Soyayya abace wadda take da matukar mahimmanci acikin kowacce irin al'umma danhaka mu hausawa muna masu tsananin jindadin soyayya musamman wacce aka ginata akan doron gaskiya, soyayya itace take gyarawa mutum tarbiyyarsa, mu'amalarsa, da addininsa, kuma; ita asalinta tan fara fadawa zuciyane ta hanyar gani. Soyayya halittace da Ubangiji subhanahu wata'alah ya halicceta sannan ya dasata a zuciyar duk wata hallitta mai rai. Zamu iya kasa soyayya gida-gida kamar haka: 1. Soyayyar ma'aiki annabi muhammad sallahu alaihi wasallam, Ahlinsa da sahabbai. 2. Iyaye. 3.'yan Uwa. 4. Malamai. 5. Abokai ko kawaye 6. sanna kuma ma'aurata

Wikidata.svgSoyayya
advanced emotion (en) Fassara
DickseeRomeoandJuliet.jpg
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na condition (en) Fassara, affection (en) Fassara da emotion (en) Fassara
Bangare na theory of emotion (en) Fassara da Psychology (en) Fassara
Hashtag (en) Fassara love
Has quality (en) Fassara intimacy (en) Fassara
Hannun riga da hatred (en) Fassara da apathy (en) Fassara
Duka wadannan idan da baka sami soyayyarsuba to ina tabbatarmaka dacewar, baka samu jin dadin rayuwar da Allah (S W T) ya halicceka acikintaba.

Da babu soyayya a zukatan mu, da baka sami tallafi da tarbiyyaba daga iyayeba, da bakagane cewar kana da muhimmanciba daga 'yan,uwanka, da baka sami kyakkyawar mu'amala daga abokaiba, da baka sami tallafi, tausayi, da taimako daga mijinki ko matarkaba. Dan haka ga duk mutumin da yatsinci kansa awanna fili na doron duniya kuma yakejin cewar yanayin rayuwa mai kyau to koshakka babu yaci karo da soyayyar wadannan abubuwan dana lissafa. Zandan tsaya anan nadan sharuwa kafinnacigaba. Daga Ado Haruna Nauwas.