan kuma yayi karatun digirin digirgir a Massachusetts Institute of Technology. a cikin Cambridge, Massachusetts, Amurka, ya cimma hakan ne a shekarar 1950 inda ya zamo ɗan Nijeriya na farko da ya karɓi PhD a fannin lissafi.
Lambobin yabo
gyara sasheKasantuwar sa farfesa dake koyarwa a Jami'ar Rhode Island, Amurka, Jami'ar Jos, Najeriya, da kuma Kwalejin Kimiyya ta China, Obi ya taɓa samun lambar girmamawa ta ƙasa ta Kwamandan Doka na Najeriya (CON) kuma ɗa ne ga Makarantar Kimiyya ta Nijeriya.
Rayuwar Iyali
gyara sasheLokacin da Obi ya mutu a shekarar 2008 ya bar matarsa wanda ta rayu har zuwa shekarar 2010. Matar Obi Belinda wadda ta kasance ma'aikaciyar jinya ce ita ma ta mutu a farkon shekarar 2010 inda suka bar yara huɗu.