Yair Lapid
Yair Lapid (Ibraniyawa: יָאִיר לַפִּי, IPA) an haife shi biyar 5 ga watan Nuwamba shekarar dubu ɗaya da ɗari tara da sittin da uku 1963, ɗan siyasan Isra'ila ne na jam'iyyar Yesh Atid mai tsakiya, kuma tsohon ɗan jarida. Ya kasance Shugaban Jam'iyyar adawa tun daga watan Janairu shekara ta dubu biyu da ashirin da uku 2023, bayan ya yi aiki a wannan mukamin daga shekarar dubu biyu da ashirin 2020 zuwa shekarar dubu biyu da ashirin da ɗaya 2021. Ya yi aiki a matsayin Firayim Minista na sha huɗu 14 na Isra'ila daga ɗaya 1 ga watan Yuli zuwa ashirin da tara 29 ga watan Disamba shekarar dubu biyu da ashirin da biyu 2022.
Yair Lapid | |||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
29 Disamba 2022 - ← Benjamin Netanyahu
15 Nuwamba, 2022 -
1 ga Yuli, 2022 - 29 Disamba 2022 ← Naftali Bennett (en) - Benjamin Netanyahu →
13 ga Yuni, 2021 - 1 ga Yuli, 2022 - Naftali Bennett (en) →
13 ga Yuni, 2021 - 29 Disamba 2022 - Ron Dermer (en) →
13 ga Yuni, 2021 - 29 Disamba 2022 ← Gabi Ashkenazi (en) - Eli Cohen (en) →
6 ga Afirilu, 2021 - 15 Nuwamba, 2022
29 ga Maris, 2020 - 6 ga Afirilu, 2021
16 ga Maris, 2020 - 29 ga Maris, 2020
3 Oktoba 2019 - 16 ga Maris, 2020
30 ga Afirilu, 2019 - 3 Oktoba 2019
31 ga Maris, 2015 - 30 ga Afirilu, 2019
18 ga Maris, 2013 - 4 Disamba 2014 ← Yuval Steinitz (en) - Benjamin Netanyahu →
5 ga Faburairu, 2013 - 31 ga Maris, 2015 | |||||||||||||||||||||||||||||
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Tel Abib, 5 Nuwamba, 1963 (61 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Isra'ila | ||||||||||||||||||||||||||||
Mazauni | Tel Abib | ||||||||||||||||||||||||||||
Ƴan uwa | |||||||||||||||||||||||||||||
Mahaifi | Tommy Lapid | ||||||||||||||||||||||||||||
Mahaifiya | Shulamit Lapid | ||||||||||||||||||||||||||||
Abokiyar zama | Lihi Lapid (en) | ||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||
Makaranta | Herzliya Hebrew Gymnasium (en) | ||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna |
Turanci Yaren Sifen Ibrananci | ||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan jarida, marubuci, ɗan siyasa, jarumi, mai gabatarwa a talabijin, newspaper editor (en) , ɗan wasan kwaikwayo da dan jarida mai ra'ayin kansa | ||||||||||||||||||||||||||||
Wurin aiki | Jerusalem | ||||||||||||||||||||||||||||
Employers | Yedioth Ahronoth (en) | ||||||||||||||||||||||||||||
Imani | |||||||||||||||||||||||||||||
Jam'iyar siyasa | There Is A Future (en) | ||||||||||||||||||||||||||||
IMDb | nm0487503 | ||||||||||||||||||||||||||||
yairlapid.org.il |
Ka duba wannan shafin domin sanin yanda zaka gyara wannan mukalar Koyon rubuta mukala
Akwai yuwar admin ya goge wannan shafin matukar ba'a inganta ta ba. |
Ya taba aiki a matsayin Mataimakin Firayim Minista na Isra'ila da Ministan Harkokin Waje daga shekarar 2021 zuwa 2022. Ya yi aiki a matsayin Ministan Kudi daga shekarar 2013 zuwa shekarar 2014. Lapid shine shugaban Yesh Atid. [1][2]
Kafin ya shiga siyasa a shekarar 2012, Lapid marubuci ne, mai gabatar da talabijin kuma mai ba da labarai. Jam'iyyar Yesh Atid mai tsakiya, wacce ya kafa, ta zama jam'iyya ta biyu mafi girma a Knesset ta hanyar lashe kujeru sha tara 19 a Zaben majalisa na farko a shekarar 2013. Sakamakon da ya fi girma fiye da yadda ake tsammani ya ba da gudummawa ga sunan Lapid a matsayin jagora mai tsakiya.
Shekarar 2013 zuwa shekarar 2014, biyo bayan yarjejeniyar hadin gwiwa tare da Likud, Lapid ya yi aiki a matsayin Ministan Kudi a karkashin Firayim Minista Benjamin Netanyahu . A cikin shekarar 2013, Lapid ya kasance na farko a cikin jerin "Yahudawa mafi tasiri a Duniya" ta hanyar The Jerusalem Post . An kuma san shi a cikin shekarar 2013 a matsayin daya daga cikin manyan masu tunani na manufofin kasashen waje na duniya, kuma an sanya shi a matsayin daya cikin ɗari 100 na mujallar Time "Mutanen da suka fi tasiri a Duniya". Ya yi aiki a Kwamitin Harkokin Waje da Tsaro na Knesset, da kuma Kwamitin leken asiri da Ayyukan Tsaro.
ranar sha bakwai 17 ga watan Mayu shekarar 2020, Lapid ya zama Shugaban Jam'iyyar adawa, bayan da aka rantsar da Gwamnatin Isra'ila ta talatin da biyar. A ranar biyar 5 ga watan Mayu shekarar 2021, ya fara tattaunawa da wasu jam'iyyun don kokarin kafa gwamnatin hadin gwiwa. A ranar biyu 2 ga watan Yuni shekarar 2021, Lapid ya sanar da Shugaban Isra'ila Reuven Rivlin cewa ya amince da gwamnatin juyawa tare da Naftali Bennett kuma yana shirye ya maye gurbin Firayim Minista mai ci, Benjamin Netanyahu . An rantsar da sabuwar gwamnati a ranar sha ukku 13 ga watan Yuni shekarar 2021.
Lapid zama Firayim Minista na Isra'ila a ranar 1 ga Yulin 2022 bayan Bennett ya sauka a matsayin Firayim Ministan bayan rushewar Knesset. Lapid ya kasance Firayim Minista har sai an kafa sabuwar gwamnati bayan zaben Nuwamba shekarar 2022.
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://www.nytimes.com/2013/01/23/world/middleeast/yair-lapid-guides-yesh-atid-party-to-success-in-israeli-elections.html?_r=0
- ↑ https://www.timesofisrael.com/liveblog_entry/lapid-says-wont-join-problematic-emergency-government-but-hell-back-it-from-outside/
- ↑ "Leader of the Opposition". Knesset. Retrieved 13 January 2023.
- ↑ "Dreams of the father guide Yair Lapid as he eyes Israel's premiership". France 24. 1 June 2021. Archived from the original on 3 June 2021. Retrieved 3 June 2021.
- ↑ Jerusalem Post staff (4 May 2013). "Top 50 most influential Jews 2013: Places 1–10". The Jerusalem Post. Archived from the original on 24 December 2017. Retrieved 5 August 2013.