Yomi Owope
Abayomi Owope (an haifeshi ranar 17 ga Disamba 1977) marubuci ne kuma ɗan Najeriya, mai gabatar da shirye-shiryen talabijin kuma ƙwararren mai sadarwa. Shi ne wanda ya kafa taron shekara-shekara na Mata a Aikin Jarida,[1] kuma Shugaba na NXTGEN, dandalin matasa.[2]
Yomi Owope | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 17 Disamba 1977 (47 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Yarbanci |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar jahar Lagos |
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan jarida |
Shi ne mai gabatar da shirye-shiryen talabijin na Wake Up Nigeria[3] akan TVC News daga 2017 - 2020.[4]
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheYomi ya yi makarantar firamare da sakandare a Kaduna, Najeriya, daga nan ya kammala karatunsa na digiri a fannin Turanci a Jami'ar Legas sannan ya yi digiri na biyu a fannin sadarwa daga Jami'ar Pan Atlantic.[5]
Sana'a
gyara sasheYomi Owope marubuci ne a ɗaya daga cikin manyan jaridun Najeriya, Thisday tsakanin 2001 zuwa 2003 kuma ya koma PR Agency Sesema PR a Legas, inda ya sami horon PR a ƙarƙashin marigayi Alima Atta. A 2004, ya zama Sakataren Yada Labarai na Uwargidan Gwamnan Jihar Kwara, Mrs Toyin Saraki,[6] rawar da ya taka har zuwa 2008 lokacin da ya koma gidan talabijin.
A cikin 2009, ya rubuta gami da ɗaukar baƙuncin farkon wasan kwaikwayon talabijin na, "The Debaters"[7] kuma ya sanya hannu kan wata kwangila don rubutawa da ɗaukar nauyin wasan kwaikwayon na biyu a cikin 2010. Daga nan ya rubuta zango na biyu na shirin farko na Afirka, "Moments with Mo"[8] wanda ya fara a cikin 2010 kuma ya kammala shirye-shiryen kashi-(episodes) 40 a 2011. Owope marubuci ne kuma mai bayar da sautin labari na shirin; "Next Titan Reality Show"[9]
A cikin 2013, Owope ya fara aiki tare da Makarantar Harkokin Watsa Labarai da Sadarwa a Jami'ar Pan Atlantic, da UNESCO, don ƙoƙarin inganta matsayin aikin jarida a Afirka.[10] Sannan ya ƙaddamar da Mata a aikin Jarida, taron mata ‘yan jarida a Legas, Najeriya.[11] Taron duniya ya gudana sau biyar, a cikin 2014, 2015, 2016, 2017 da 2019.
A 2013 ya sami lambar yabo ta (Innovation Award) don jagoranci da kuma kafa ƙungiyar muhawara da magana a Jami'ar Pan Atlantic da ke Legas.[12]
A watan Yuli, 2017, ya shiga TVC a matsayin mai masaukin baki na Wake Up Nigeria tare da Titi Oyinsan.[13]
A watan Oktoba, 2021, an naɗa Owope babban mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun.[14]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheYomi Owope ya auri Ayotunde, suna da ‘ya’ya uku tare.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Adie Vanessa Offiong (June 22, 2014). "Day Women in Journalism held its first conference in Lagos". Sunday Trust. Retrieved 2023-03-03 – via PressReader.
- ↑ "| First-rate Next Generation Content" (in Turanci). Archived from the original on 2022-03-08. Retrieved 2022-05-31.
- ↑ "Nigeria's first all-entertainment breakfast show, Wake Up Nigeria, makes a debut on TVC". Marketing Edge Magazine (in Turanci). 2017-07-21. Retrieved 2020-09-29.
- ↑ Ijeoma, Doris Israel (2020-07-17). "Popular TVC Presenter And Co-host Of Wake Up Nigeria, Yomi Owope Resigns". EKO HOT BLOG (in Turanci). Archived from the original on 2020-12-14. Retrieved 2020-09-29.
- ↑ "Yomi Owope | Pan-Atlantic University - Academia.edu". pau-edu-ng.academia.edu. Retrieved 2016-01-25.
- ↑ "The Wellbeing Foundation Blog - Part 2". www.thewellbeingfoundation.com. Archived from the original on 2016-01-29. Retrieved 2016-01-22.
- ↑ "11 Things You Should Know About #WakeUpNigeria Co-host Yomi Owope". Blackbox Nigeria (in Turanci). 2017-07-24. Retrieved 2020-08-13.
- ↑ "MomentswithMo | " If you can think it, you can do it ! "". momentswithmo.ebonylifetv.com. Retrieved 2016-01-22.
- ↑ "Home - The Next Titan". The Next Titan (in Turanci). Retrieved 2016-05-31.
- ↑ Oluwamuyiwa, Akinlolu. "UNESCO pledges support for women in journalism". Guardian News Website. Retrieved 2016-01-25.
- ↑ "5th Women in Journalism Africa conference holds October 5". mediacareerng.org. 31 August 2019. Archived from the original on 2019-09-07. Retrieved 2020-08-13.
- ↑ "Yomi Owope Wiki, Biography, Age, Wife, Family, Net Worth". Wiki: Biography & Celebrity Profiles as wikipedia (in Turanci). 2021-09-24. Retrieved 2022-07-14.[permanent dead link]
- ↑ "TVC Debuts New Breakfast Show #WakeUpNigeria - Blackbox Nigeria". blackboxnigeria.com. Archived from the original on 2017-09-21.
- ↑ Ambali, Fehintola (2021-10-20). "JUST IN: Dapo Abiodun Appoints Yomi Owope Senior Special Assistant" (in Turanci). Retrieved 2022-05-31.