Tunde Eso
Tunde Eso (an haife shi a ranar 16 ga watan Agusta shekara ta alif dari tara da saba'in da bakawai 1977) ɗan jaridar Nijeriya ne, mai sharhi kan zamantakewar al'umma, masanin alaƙar jama'a da kuma mai buga Jaridar Findout. [1] Shi dan takarar Gwamnan ne a jam'iyar people Democracy Party (PDP) a Jihar Osun .[2][3][4] Eso shine wanda ya kafa Youthocracy; sabon tsarin mulki, shugaban kungiyar Fix Nigeria Group kuma marubucin littattafan Maganar Tsaro na Afirka da kuma Burin Afirka. [5]
Tunde Eso | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Ilesa, 16 ga Augusta, 1977 (47 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Yarbanci |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Ilimi, Winneba |
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa da ɗan jarida |
tundeeso.com |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheEso an haife shi kuma ya girma a Ilesha, Jihar Osun, kuma ya fito daga zuri'ar Pa Obafemi da Iyabode Eso (née Fanibe) a ranar 16 ga watan Agusta shekara ta alif dari tara da saba'in da bakawai 1977. Ya yi karatun lissafi don takardar shaidar difloma ta kasa a Kwalejin Fasaha ta Jihar Osun, Esa-Oke, a shekara ta 2005. Ya sami digiri na farko a Kimiyyar Siyasa a Jami'ar Ilimi, Winneba, Ghana .[2][6][7]
Ra'ayin Siyasa
gyara sasheA wata hira da jaridar Guardian ta Najeriya, Eso ya ce tsofaffin ‘yan siyasa za su ci gaba da yin watsi da matasan Najeriya har sai matasa sun fahimci cewa su ne mafi mahimmancin yawan masu jefa kuri’a. Ya nuna cewa karfin na yara ya isa ya zabi daya daga cikin matasan Najeriya tare da shirye-shiryen kwarewa. A ra'ayin Eso, gwamnatocin da suka gabata sun yi watsi da matasan Najeriya. [8] Ya kuma yi imanin cewa lokaci ya yi da za a gina shugabanni da tunani da ayyukan da suka dace, shugabannin da ba za su yi yaƙi don aljihunsu kawai ba, shugabannin da za su yi tunanin wasu kuma ba su kaɗai ba. [9] A nasa ra'ayin, ana bukatar shigar da matasa cikin siyasa don magance matsalolin rashin tsaro a Najeriya. [10]
Youthocracy
gyara sasheA shekarar 2013, Eso ya kirkiro wani sabon tsarin gwamnati mai suna Youthocracy wanda ya fassara shi da 'Gwamnatin mutane, ta matasa da kuma ta mutane' a cikin littafinsa mai taken Vision for Africa ; ya kara bayyana cewa dalilansa shi ne samar da damar siyasa ga matasa don su kasance masu dacewa a siyasar Najeriya, saboda haka bukatar da tayi daidai da Youthocracy wanda ke shirin karbe mulki daga Demokradiyya kamar yadda ya zanta da jaridar The Nation .
Manazarta
gyara sashe- ↑ "We need new ideas in governance – Tunde Eso". The Nation Newspaper (in Turanci). 2017-10-09. Retrieved 2019-08-14.
- ↑ 2.0 2.1 Adebisi, Yemi. "Why I Want To Become Osun's Next Governor". Independent. Nigeria: Independent News. Archived from the original on 10 March 2017. Retrieved 12 January 2017.
- ↑ Admin. "Addressing security challenges in Africa". Vanguard. Retrieved 12 January 2017.
- ↑ Dike, Ada (29 June 2015). "Eso explains why he wrote the book 'African Security Solution'". Adadke Blog. Retrieved 12 January 2017.
- ↑ Eso, Tunde (6 August 2012). African Security Solution. Strategic Insight Publishing. Samfuri:ASIN.
- ↑ admin. "About Tunde eso". Tunde Eso. Archived from the original on 16 January 2017. Retrieved 12 January 2017.
- ↑ "Tunde Eso". The Achievers. Archived from the original on 21 June 2010. Retrieved 7 February 2011.
- ↑ "We'll Make Osun Great – Tunde Eso", Daily Dispatch, 2 February 2017.
- ↑ Edo, Tunde, "Ends of a Good Nation", Daily Dispatch, 2 April 2017.
- ↑ Eso, Tunde, "Solving Nigeria’s insecurity challenges with youth integration", The Guardian (Nigeria), 19 March 2015.