Ayo Fasanmi

Mai harhada magunguna na Najeriya kuma dan siyasa.

Ayorinde Fasanmi (an haife shi a ranar 27 ga watan Satumban shekara ta 1925 [1] [2] - ya mutu a ranar 29 ga watan July na shekara ta 2020) ya kasance masanin harhada magunguna kuma dan siyasa na Nijeriya.[3][4][5][6][7][8]

Ayo Fasanmi
Rayuwa
Haihuwa Ekiti, 1925
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Mutuwa 29 ga Yuli, 2020
Karatu
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Rayuwar farko gyara sashe

An haife shi a shekara ta 1925 a garin Iye Ekiti, ƙaramar hukumar ta jihar Ekiti, kudu maso yammacin Najeriya . Ya halarci makarantar firamare ta St Paul, Ebutte Metta da kuma Makarantar Gwamnati, Ibadan kafin ya zarce zuwa Makarantar harhada magunguna ta Yaba inda ya sami takardar difloma a fannin harhada magunguna. Ya yi aiki a matsayin mai harhaɗa magunguna a Oshogbo a takaice kafin ya shiga siyasar Najeriya.

Harkar siyasa gyara sashe

Ya shiga jam'iyyar Unity Party of Nigeria a shekara ta 1978 kuma ya kasance dan takara a zaben fidda gwani na gwamnan jihar Ondo amma ya kayar da Michael Adekunle Ajasin, tsohon gwamnan jihar Ondo. A shekara ta 1983, an kuma zaɓe shi dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Ondo ta Arewa. Daga baya ya yi aiki a matsayin memban Hukumar Gudanarwa na Kamfanin Kula da Gidaje na Old Western Nigeria. A lokacin Jamhuriyyar Najeriya ta Hudu, ya yi aiki a matsayin Mataimakin Shugaban Kasa na Alliance for Democracy, shiyyar Kudu maso Yamma. [9][10][11][12][13]

Rayuwar mutum gyara sashe

Ya auri marigayi Madam Adejoke wacce ta mutu tana da shekara 82 a cikin watan Oktoban shekara ta 2014.

Manazarta gyara sashe

 

  1. [1]
  2. https://www.pulse.ng/news/local/pa-ayo-fasanmi-afenifere-national-leader-dies-at-94/rrvh9jy
  3. [2]
  4. https://www.pulse.ng/news/local/pa-ayo-fasanmi-afenifere-national-leader-dies-at-94/rrvh9jy
  5. "Fasanmi, factional leader, threatens on Afenifere crisis : I". NigerianMuse. Retrieved 24 February 2015.
  6. "Afenifere's Comeback Bid, Articles - THISDAY LIVE". thisdaylive.com. Archived from the original on 22 February 2015. Retrieved 24 February 2015.
  7. Latestnigeriannews. "I never discussed Bola Ige with Olaniwun Ajayi -Ayo Fasanmi". Latest Nigerian News. Retrieved 24 February 2015.
  8. "Obasanjo/Iyabo feud: Why we won't intervene— Yoruba elders - Vanguard News". Vanguard News. Retrieved 24 February 2015.
  9. "Archived copy". Archived from the original on 2015-02-22. Retrieved 2015-02-22.CS1 maint: archived copy as title (link)
  10. "Fasanmi urges Afenifere leaders to support APC". Daily Independent, Nigerian Newspaper. Archived from the original on 22 February 2015. Retrieved 24 February 2015.
  11. "Yoruba leaders should forge a synergy –Senator Ayo Fasanmi - P.M. NEWS Nigeria". pmnewsnigeria.com. Retrieved 24 February 2015.
  12. "Yoruba Elites and Ethnic Politics in Nigeria". google.co.za. Retrieved 24 February 2015.
  13. Our Reporter. "Fasanmi bags award". thenationonlineng.net. Retrieved 24 February 2015.