Abubakar Gimba (An haife shine a garin lapai, Jahar Niger) . Ya fara makarantar sa a Gulu Primary School daga shekara ta alif 1959 zuwa alif 1962, sannan ya je Senior Primary School Lapai ya gama a shekara ta alif 1964 kuma ya ci gaba inda ya sami takardar kammala kwaleji ta Government College Keffi daga alif 1965 zuwa alif 1969,Daga nan yayi jami'ar Ahmadu Bello Zaria daga shekara ta alif 1970 Har zuwa shekara ta alif 1974 inda yayi digirin shi na daya da na biyu, Sannan kuma ya halarce jami'ar Cincinmati wato University of Cincinmati a 1977 sai jami'ar lowa wato University of Iowa don program service.[1][2]

Abubakar Gimba
Rayuwa
Haihuwa Jahar Nasarawa, 10 ga Maris, 1952
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Mutuwa Minna, 12 ga Faburairu, 2015
Karatu
Makaranta University of Cincinnati (en) Fassara
Jami'ar Ahmadu Bello Bachelor in Economics (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Malami, Marubuci, Mai tattala arziki, maiwaƙe da columnist (en) Fassara
Muhimman ayyuka Witnesses to tears (en) Fassara
Innocent Victims by Abubakar Gimba (en) Fassara

Abubakar Gimba yayi aiki a bankin Union sai kuma United Bank of Africa a matsayin darakta me cikakken iko. Kafin ya fara kasuwanci Ya kasance ma'aikacin gwamnati wanda ya samu daukaka a tsakanin abokan aikinsa zuwa sakatare na dindindin a ma'aikatan kudi a lokacin David Mark tsakanin 1984 zuwa 1987. Bayan ajiye aikin sa daga hidimar bankuna, an sa cikin masu aiki ko bada shawara wasu bangaren public institutions. An ba Gimba mukamin shugaban kwamitin ladabtarwa ta jami'ar Ahmadu Bello, lokacin makarantan yana tsakanin mulkin Mamman Kontagora.Daga nan sai, Abdussalami Abubakar ya sa shi cikin wani kwamiti wato [Programme Implementation Monitoring Committee] har karshen lokacin shi a 1999. Gimba tsohon shugaban kungiyar tsofaffin daliban jami'ar Ahmadu Bello, wato Ahmadu bello University alumni association .Sannan kuma daya daga cikin memba na Ahmadu Bello University Governing Council daga 2002 zuwa 2006. Shine farkon shugaban jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida Lapai. Ya zama me bada shawara ga shugaban majalisa David Mark akan tattalin arziki da abin da ya shafi kasafin kudi a shekara ta alif 2010, sannan ya kasance me bada shawara akan abubuwa da dama.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Abubakar Gimba died after a period of illness – Faces International Magazine" (in Turanci). Archived from the original on 2020-06-22. Retrieved 2020-06-21.
  2. "Abubakar GIMBA | The International Writing Program". iwp.uiowa.edu. Retrieved 2020-06-21.