Abimbola Fashola
Abimbola Fashola (an haifeta 6 ga watan Afrilu a shekara ta 1965) tsohuwar Uwargidan Gwamnan Jihar Legas ce kuma matar Babatunde Fashola.[1]
Abimbola Fashola | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jahar Ibadan, 6 ga Afirilu, 1965 (59 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Ƙabila | Yaren Yarbawa |
Harshen uwa | Yarbanci |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Babatunde Fashola |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar jahar Lagos |
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Farkon rayuwa da aiki
gyara sasheAn haife ta ranar 6 ga watan Afrilu a shekara ta 1965, a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, kudu maso yammacin Najeriya. An ɗora ta a matsayin sakatariya a Kwalejin Sakatariyar Lagoon dake Legas, inda ta samu takardar difloma. Daga baya ta samu takardar shedar karatun Komfuta daga Jami’ar Legas . Tayi aiki na ɗan lokaci a matsayin ɗan jaridar dake horarwa a jaridar Daily Sketch kafin ta fara aiki da British Council a shekara ta 1987 amma ta yi murabus a 2006 lokacin da aka gabatar da mijinta Babatunde Fashola a matsayin ɗan tutar jam’iyyarsa kuma ɗan takarar gwamna na rusasshiyar jam'iyar Action Congress of Najeriya. [2][3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "My love story with gov Fashola-Lagos first lady". Mynewswatchtimesng. Archived from the original on 23 April 2015. Retrieved 19 April 2015.
- ↑ Clement Ejiofor. "Abimbola Fashola Shares Her Love Story". Legit. Retrieved 19 April 2015.
- ↑ "ABIMBOLA FASHOLA, SYMBOL OF HUMILITY". This Day Live. Archived from the original on 27 April 2015. Retrieved 19 April 2015.