Abubakar Adamu Rasheed

Malami ne kuma farfesan harshen Turanci

Abubakar Adamu RasheedAbout this soundAbubakar Adamu Rasheed , MFR malami ɗan Najeriya kuma masanin ilimi da ke koyarwa da kuma kula da sashen gudanarwa, Farfesa ne shi na harshen Turanci kuma mataimakin shugaban jami'a na 9 na Jami'ar Bayero, Kano. [1]

Abubakar Adamu Rasheed
Rayuwa
Haihuwa jihar Kano, 22 ga Janairu, 1959 (65 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Malami
Imani
Addini Musulunci

Tarihin Rayuwa gyara sashe

Rasheed ya samu digirinsa na farko a fannin kere kere a jami’ar Bayero ta Kano, sannan ya kuma samu digiri a fannin fasaha daga jami’ar Nottingham sannan ya samu digiri na uku daga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. [2]

Aiki gyara sashe

Rasheed ya zama mataimakin shugaban jami’ar Bayero a shekara ta 2010, ya rike mukamin har zuwa shekara ta 2015. A shekara ta 2016, an kuma naɗa Rasheed a matsayin babban sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa. [3]

Manazarta gyara sashe

  1. http://buk.edu.ng/?q=news6
  2. "Thank you Prof. Rasheed, VC extraordinaire!". Daily Trust. Archived from the original on 2018-04-09. Retrieved 2018-04-08.
  3. "Prof. Rasheed takes over as substantive Executive Secretary". NUC. Retrieved 2018-04-08.