Dapo Abiodun lokacin yana matashie
Dapo Abiodun
Gwamnan jahar ogun

29 Mayu 2019 -
Ibikunle Oyelaja Amosun
Rayuwa
Cikakken suna Dapo Abiodun
Haihuwa Iperu (en) Fassara, 29 Mayu 1960 (64 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Ƴan uwa
Abokiyar zama Bamidele Abiodun
Karatu
Makaranta Jami'ar Obafemi Awolowo
Christ's School Ado Ekiti (en) Fassara
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan kasuwa da ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress
Dapo Abiodun

Adedapo Oluseun Abiodun (an haife shi a ranar 29 ga watan Mayu shekara ta 1960) ɗan kasuwan Najeriya ne kuma ɗan siyasa, wanda ya kasance gwamnan jihar Ogun tun bayan lashe zaɓen 2019 a ƙarƙashin jam'iyyar All Progressive Congress. Dapo Abiodun shi ne shugaban hukumar kula da harkokin kamfanoni. Kafin hawansa mulki, yakkasance manajan darakta na kamfanin mai na Heyden Petroleum kuma ya kafa kamfanin First Power Limited. A ranar 10 ga Maris, 2019, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta ayyana shi a matsayin Gwamnan Jihar Ogun.[1]

 
Dapo Abiodun

An haifi Abiodun a ranar 29 ga Mayu 1960 a Iperu Remo, Jihar Ogun, ga dangin sarauta na Iperu. An haife shi a gidan Dr. Emmanuel Abiodun da Mrs. Victoria Abiodun daga Iperu Remo, a gundumar Ogun ta Gabas.[2]

Har yanzu ba a san tarihin ilimin Abiodun ba. Ya shiga cikin badakalar satifiket wajen tunkarar zaben 2015 lokacin days fito takarar sanata ya yi ikirarin cewa ya kammala karatunsa a jami’ar Obafemi Awolowo, amma a takarar gwamna a 2019 ya yi ikirarin cewa ya mallaki shaidar kammala makarantar sakandare ne kawai.

A wata hira da Seun Okinbaloye a tashoshi talabijin a watan Disamba 2018, Abiodun "Da'awar cewa bai taba samun digiri daga Obafemi Awolowo University". Ya yi ikirarin cewa shi dalibin makarantar ne amma bai kammala karatunsa a makarantar ba

Shi ne Manajan Darakta/Shugaba na Kamfanin Mai da Gas na Najeriya Heyden Petroleum Ltd (HPL). Har ila yau rahotanni sun ce shi ne ya kafa kamfanin First Power Limited.

Abiodun da dan jam’iyyar PDP ne a jihar Ogun, duk da cewa a halin yanzu dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne ya sauya sheka bayan zaben 2015. Ya tsaya takarar Sanatan yankin Ogun ta Gabas a karkashin jam’iyyar APC a zaben shekarar 2015 da ya gabata a Najeriya inda ya sha kaye a hannun dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP). An zabe shi dan majalisar dattawan tarayyar Najeriya a karkashin rusasshiyar jam'iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP) a shekarar 1998. Ya taba zama memba na kwamitocin shugaban kasa da kungiyoyi daban-daban. [3]

A 2019, ya tsaya takarar gwamna a jihar Ogun, ya kuma yi nasara, a karkashin jam’iyyar APC.

An rantsar da shi a matsayin Gwamnan Jihar Ogun a ranar 29 ga Mayu 2019. Shi Kirista ne kuma yana yin ibada a cocin mountain of fire and miracle ministry. Ya shaida cewa duk da adawar da aka yi masa na shiga ofishin gwamnan jihar Ogun saida Allah yabashi nasara.

Rigingimu

gyara sashe

A shekarar 2018, jaridar Cable ta yi zargin cewa Abiodun na da hannu wajen yin jabun satifiket.[1]

Sakamakon leken asirin Pandora Papers, Premium Times ta ruwaito yadda Abiodun ya shiga cikin wasu kamfanoni biyu na teku da aka fi sani da wurin biyan haraji, British Virgin Islands . Rahoton ya bayyana cewa Abiodun ya mallaki kuma shi ne darakta daya tilo na kamfanin Marlowes Trading Corporation da Heyden Petroleum Limited wanda hakan ya saba wa ka’idar da’ar ma’aikata da kuma dokar kotun shari’a kasancewar babu wani kamfani da aka bayyana a lokacin da aka zabi Abiodun a matsayin Gwamna. Shi kansa Abiodun ya kaucewa tambayoyi kan batun amma wani na hannun daman Abiodun ya yi ikirarin cewa gwamnan ya yi niyyar rusa kamfanonin ne amma bai lura ba har yanzu ba a rushe su ba.

A watan Maris na 2022 ne SaharaReporters ta buga tarihin yadda aka daure Abiodun a gidan yari a 1986 bisa laifin zamba a Miami Dade Florida, Amurka.

An ce gwamnan ya yi amfani da wani sunan bogi (Shawn Michael Davids) da nufin boye laifinsa.

Rahoton ya nuna cewa an daure Abiodun ne bisa laifin aikata laifukan da suka hada da zamba da katin kiredit, kananan sata da kuma na jabu.

An kama shi a ranar 7 ga Nuwamba, 1986, saboda fada da raunata wani dan sanda a kokarin da ya yi don kar a kama shi.

Yayin da ake tanyance shi a tasha, an binciki hoton yatsansa a cikin ma’adanar laifuka kuma an gano cewa Adedapo Oluseun Abiodun da Shawn Michael Davids Duk mutum daya me.

Ta haka ne aka tabbatar da laifinsa da tarihinsa kuma aka daure shi.

Wasu takardu da SaharaReporters ta samu sun nuna cewa, lambar gidan yari Abiodun itace 8600B943

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Yana auren Bamidele

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.channelstv.com/2022/06/03/i-am-not-an-emperor-dapo-abiodun-says-after-tinubus-jab/amp/
  2. https://www.vanguardngr.com/2022/06/abiodun-appoints-two-clerics-as-consultants-on-religious-matters/amp/
  3. https://dailytrust.com/i-am-not-an-emperor-dapo-abiodun-replies-tinubu