Al’adun Arewacin Najeriya, galibi sun mamaye al’adun masarautu goma sha hudu da suka mamaye yankin a zamanin kafin tarihi, amma kuma waɗannan al’adu suna da tasiri matuƙa a kan al’adun ƙabilu sama da ɗari da ke zaune a mabanbanta yankin.

Al'adun Arewacin Najeriya
culture of an area (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na Al'adun Najeriya na gargajiya
Facet of (en) Fassara Arewacin Najeriya
Ƙasa Najeriya
Wuri
Map
 9°19′14″N 13°23′44″E / 9.3206°N 13.3956°E / 9.3206; 13.3956
 
Helon Habila ta Arewacin Najeriya

Arewacin Najeriya ya gaji da yawa daga cikin abubuwan adabi na tsohuwar jihohin Sudan. Sarakunan Hausawa daga ƙarni na 9 zuwa na 18 sun samar da ayyukan adabi da dama.[1] Dubban irin waɗannan ayyuka galibi a cikin harsunan Ajami, Hausa da Larabci har yanzu ba a lissafta su a duk Arewacin Najeriya.[2] Tun lokacin da daular Birtaniyya ta yi wa mulkin mallaka, Ingilishi da rubutun Latin sun maye gurbin rubutun Ajami. Ana kallon Abubakr Imam Kagara a matsayin ɗaya daga cikin uban adabin Arewacin Najeriya na zamani,[1] Ayyukansa irin su Ruwan Bagaja da Magana Jari Ce, wanda aka buga a shekarun 1930, sun kasance wata gada tsakanin tsohuwar al'adar adabin Sudan da hanyoyin yamma.

Sauran irin su Yabo Lari da Muhammed Sule – marubucin The Undesirable Element – sun ba da gudummawa daidai gwargwado a cikin shekarun 1960. A shekarun 1980 fitattun marubutan da suka haɗa da Abubakar Gimba da Zaynab Alkali sun yi aiki don raya al’adun adabin Arewa da kuma bambanta da kudancin Najeriya.[1] A shekarun 1990 ne aka samu fitowar marubuta daga Abubakar Othman, Ismail Bala da Ahmed Maiwada a cikin waƙoƙi ga Maria Ajima da Victor Dugga a wasan kwaikwayo. Adabin Arewacin Najeriya na zamani ana yin su ne a Kano, Kaduna, Jos da Minna. Marubuta irin su BM Dzukogi, Ismail Bala, Yusuf Adamu, Musa Okapnachi, Razinat Mohammed da E.E. Sule suna nan suna aiki.[1]

Yayin da tsohuwar al’adar Sudan ta fi mayar da hankali kan waƙa ko waƙe-waƙe, tun daga shekarun 1950 shigowar tasirin Birtaniya ya yi haɓɓaka kiɗan Arewacin Najeriya.[3] Dan Maraya Jos, Mamman Shata, Barmani Choge, Aliyu Dan Kwairo da wasu da dama ana ɗaukar su a matsayin waɗanda suka kafa irin salon waka na musamman a Arewacin Najeriya.[3] Wasu irin su Fatima Uji sun ci gaba da shahara. Tun a shekarun 1990 tasirin al'adun salon wakar pop ya haifar da ƙaruwar mawakan R&B na Arewacin Najeriya. Mawaƙan Arewacin Najeriya da suka haɗa da Adam Zango, Ice Prince Zamani, Idris Abdulkareem da Sarki Bawa sun shahara a duk faɗin Afirka.

Masana'antar fina-finai ta Arewacin Najeriya, wacce aka fi sani da Cinema ta Hausa, ta kasance ɗaya daga cikin masana'antar fina-finai ta farko ta kasuwanci a yankin kudu da hamadar Sahara. Manyan ‘yan jarida da ‘yan wasan kwaikwayo daga Rediyo Kaduna da RTV Kaduna ne suka ƙirƙiro masana’antar a shekarun 1950. A yau jarumai irin su Ali Nuhu, Adam A Zango, Sani Danja, da Ibrahim Maishukku sun shahara a yankin. Tun daga shekarun 1990 da kuma tafiyar hawainiya na dalilin ra'ayin addinin Musulunci ta hanyar yaƙin neman zaɓe na kungiyar Izala, fina-finan Arewacin Najeriya ya gamu da koma baya sosai, kuma yanzu takwarorinsu na Kudancin Najeriya sun musu nisan kiwo.

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 Ali, Richard Ugbede. "On Northern Nigerian Literature And Related Issues". Archived from the original on 2015-01-02. Retrieved 2014-11-11.
  2. Auyo, Musa; Mohammed, Ahmed (2009). "The Prevalence of Arabic and Ajami Manuscripts in Northern Nigeria, Implications for Access, Use, and Enduring Management: A Framework For Research". National Conference on Exploring Nigeria's Arabic/Ajami Manuscript Resources for Development of New Knowledge.
  3. 3.0 3.1 Adah, Abah; Chiama, Paul. "Northern Nigeria's Music Legends". leadership.ng. Retrieved 2014-11-11.