Tulu jam'in kalmar itace Tuluna, Tulu dai wani kayan amfani ne wanda ake amfani dashi a gida musamman don aje ruwa da kuma zuwa rafi ɗauko ruwa daga rafi ko kuma a Rijiya. Sai dai yanzu ba'a cika amfani da tulu ba a birane sai dai a ƙauyuka, to amma irin Zamfara, Sokoto, Kebbi da sauran jihohin arewa da Nijar duk ana amfani da tulu.[1][2]

Tukunyar Kasa wadda aka fi sani da Tulu

Yadda ake yin Tulu

gyara sashe

Anayin tulu ne da ƙasa wato yanɓu mai laushin, ana zuwa ne a nema yanɓu mai laushin da kyau sai a ɗibo azo a kwaɓa da ruwa sai a fara gina tulu da duk abinda ake so a gina bayan an gama ginawa ya bushe sai kuma a samo ciyawa busasshiya a sa wuta a gasa shi saboda yayi ƙarfi. Yadda dai ake yin randa shima haka akeyin tulu duk da da tulu da randa banbanci su baida yawa tulu yanada ƙaramin baki sai kuma ana ɗibo ruwa da tulu a rafi ita kuma randa sai dai a girke ta waje ɗaya don zuba ruwa duk da shima tulu akan ajeshi don ajiye ruwa. Hausawa suna wani Karin magana da tulu ga yadda karin magana yake "ƙadangaren bakin tulu a barka ka ɓata ruwa a kashe ka a fashe tulu" ma'ana idan wani yazamewa wani ƙarfen ƙafa.[3]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Tulu/Tuluna". Hausadictionary.com. 10 August 2020. Retrieved 16 September 2021.
  2. "sana'ar gini". rumbunilimi.com.ng. Archived from the original on 21 October 2021. Retrieved 16 September 2021.
  3. "Matar da ta zamewa masu aikata laifi a Kenya ƙadangaren bakin tulu". BBC Hausa.Com. 21 January 2021. Retrieved 16 September 2021.