Ahmad Sulaiman Ibrahim

Mahaddacin Alqur'ani ɗan Najeriya

Ahmad Sulaiman Ibrahim wanda aka fi sani da Alaramma Ahmad Sulaiman, an haife shi ne a shekara ta alif dari tara da sittin da shida miladiyya (1966), Mahaddacin Alqur'ani ne kuma ɗan Najeriya ne, Malamin Addinin Musulunci ne, kuma Shahararren Masanin Alqur'ani mai girma ya samu lambobin yabo da dama a fadin duniya saboda bajintarsa wajen sanin Alqur'ani mai girma. Shaikh Ahmad Sulaiman ya kuma shahara wajen sarrafa harshe a yayin da yake rera AlQur'ani, don mutane da dama daga sassan duniya suna son muryarsa, haka kuma yayin da wasu suke kwaikwayon salon karatunsa. Malam Ahmad Sulaiman yayi Musabaƙa ta duniya har kusan sau 3 yana cin na 1, wannan yasa mutane suke ganin yana daga cikin masana Alqur'ani na duniya, ba wai Najeriya kadai ba.[1]

Ahmad Sulaiman Ibrahim
Rayuwa
Haihuwa 1966 (57/58 shekaru)
Sana'a

Farkon Rayuwar shi

gyara sashe

An kuma haifi Ahmad Sulaiman a gidan sulaiman, mahaifinsa ya rasu tun yana ɗan shekara 6, sannan ya koma jihar Kano yana ɗan shekara 9 don neman ilimin Addini da kuma na zamani (Boko), Ahmad Sulaiman ya haddace Alqur'ani tun yana ƙarami. Haka yana cewa Dr Kabir Haruna Gombe yana cikin malamansa kuma Alarammansa a lokacin tafsirin Watan Ramadan, duk da cewa kusan duk inda Sheikh Kabir Haruna Gombe zaije wa'azi suna tareda Alaramma Ahmad Sulaiman, Ahmad Sulaiman mamba ne a ƙungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah wa Iqamatus Sunnah, babbar ƙungiyar Salafiyyah dake Najeriya.

Garkuwa da Sheikh Ahmad Sulaiman

gyara sashe

A watan Maris ɗin shekara ta 2019 ne wasu masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da Sheikh Ahmad Sulaiman a hanyarsa ya fito mahaifarsa zai koma zuwa jihar Kano bayan ziyarar da ya kai a jihar Kebbi. Garkuwa dashi tazo gab da yana shirin aurar da ƴa-ƴansa mata biyu, an yi awon gaba da shi tare da wasu mutane biyar a ƙaramar hukumar Sheme/Ƙanƙara wadda wannan yana cikin yakin jihar Katsina.[2][3][4][5] An sako Sheikh bayan kwanaki 15 da garkuwa dasu.[6][7][8][9]

Kwamishinan Ilimi a Kano

gyara sashe

Dr Abdullahi Umar Ganduje gwamnan jihar Kano na wancan lokacin ya naɗa Ahmad Sulaiman a matsayin kwamishinan Ilmi na biyu a jihar Kano.[10][11][12]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Qaari - Shaikh Ibrahim Ahmad Sulaiman". dawanigeria.com. Retrieved 18 January 2022.
  2. Adewale, Kano, Murtala (27 March 2019). "Sheikh Ahmad Sulaiman regains freedom after 15 days in captivity". guardian.ng. Archived from the original on 17 January 2022. Retrieved 17 January 2022.
  3. "Kano famous Sheikh, five others regain freedom". channelstv.com. 27 March 2019. Retrieved 17 January 2022.
  4. Adamu Yahaya, Nasidi (29 May 2019). "How Nigeria and its president are being held to ransom". bbc.news.com. Retrieved 17 January 2022.
  5. "Kidnappers of 'Buhari's prayer-warrior' demand N300m ransom". premiumtimesng.com. 19 March 2019. Retrieved 17 January 2022.
  6. "Kidnappers of Buhari's prayer-warrior, Sheikh Sulaiman, demand N300m ransom". Vanguardngr.com. 19 March 2019. Retrieved 17 January 2022.
  7. Ososanya, Tunde (20 March 2019). "Kidnappers of prayer warrior Sheikh Sulaiman demand N300m for his release". legit.ng. Archived from the original on 17 January 2022. Retrieved 17 January 2022.
  8. "Sheikh Sulaiman: Kidnappers of Buhari's Prayer-Warrior Demand N300m Ransom". prnigeria.com. 19 March 2019. Retrieved 17 January 2022.
  9. Adewale, Kano, Murtala (16 March 2019). "Kano Islamic clergy, five others kidnapped". the guardian.ng. Archived from the original on 17 January 2022. Retrieved 17 January 2022.
  10. Khalid, A'isha (4 December 2021). "Labari cikin hotuna: Ganduje ya nada Alaramma Ahmad Sulaiman kwamishinan ilimi 2". legit.hausa.ng. Retrieved 17 January 2022.
  11. "Sheikh Ahmad Sulaiman Bags New Political Appointment As The Commissioner For Education, Kano State". opera.news.ng. Archived from the original on 18 January 2022. Retrieved 17 January 2022.
  12. Khalid, Aisha (6 December 2021). "Hotuna cikin labari: Alaramma Ahmad Sulaiman ya shiga ofis, ya mika godiya ga Allah". legit.hausa.ng. Retrieved 17 January 2022.