Boris Johnson
Alexander Boris de Pfeffel Johnson (an haife shi a 19 ga watan Yuni shekara ta 1964) Ɗan siyasan Biritaniya ne, tsohon ma'aikacin jarida ne kuma a baya ya riƙe Firayim Minista na United Kingdom kuma Shugaban Jam'iyar Conservative Party tun a watan Yulin 2019.[1] Ya kasance Member of Parliament (MP) dake wakiltar Uxbridge da Kudancin Ruislip tun 2015, ya kuma riƙe MP na Henley daga 2001 zuwa 2008. Shi ne kuma Mayor na London dga 2008 zuwa 2016, sannan Foreign Secretary daga 2016 zuwa 2018. Johnson dai ana ganin sa a matsayin one-nation conservative da kuma danganta shi da gudanar da siyasa wadda take da sassauci ta fuskar tattalin arziki da kuma zamantakewa.
Tarihin rayuwa
An haife shi a New York City daga gidan masu hannu da shuni, Johnson ya yi karatu a European School, Brussels I, Ashdown House, da Eton College. Ya karanci Classics a Balliol College, Oxford, inda aka zaɓe shi President of the Oxford Union a 1986. Ya fara gudanar da harkar rayuwarsa a matsayin ma'aikacin jaridar The Times amma sai aka kore shi da cusa wani magana ta karya. Daga nan ya koma The Daily Telegraph's mai rahoto daga Brussels.
-
Boris na kallon was an Paralympic
-
Boris na Jawabin
-
Boris da kaninsa Leo
-
Shugaba Boris Johnson da sarki Abdullah II na Jordan
-
Shugaba Boris Johnson da shugaba Neranda Modi
-
Boris tare da shugaba Macron
Manazarta Gyara
- ↑ Lawless, Jill; Kirka, Danica (23 July 2019). "Boris Johnson chosen as new UK leader, now faces Brexit test". AP NEWS. Retrieved 23 July 2019.