Hon. Abdullahi Idris Garba dan siyasar Najeriya ne. Shi dan majalisar wakilai ne na tarayya (Nigeria), mai wakiltar mazabar tarayya ta Kontagora / Wushishi / Mariga / Mashegu.[1]

Abdullahi Idris Garba
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

11 ga Yuni, 2019 -
District: Kontagora/Wushishi/Mariga/Mashegu
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

ga Yuni, 2015 -
District: Kontagora/Wushishi/Mariga/Mashegu
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

Rayuwa
Haihuwa Kontagora, 1975 (48/49 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Rayuwar farko da Ilimi

gyara sashe

An haife shi a ranar 6 ga watan Satumba, a shekara ta alif dari tara da saba'in da biyar (1975)Miladiyya,(A.c).Shi dan asalin jihar Neja ne daga karamar hukumar Kontagora.[2]

Ya yi karatun firamare a Baptist Primary School. Sannan ya wuce Makarantar Sakandaren Gwamnati inda ya yi karatunsa na Sakandare. Ya yi karatu a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, sannan ya wuce Jami'ar Abuja. Kafin zama dan majalisar wakilai, ya kasance jami'in kula da dabbobi daga Shekarar 1992 zuwa 2006.[3][4]

Kafin zama dan majalisar wakilai, ya kasance jami'in kula da dabbobi daga shekara ta ( 1992 zuwa 2006).[3][5]

Abdullahi Idris Garba ya fara siyasa ne a lokacin da aka zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai daga a shekara ta ( 2007 zuwa 2011) sannan ya sake samun wani wa’adi a shekara ta (2011 zuwa 2015).

A zaben shekara ta (2015) ya sake tsayawa takarar majalisar wakilai ta tarayya a karkashin jam’iyyar APC.[6]

Ya zuwa yanzu, Abdulahi Idris Garba yana cikin mamba mafi tsufa a majalisar wakilai ta tarayya.

Sha'awar Doka:

Ilimi, Sufuri da Ayyuka

Membobin Kwamitin Majalisa da Shugabanci

Wakilin Tarayya a Majalisar Wakilai daga watan Mayu a shekara ta 2011 zuwa Mayu 2019

Mataimakin Shugaban Kwalejojin Noma da Kwamitin Cibiyoyin Noma (Reps) daga watan Yuni a shekara ta 2015 zuwa Mayu 2019.[7]

Shugaban Kwamitin Jama'a (Reps) har zuwa watan Mayu a shekara ta 2015

Memba na Kwamitin a Kwamitin Jirgin Sama (Reps) har zuwa watan Mayu shekara ta 2015.

Memba na Kwamitin a Tsaron Ruwa, Ilimi da Kwamitin Gudanarwa (Reps) har zuwa watan Mayu a shekara ta 2015.

Shugaban a Babban Birnin Tarayya (Reps) daga watan Yuli a shekara ta 2019 har zuwa yau.[8]

  1. "Public offices held by Abdullahi Idris Garba in Nigeria". citizensciencenigeria.org (in Turanci). Retrieved 2022-05-22.
  2. "Tribunal also upheld the election of Hon. Abdullahi Idris Garba of the CPC as member representing". Vanguard.
  3. 3.0 3.1 Nigeria, Media (2018-06-06). "Biography Of Abdullahi Garba". Media Nigeria (in Turanci). Archived from the original on 2020-08-12. Retrieved 2020-05-10.
  4. "Group disagrees with Hon. Garba over election case claims". Vanguard News (in Turanci). 2019-02-05. Retrieved 2022-02-21.
  5. "Group disagrees with Hon. Garba over election case claims". Vanguard News (in Turanci). 2019-02-05. Retrieved 2022-02-21.
  6. "Official AIG Website". repabdullahiidrisgarba.com (in Turanci). Retrieved 2018-06-29.
  7. "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". www.nassnig.org. Archived from the original on 2019-10-24. Retrieved 2020-05-24.
  8. npa2016. "Board". Nigerian Ports Authority (in Turanci). Archived from the original on 24 October 2019. Retrieved 2020-05-24.