Aliyu Ahman Bahago (An haife shi a ranar 31 ga watan Disamban shekara ta 1964), [1] ɗan siyasan Nijeriya ne. Shi memba ne na majalisar wakilai ta tarayya don EduMoro . [2]

Aliyu Ahman-Pategi
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

Rayuwa
Haihuwa 1964 (59/60 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Rayuwar farko gyara sashe

Mahaifinsa ya kasance tsohon Ministan Lafiya da Noma Ahman Pategi, a lokacin Ahmadu Bello, yana mulki. [3]

Ya halarci makarantar firamare Patigi, kuma ya yi makarantar sakandare ta gwamnati a Ilorin a shekara ta 1976 -81. Ya kuma kammala Karatun Basic 1981–82. Ya sami BS'c a kan Nazarin Duniya a Jami'ar Ahmadu Bello a shekara ta 1982-85. Shi kuma MS'c a fannin Tattalin Arzikin Siyasa da Nazarin Bunkasawa a Jami’ar Abuja, 2000 - 02. [4]

Ayyuka gyara sashe

Ya fara a matsayin Babban Jami'in Kamfanin Platform Nigeria Limited, a Ahmann Patigi Farms. Ya yi aiki a matsayin Darakta a Tranex kuma Shugaban reshe na Kungiyar Bayar da Agaji ta Jihar Kwara. Aliyu Ahman Ya kasance Wakili na Majalisar Wakilai ta Tarayya a Kasa, Ya yi zama sau uku a Edu Moro, Pategi, mazabar Tarayya ta Kwara ta Arewa ,. [5] ya taba zama Shugaban Kwamitin Majalisar kan Albarkatun Ruwa sau biyu, sannan kuma Shugaban, Binciken kasafin kudi. Ya kasance memba na sauran kwamitocin kan Kasafin Kudi da Kasuwanci. [6]

Manazarta gyara sashe

  1. books html "about aliyu ahman", Google Books, 2016
  2. "member house of rep", EveryPolitician, 2016
  3. ade the admin html "about aliyu pategi" Archived 2021-06-07 at the Wayback Machine, Madian Nigeria, 2017
  4. nass gov admin html" aliyu ahman" Archived 2019-08-14 at the Wayback Machine, nigeria biography, 2017
  5. admin post "list of member rep", NG Gallery, 2017
  6. member data html "hon ahman aliy", NASS, 2015