Adil al-Kalbani ( Larabci: عادل الكلباني‎ ) Malamin addinin Musulunci ne ɗan asalin ƙasar Saudiyya, wanda ya kasance limamin babban masallacin Makkah.[1][2][3]

Adil al-Kalbani
Rayuwa
Haihuwa Riyadh, 3 ga Afirilu, 1959 (65 shekaru)
ƙasa Saudi Arebiya
Harshen uwa Larabci
Karatu
Makaranta King Saud University (en) Fassara
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a Liman
Imani
Addini Mabiya Sunnah

Tarihin rayuwa gyara sashe

An haifi Adil al-Kalbani a birnin Riyadh a ranar 4 ga watan Afrilu, shekara ta 1958 gidan su sun kasance talakawa kuma waɗanda sukayo hijira daga Ras Al Khaimah na Hadaddiyar Daular Larabawa wadanda suka zo Saudiyya a shekarun 1950. Saboda halin babu da Ahalinsa suke ciki, al-Kalbani ya samu aiki da kamfanin jirgin saman Saudi bayan ya kammala makarantar sakandare, a lokacin kuma fara halartar darussan yamma a Jami'ar Sarki Saud.

Malamin farko da Al-Kalbani ya fara yi a karatuttukansa na Musulunci shi ne Hasan bn Gaanim al-Gaanim. Ya karanci Sahihul Bukhari da Jami` at-Tirmidhi da tafsirin Ibn Kathir a wurinsa. Ya kuma yi karatu a wurin Mustafa Muslim wanda ya koyar da tafsirin al-Baydawi a jami'ar Musulunci ta Imam Muhammad ibn Saud. Sannan ya karanci Akhir Tadmariyah wajen Abdullahi Ibn Jibrin, sannan ya karanci Alqur'ani wurin Ahmad Mustafa. A shekarar 1994 ya ci jarrabawar gwamnati na zama Liman.

Fara Limancin sa gyara sashe

Ya taba yin mafarki cewa ya zama limami a Babban Masallacin Makka; Bayan shekaru biyu, a shekara ta 2008, Sarki Abdullahi ya zaɓe shi don jagorantar sallar tarawihi a masallaci.

A birnin Bandu na ƙasar Japan, Al-Kalbani ya ziyarci cibiyar Minhaj-ul-Qur'an a ranar 30 ga watan Yuni, 2013.

Al-Kalbani ya ce shi ba Shaihi ba ne (Mai bada da'awa a Addinin Musulunci) amma Qari ne.

Rayuwar Sirrin gyara sashe

Yana da mata biyu da ƴaƴa goma sha biyu.

Ra'ayin sa gyara sashe

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter, al-Kalbani ya bayyana cewa rashin kasancewar ƙararrawar coci a kasar Saudiyya ya faranta masa rai.

Faɗuwar Injin ɗaukar a Makka gyara sashe

Al-Kalbani ya soki wani sakon da wani mawakin Saudiyya ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya ce Injinan da ya faɗo a Makkq "sun faɗo ƙasa a inda ake Sallah". Al-Kalbani ya ce, wannan shi ne irin wauta mafi muni. Cikin ba'a ya ba da shawarar cewa sauran injinan ba su rushe ba saboda suna da "Kyau sosai".

Al-Kalbani ya bayyana cewa Salafiyya ita ce tushen akidar ISIL.

Rabawa tsakanin Maza da Mata gyara sashe

Ya soki yadda ake raba tsakanin Mata da Maza a masallatai, inda mata suke keɓewa can wani gefe daban inda Maza basa Iya ganin suma kuma basa ganin mazan. Sai dai suje muryar Liman a Ansakuwwa (Lasifika). Ya kira wannan da "Nuna ƙyama ga mata" ("phobia of women")

Ƴan Shi'a gyara sashe

Cikin wata hira da BBC, al-Kalbani ya ayyana Shi'a goma sha biyu a matsayin masu ridda, wanda ya haifar da martani daga mabiya dariƙar Sunnah ta Saudiyya. A shekara ta 2019, sai ya janye matsayinsa bayan ya karanta wani littafi na wani ɗan’uwansa malami Hatim al-Awni, inda ya bayyana cewa, ya daina kallon waɗanda suka yi ridda a matsayin waɗanda suka “yi imani da Allah ɗaya, suna cin naman mu [halal], kuma suna yin sujada zuwa ga alƙibla.

Matsayinsa gameda kayan kaɗe-kaɗe gyara sashe

A cikin fatawar, al-Kalbani ya ɗauki waƙa a matsayin halaltacciya a shari’ar Musulunci, sai dai daga baya ya janye wannan fatawar a shekarar 2010. A shekarar 2019 ya sake canza ra'ayinsa game da waƙa inda ya sake bayyana cewa waƙa ba Haram nace a Musulunci. Al-Kalbani ya halarci taron waƙa ta addini. An zargi cewa any amfani da sarewa a lokacin gudanar da wannan waƙar.

Shiga Harkar Fina-finai gyara sashe

A cikin watan Nuwamba shekarar 2021 ya bayyana a cikin wani bidiyo na talla Combat Field - Riyadh Season 2021.

Shafin yanar gizo na waje gyara sashe

Manazarta gyara sashe

  1. Worth, Robert F. (April 10, 2009). "A Black Imam Breaks Ground in Mecca". The New York Times. Riyadh.
  2. "Former Mecca Grand Mosque's Imam: Clerics can make mistakes like politicians". Al Arabiya English (in Turanci). 2020-02-12. Retrieved 2020-08-03.
  3. Sheriff, Othman. "The First Black Saudi Imam Heads for Sierra Leone: a Rejoinder". Critique Echo. Retrieved 27 August 2020.