Ɗan jarida
Ɗan jarida shi ne mai samo labarai yana yaɗawa a gidajen talabijin, rediyo da kuma jaridu. Ana samun Ɗan jarida mai zaman kansa ko kuma wanda zai rinƙa yima wata kafar yaɗa labarai, Rediyo ko Talabijin aiki. Akwai ire-iren Yan jaridu kamar, Mai rahoto (wanda yake bincike kuma ya rubuta sannan ya kawo rahoto.) ƴan jaridu suna rubuta labarai da sharhi ga kafafen yaɗa labaru. Suna yin bincike ne da hira da mutane da tambayoyi wajen rubuta labaru da rahotanninsu. Dolene masu rubuta labarai da sharhi su zama masu faɗin gaskiya. Faɗin gaskiya yana da matukar muhimmancin gaske ga aikin jarida. Idan Ɗan jarida ya zama baya faɗin gaskiya a labaransa ko kuma rahotanninsa to yakan fuskanci hukunci na dakatarwa ko ma kora baƙi ɗaya.
![]() | |
---|---|
sana'a, sana'a, occupation group according to ISCO (en) ![]() ![]() | |
![]() | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na |
media professional (en) ![]() ![]() ![]() ![]() |
Field of this occupation (en) ![]() |
journalism (en) ![]() ![]() |
ISCO-08 occupation code (en) ![]() | 2642 |
ISCO-88 occupation code (en) ![]() | 2642 |
Haɗari ga Ɗan JaridaGyara
Sau da yawa ƴan Jarida kan samu kawunansu a haɗura, musamman ma wajen da ake samun rikicin ta'addanci ko fagen yaƙi. Hakanan daga cikin hatsari na aikin jarida akwai rashin samun ƴancin yin aikin samo rahoto a wasu ƙasashe. Kuma Wani Kwamiti mai kare Ƴan Jarida ya yi rahoton cewa daga 1 ga Disamba na 2010, akwai ƴan jaridu 145 da ke a ɗaure a faɗin duniya. Ƙasashe goma waɗanda aka fi samun ƴan jarida a gidan kurkuku sune Turkiyya (95),[1] Sin (34), Iran (34), Eritrea (17), Burma (13), Uzbekistan (6), Vietnam (5), Cuba (4), Ethiopia (4), da Sudan (3.[2]
Rabe raben aikin jaridaGyara
Akwai rabe-rabe masu yawa a aikin jarida.
- Akwai mai rubutu da nazarin labarai.
- Akwai mai rahoto na nesa, wanda ke ɗauko rahoto ga rediyo ko talabijin daga wani gari mai nisa koma daga wata ƙasar.
- Akwai kuma Ɗan jarida mai duba gyare-gyare da yadda labari yake.
- Akwai kuma wanda shi aikinsa duba kuskuren rubutu.
- Akwai kuma wanda ke gabatar da labarai.
- Akwai mai ɗaukar hoto.
ManazartaGyara
- ↑ "Number of Jailed Journalists Nearly Doubles in Turkey". Los Angeles Times. 5 April 2012. Retrieved 6 April 2012.
- ↑ Iran, China drive prison tally to 14-year high. "Iran, China drive prison tally to 14-year high (December 8, 2010). Committee to Protect Journalists. Retrieved November 18, 2011". Cpj.org. Retrieved 2013-04-16.