Blessing Onyeche Onuh (an haife ta a ranar 30 ga watan Yuni shekara ta alif ɗari tara da saba'in da shida1976A.C) 'yar siyasan Nijeriya ce daga Jihar Benue.[1] Tana wakiltar Mazabar Tarayya ta Otukpo/Ohimini a Majalisar Wakilai. Ta kasance diya ga tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya David Mark.[2]

Blessing Onuh
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

8 Disamba 2020 -
District: Otukpo/Ohimini
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

11 ga Yuni, 2019 - 8 Disamba 2020
District: Otukpo/Ohimini
Rayuwa
Haihuwa Jahar Benue, 30 ga Yuni, 1976 (48 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar jahar Lagos
Jami'ar Abuja
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Grand Alliance

Kuruciya da Ilimi

gyara sashe

An haifi Blessing Onyeche Onuh a ranar 30 ga watan Yunin, 1976 a Otukpo, Jihar Benue ga iyalin David Mark na Akpegedde-Otukpo. A cikin 1988, ta sami takardar shedar kammala makarantar farko daga makarantar firamaren St. Andrew, Otukpo. Sannan ta halarci Kwalejin 'Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya da ke Gboko kuma ta kammala a shekarar 1995. Sannan kuma, ta samu gurbin karatu a fannin ilimin zamantakewar dan adam a Jami'ar Abuja a shekarar 1995 kuma ta kammala da digirin ta na farko a shekarar 1999. A yanzu haka tana karatun digirinta na uku a fannin nazarin jinsi a jami’ar Abuja. [3]

Bayan kammala digiri daga Jami'a, Blessing Onuh ta zarce bautar kasa na shekara guda inda ta yi aiki a Sashen Noma na Babban Bankin Najeriya a Jos, Jihar Filato, daga 2000 zuwa 2001. A shekarar 2005, an nada ta Mataimakiya na musamman ga karamin ministan ilimi. Daga baya an nada ta a matsayin mataimakiya ta musamman ga Minista na tsakanin Gwamnatoci, Kananan Hukumomi da Ayyuka na Musamman. Yayin da take wannan mukamin, ta yi aiki a matsayin Shugabar riko, Kwamitin Babban Birnin Tarayya kan Rahama da yafiya.

Sannan aka naɗa ta sakatariyar walwala da jin daɗi na Babban Birnin Tarayya. A shekarar 2018, ta yi takarar dan majalisar wakilai na mazabar Otukpo/Ohimini a karkashin jam'iyyar People's Democratic Party a jihar Benue amma ta rasa zaben a zaben share fage ga kawun ta Johnson Ahubi.[4] Ta bar jam’iyyar ta koma jam'iyyar APGA.[5] Daga nan ta yi takara da APGA sannan ta zama mamba a majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Otukpo/Ohimini.[6][7]A cikin watan Febrerun 2021, Onuh ta koma jam'iyyar APC, bayan ta hangi matsaloli a jagorancin jam'iyyar APGA.[8]

Rayuwar Kai

gyara sashe

Blessing ta auri Dakta Innocent Onuh, wani likita ne daga Obotu-Ugboju, karamar Hukumar Otukpo a shekarar 1999. Ubangiji ya albarkaci auren da kyawawan yara guda uku.[9]

Manazarta

gyara sashe
  1. "BREAKING: David Mark's daughter, Bauchi Rep join APC". The Nation Newspaper. 2021-02-16. Retrieved 2022-02-21.
  2. "Salaudeen, Omoniyi (7 July 2019). "Face of politicians in self-succession scheme". Sun News. Retrieved 22 November 2020.
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-11-29. Retrieved 2020-11-22.
  4. Anonymous (18 October 2018). "David Mark's daughter, Blessing Onuh dumps PDP after losing Reps ticket". Daily Post. Retrieved 22 November 2020.
  5. "Oloja, Martins (3 March 2019). "2019 Elections: Some consequences and lessons". Guardian. Retrieved 22 November 2020.
  6. Editorial (20 November 2018). "David Mark's daughter pulls 15,000 supporters to APGA". Blueprint. Retrieved 22 November 2020.
  7. Ochayi, Chris (26 February 2019). "David Mark's daughter wins Reps seat under APGA". Vanguard. Retrieved 22 November 2020.
  8. "Two Reps defect to APC". Premium Times. 16 February 2021. Retrieved 2 November 2021.
  9. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-11-29. Retrieved 2020-11-22.