Jami'ar Dan Dicko Dankoulodo ta Maradi ( UDDM ) jami'a ce ta Jamhuriyar Nijar da ke birnin Maradi . Ta fara ne a cikin 2008 tare da kwalejin fasaha ta jami'a (IUT).

Jami'ar Dan Dicko Dankoulodo de Maradi

Bayanai
Iri jami'a da quarter of Niger (en) Fassara
Ƙasa Nijar
Tarihi
Ƙirƙira 2008
uddm.edu.ne

A shekarar 2016, UDDM tana da ma'aikata kimanin 87; inda 65 daga cikinsu malaman jami'a ne masu bincike, 22 kuma malamai masana fasaha. Bancin hakan akwai ma'aikatan tallafi na fasaha (PAT) da dalibai 3 325 (560 daga cikinsu mata ne).

Tarihi gyara sashe

Jami'ar Dan Dicko Dankoulodo Maradi an kirkire ta ne ta hanyar Doka mai lamba 2014-49 ta16 Oktoba na 2014  ; Bayan gyare-gyare na Jami'ar Maradi da wadda ita kuma aka kirkire ta da doka mai lamba 2010-40 11 ga watan Yuli, 2010 . Tsarin horarwar sun kunshi fannoni uku, kwalejin fasaha da kuma sassan bincike.

Horon da ake bayarwa gyara sashe

  • Matakin Horo na Bac + 2: Difloma na Jami'a kan Fasaha (DUT)
  • Matakin Horo na Bac + 3: Digiri wato Bachelor kan Kimiyya (Licence)
  • Matakin Horo na Bac + 5: Digiri na biyu na Sana'oi da binciken kimiyya (Master)
  • Matakin Horo na Bac + 8: Digirin digirgir wato Doctorate (PhD)

Tsarin Jami'a gyara sashe

Jami'ar Fasaha ta IUT gyara sashe

Fannin Kimiyya da fasaha FST gyara sashe

Fannin Noma da Muhalli FASE gyara sashe

Aji-aji na bincike daban-daban UMR gyara sashe

Dangantaka da wasu Jami'ai na Duniya gyara sashe

Jami'ar Dan Dicko Dankoulodo da ke Maradi tana cikin haɗin gwiwa tare da cibiyoyin ƙasa da na ƙasa da yawa da sauransu :

Diplomas da ake bayarwa a Jami'ar UDDM yana samun karbuwa daga CAMES [1] .

Manazarta gyara sashe