Turare
Turare: Turare wasu chakudaddun sinadarai ne masu kamshin dadi. Wadanda ake narke su gami da hade su guri daya tare da ruwa, don su bada cikakken kamshin da ake so, da dai sauran gyare-gyare bayan an gama hada su ana amfani dashi turaren don kamsasa jiki, na mutane ko na dabbobi har da tufafi da masallatu da majami'u don samun gamsasshen kamshi.
Turare | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | Kwalliya da aroma compound (en) |
Bangare na | cosmetic terminology (en) |
Amfani | pleasantness (en) da hiding (en) |
Ƙasa | no value |
Shafin yanar gizo | no value |
Shi Kuma Turare tun fil'azal ana amfani dashi kowane zamani da yadda suke yin nasu ya danganta da yanayin cigaban fasaha da ilimi. Misali yanzu yadda ilimi musamman na tekanolaji ya samu a duniya, ansamu babban ci gaba.
Ire-iren Turare
1. Akwai turare oyel (oil) 2. Akwai na jiki (body spray) 3. Akwai turaren hayaki na iche (insence) 4. Akwai turaren Humra na Amare da dai sauran su.
Turare yanada muhimmanci sosai ga rayuwar dan Adam babu addinin da ya haramta amfani da turare illa dai ma wasu Addinan sun maida shi a matsayin da sunna mai kyau, kamar Addinin Musulunci turare yanada muhimmanci sosai gareshi. [1].
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Matsayin musulunci kan sanya turare a al'aurar mace". BBC Hausa. 23 January 2018. Retrieved 1 July 2021.
.