Tuwon masara

Abincin Arewa wanda aka fi sani da hausa fufu. Tuwo masara ana yin shi ne daga masarar ƙasa

Tuwan masara, dai abinci ne na gargajiya mai dadadden tarihi, kuma mafi akasarin 'yan kasar musamman 'yan Arewacin Nijeriya musamman ma Hausawa ke cin shi, kuma akan hada shi ne da miyar kuka. Ana kuma matukar girmama shi tun daga karni na baya har zuwa yau ana amfani da wannan abincin. Yadda ake hada shi kuma shi ne akan samu masara bayan an same ta, sai a wanke a surfa,a kuma bakace dussar, wadda shi ma a kan sayar ga masu kiwon dabbobi. Bayan an bakace sai kuma a nika shi ya zama gari.To daga nan kuma sai girki. A sanya ruwan zafi ya tafasa har dai a kai ga tuka shi. Shikenan sai a rinka tukawa har ya yi kauri, shi ne ya zama tuwo kenan. Ana cin shi da kowace irin miya, amma an fi cin shi ne da miyar kuka a Arewacin Nijeriya wanda tun a baya da ita ake amfani sai kuma miyar kubewa.[1][2][3][4][5].

Tuwon masara
Tuwo
Kayan haɗi tuwon masara
Tarihi
Asali Najeriya
hoton tuwon massara
Shikan masara
Tsabar masara
Garrin wasara

Bibiliyo gyara sashe

  • Adamu, Abdalla Uba, 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Hausa home videos : technology, economy and society. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004. ISBN 978-36906-0-4.OCLC 61158034.
  • Abubakar Aliyu Mohammed. Cultural Torism. ISBN:978-978-087-937-2

Manazarta gyara sashe

  1. https://bakandamiya.com/blogs/1229/96/tuwon-masara?mobile=0[permanent dead link]
  2. https://cookpad.com/ng/recipes/13378123-tuwon-masara?via=search&search_term=tuwon%20masara
  3. https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/10/karanta-jerin-abincin-hausawa-kafin-zuwan-yar-thailand-kafin-zuwan-shinkafa-yar-kasashen-waje-girke-girken-gargajiya-sunayen-abincin-gargajiya-abincin-zamani-filin-girke-girke-abincin-zamani-filin-girke-girke.html
  4. https://cookpad.com/ng/search/tuwon%20masara
  5. Adamu, Abdallah Uba, 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Hausa home videos : technology, economy and society. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004. p. p 473-475 ISBN 978-36906-0-4.