Yisa Braimoh (an haife shi a ranar 12 ga watan Agustan, a shekarar 1942) an zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa Sanatan Jihar Edo, Najeriya, inda ya karɓi mulki a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2007. Ɗan jam'iyyar PDP ne.[1]

Yisa Braimoh
mutum
Bayanai
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Shekarun haihuwa 12 ga Augusta, 1942
Wurin haihuwa jahar Edo
Yaren haihuwa Yaren afenmai
Harsuna Turanci da Yaren afenmai
Sana'a ɗan siyasa
Muƙamin da ya riƙe mamba a majalisar dattijai ta Najeriya
Ilimi a Jami'ar Cranfield da Western University (en) Fassara
Ɗan bangaren siyasa Peoples Democratic Party
Addini Musulunci
Hair color (en) Fassara black hair (en) Fassara


Braimoh ya sami ilimi a matsayin injiniya a Jami'ar Western Ontario, Ontario Canada a shekara ta 1982, Cibiyar Fasaha ta Cranefield, Cranfield, UK a shekara ta 1981 da Kwalejin Injiniya, Penzance, Cornwall UK daga shekarar 1969 zuwa 1970. Kafin zaɓen majalisar dattijai, ya kasance mai ba da shawara na musamman ga ministan sufuri da sufurin jiragen sama (1993), mai ba da shawara na musamman ga ministan wuta da ƙarafa (1994), memba na hukumar gudanarwar hukumar kula da jiragen ruwa ta ƙasa (2000) da kuma shugaba. na Hukumar Mulki ta NYSC daga 2005 zuwa 2007.[1]


Zaɓen da ya yi wa Majalisar Dattawa a cikin watan Afrilun shekarar 2007. ɗan takarar Action Congress ya ɗaukaka ƙara kan rashin bin dokar zaɓe ta shekarar 2006. Daga karshe an yi watsi da ƙarar a cikin watan Afrilun shekarar 2010.[2] Bayan an zaɓe shi Sanata, an naɗa shi kwamitocin tsare-tsare na ƙasa, haɗe-haɗe da haɗin kai, al’adu da yawon buɗe ido da sadarwa.[1] A cikin watan Afrilun, shekarar 2010, Braimoh ya yi watsi da iƙirarin da Misis Evelyn Igbafe ta jam'iyyar Action Congress ta yi wadda ta bayyana shi a matsayin "mai ɗumama kujera" kuma matalaucin wakilin mutanen gundumar sa ta majalisar dattawa.[3]

Manazarta

gyara sashe