Asabe Vilita Bashir
Asabe Vilita Bashir (an haifeta a ranar 19 ga watan Faburairu, shekara ta alif ɗari tara da sittin da biyar 1965A.c) a ƙauyen Limankara da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar gwoza,ta kasance mace yar siyasa a Najeriya. An zaɓe ta a matsayin mace mai wakiltar Gwoza, Chibok da ke jihar Borno. Yar siyace a ƙarƙashin jam'iyyar APC dake wakiltan Gwoza, Chibok da kuma Damboa na jihar Borno. Ta kuma goyi bayan samar da adalci ga majiyatan rikicin Boko Haram.
Asabe Vilita Bashir | |||
---|---|---|---|
9 ga Yuni, 2015 - District: Damboa/Gwoza/Chibok | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Jihar Borno, 19 ga Faburairu, 1965 (59 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Jami'ar Maiduguri academic degree (en) Master of Education (en) : karantarwa academic degree (en) Digiri a kimiyya : karantarwa academic degree (en) Doctor of Philosophy (en) | ||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Ilimi
gyara sasheBashir ta karɓi takardar shedar karatun ta na GCE daga Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke jihar Maiduguri a shekarar 1984. Daga nan sai ta shiga Jami'ar Maiduguri don karatun koyarwa. An ba ta sakamakon BSc na Koyarwa (Education) a cikin shekarar 1988, da MEd a Gudanarwa da Tsare-tsare a shekarar 1992, da kuma Ph.D. a cikin Falsafa a shekarar 2002.[1]
Ayyuka
gyara sasheTa kasance mamba a Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya,[2] wakiltar mazabar Gwoza, Chibok da Damboa a jihar Borno .[3] Tana yin shawarwari kan aikin da zai inganta rayuwar wadanda rikicin Boko Haram ya shafa, musamman mata da yara.[4][5]
Manazartani
gyara sashe- ↑ "Hon. Asabe Vilita Bashir: Education". National Assembly. Federal Republic of Nigeria. Archived from the original on 10 June 2019. Retrieved 14 June 2018.
- ↑ Biography of Asabe Vilita Bashir". Nigerian Biography. 16 December 2015. Retrieved 26 May 2018.
- ↑ "Biography of Asabe Vilita Bashir". Nigerian Biography. 16 December 2015. Retrieved 26 May 2018.
- ↑ Editor. "Lawmaker to Aisha Buhari: Start a pet project on Boko Haram victims". The Cable. Retrieved 26 May 2018.CS1 maint: extra text: authors list (link)
- ↑ Victor Oluwasegun, Dele Anofi. "Reps to FG: Reopen schools in Borno, Yobe, Adamawa". The Nation. Retrieved 26 May 2018.