Alwali Kazir
Alwali Jauji Kazir CFR (an haife shi ranar 2 ga watan Agusta, 1947) Manjo Janar ne na sojan Najeriya mai ritaya wanda ya kasance Gwamnan Soja a Jihar Kwara, Najeriya daga Disamba 1989 zuwa Janairu 1992 a lokacin mulkin soja na Manjo Janar Ibrahim Babangida. Sannan kuma shugaban hafsan soji daga Agusta 1994 zuwa Maris na shekarar 1996 a lokacin mulkin Janar Sani Abacha.
Alwali Kazir | |||||
---|---|---|---|---|---|
ga Augusta, 1994 - ga Maris, 1996
Disamba 1989 - ga Janairu, 1992 ← Ibrahim Alkali (en) - Mohammed Shaaba Lafia → | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Jihar Yobe, ga Augusta, 1947 (77 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Karatu | |||||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Kazir a ƙauyen Kazir, ƙaramar hukumar Jakusko a jihar Yobe a yau. Ya halarci Makarantar Firamare ta Amshi tsakanin 1955 zuwa 1957 da Gashua Central Primary School a 1958.
Aikin soja
gyara sasheA matsayinsa na Birgediya Janar, ya kasance daraktan tsangayar aikin soja a kwamandan runduna da kwalejojin ma’aikata na Jaji a shekarar 1992. Bayan korar Manjo Janar Chris Alli kwatsam daga muƙamin Hafsan Hafsoshin Soja, Alwali Kazir daga nan ya samu muƙamin Major-Janar na GOC 1 ya kuma naɗa babban hafsan soji daga Agusta 1994 zuwa Maris 1996 a lokacin mulkin Janar Sani Abacha. Alwali Kazir yayi ritaya a shekarar 1996.
Bayan ritaya
gyara sasheBayan ya yi ritaya, Sarkin Bade Alhaji Abubakar Umar Suleiman ya naɗa shi Madakin Bade a watan Afrilun shekara ta 2009.
Iyali
gyara sasheAlwali Kazir ya auri Marigayiya Aisha Larai Bukar, wadda take da ɗa ɗaya tare da shi, mai suna Muhammad, sai kuma Hajara-(mata ta biyu) wadda take da ‘ya’ya 6 tare da shi-(mijin): Halima, Abdulazeez, Ibrahim, Musa, Mubarak da Maryam, sai kuma jikoki 10: Alwali (Najeeb), Aisha. Hajara (Nabila), Maryam, Amina, Muhammed, Abubakar, Hajara (Deena), Ayman da Halimatu Sa'diyyah.