Karin magana

Hikima a Zance

Karin magana magana ce ko zance da hausawa kan yi wanda ke dauke da hikima da basira aciki, domin yin hannunka mai sanda da huce takaici akan wani abinda aka yi maka. Masana Harshen Hausa sun fassara karin magana gwargwadon fahimtarsu. Daga ciki akwai: Farfesa Ɗangambo (1984) da ya ce, “Karin magana dabara ce ta dunƙule magana mai yawa a cikin zance ko ‘yan kalmomi kaɗan, cikin hikima”.

AsaliGyara

“Karin Magana Tsararren zance ne wanda yake zuwa a gajarce na hikima da zalaƙa tare da bayar da ma’ana gamsasshiya, mai faɗi, mai yalwa, musamman idan aka tsaya aka yi bayani daki-daki”. Kenan idan aka lura sosai, za a ga cewa ita karin magana, magana ce dunƙulalliya wacce ba kowa ne zai iya gane ta ba tare da an yi masa cikakken bayani ba. Amma yau da gobe da kuma yawan amfani da ita, musamman a zamunan da suka shuɗe, da ake yawan tsarma ta a cikin zance, sai ya zama shi Bahaushe yana iya gane abinsa. Misali, ana iya yiwa mutumin da bashi da tattali nuni cikin ‘yan kalmomi marasa yawa, kamar a ce da shi, wannan abin da ka ke yi zai hana ka farcen susa. Ko kuma idan ana son yin magana game da wani abu mai amfani da kuma maras amfani. Kamar a ce idan an aikata abin, wani abu maras daɗi zai faru da wanda ya aikata, to ana iya yi masa nuni ta hanyar cewa da shi, wannan abin ba zai haifar maka da ɗa, mai ido ba. Da sauransu. Kowace ɗaya aka ɗauka daga cikin waɗannan karin magana guda biyu, za a taras cewa maganganu ne dunƙulallu, waɗanda idan aka tashi farfasa su, za su ci guri mai yawa. Amma idan aka faɗe su da baki ko aka rubuta su, za a ji su ko a gan su gajeru, sannan kuma shi wanda ake magana da shi zai iya fahimtar abin da ake nufi.[1] Karin magana zance ne a dunƙule k a karye, wacce aka tsakaita ta ta hanyar karya magana, wacce ake faɗa yau da gobe domin isar da saƙon hikima da hankalta ga wanda aka faɗamawa acikin harshen hausa.[2]  kamar ace “ Karen Bana Shike Maganin Zomon Bana” ko “Ra’ayi Riga ce” ko “ Tafiya Sannu Sannu Baya Hana Kwana Nesa”. “ Abinda Babba Ya Hango Yaro Ko Ya Hau Rimi Ba Zai Hango shi Ba” ko ace “Sara da sassaƙa ba sa hana gwamji toho”.

SifaGyara

Karin magana nada banbanci da wasu hikimomin magana na hausawa kamr su habaici, zambo, Kirari, Take, wanda wadannan daban suke da karin magana,[2] Kuma karin magana wani nau’i ne na azancin magana da harshen hausa, ba tare da ka tsawwala ma mutum ba ta sigar magana ko tawaita masa ba a cikin zance, amman ta hanyar amfani da karin magan zaka isar da saƙo a sauƙaƙe ko a fahimce.

Sigar sauyiGyara

Karin magana takan zo a sigar tambaya, habaici ko azanci, sannan takan zo a sigar misali kamar karin maganar da ake cewa “ Ina ganin Kura da Rana/ yaya zan yarda ta cije ni?” wannan karin maganar tazo ne a sigar tambaya, amma ba a buƙatan wanda aka gaya ma karin maganan da ya bayar da amsa, kamar yace eh! Ko A’ah!, amman zai iya bayar da amsar ta sigar mayar da baƙan magana ko raddi, misali “Mallam Musa yaga alamun cewa Mallam Shehu naso ya ara fatanyarshi yaƙi dawo masa da kayansa, sai yace ma Mallam Shehu “ Ina ganin Kura Da rana, Taya zan yarda ta cijeni?” ma’ana ba zi yarda Mallam Musa ya mai wayo ba ya ara fatanyar sa ya cuce shi ba, Shi kuma Mallam Shehu da yin karin maganan ya fahimci cewa Mallam Musa ya gane, amman tinda al’amari ne wanda ba a fili yakeba na cewar tabbas cutarshi zai yi ba, sai shi kuma ya mayar masa da baƙar magana, ta hanyar cewa “ ba kura bace zaki ne” kaga a nan kamar ya amsa ga tambayar karin maganan ne, amman kuma bada amsawa, a wannan misali amsa tamabayan karin magana ta sigar tambaya ba laifi bane, amman galibi ba a amsawa sai dai a amsa ta sigar baƙar magana, zambo, ko habaici.

Karin Magana Mai Siffar Tambaya.Gyara

1-     Ƙasa ta gudu ta je ina?

2-     Ina ganin kura da rana ta yaya zan yarda ta cijeni?

Karin Magana Mai Siffar MisaliGyara

1-     Wanka da gari baya maganin yunwa.

2-     Mushen tinkiya tafi yankakken biri.

3-     Na shiga ban ɗauka ba, bata fidda ɓarawo.

4-     Wankan wuta sau guda ka yafa.[3]

Wasu Karin MaganaGyara

1-     Hadarin ƙasa, maganin mai kabido.

2-     Gobara daga kogi.

3-     Hakuri maganin  zaman duniya.

4-     Ana kukan karaya ga mutuwa tazo.

5-     Kome nisan daji, da gari gabansa.

Canjin sigar Karin MaganaGyara

A karin magana ana cewa “ hadarin ƙasa, maganin mai kabido”  ida ɗan dambe ya furta hakan kamar ya na yiwa abokin takararsa habaici ne, kamar yace “sai ni hadarin ƙasa, maganin mai kabido”. [4]

Amfani da HikimaGyara

 1. Taƙaita doguwar magana.
 2. Nuni, gargaɗi, da faɗakarwa cikin nishaɗi, sannan kuma a taƙaice.
 3. Bayyanar da ƙwarewa da fasahar Bahaushe wajen iya magana.
 4. Adon harshe. Abin da ake nufi da adon harshe a nan, shi ne cewa karin magana yana ƙarawa zance kyau da kuma daɗi.[5]

MisalaiGyara

 • Kowane bakin wuta, da nashi hayaki
 • Komai tsufan zaki, ya fi saurayin kare
 • Komai jarabar bunsuru, ya kiyayi matar kura
 • Komai nisan jifa, Ƙasa zai faɗo
 • Wuta da Aljanna duka na Allah ne. Inji mai sabo
 • Duk wanda ka gani a inuwa, ba ta can faro ba.
 • Idan ka ji wane, ba banza ba.
 • Taya taito, yafi ban cigiya.
 • Rashin jini, rashin tsagawa.
 • Idan kaga ki gudu, sa gudu ne bai zo ba.
 • Da mai rai ake rikicin duniya
 • Aikin banza, antura agwagwa ruwa

BibiliyoGyara

 • The Hausa world of Rudolf Prietze : being the complete collection of the scholar in the Hausa and German originals and the English versionsISBN978-125-659-1OCLC950033236
 • Ahmed, Umaru Balarabe,. The Hausa World of Rudolf Prietze being the complete collection of the Scholar in the Hausa and German originals and the English versions. Volume 2. Zaria. ISBN 978-125-653-2. OCLC 992986877.
 • Aminu, Alhaji Ayuba. (1998). Kacici-kacici. Dukku, Malam Bello., Mu'azu, Mohammed Aminu. (1. publ ed.). Maiduguri: Compaq Publ. ISBN 978-32300-4-2. OCLC 634309537.
 • Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. ISBN 978-1-4744-6829-9. OCLC 648578425.
 • Dikko, Inuwa. (2006). Ruwan bagaja : wasan kwaikwayo. Zaria: Northern Nigerian Pub. ISBN 978-978-169-143-0. OCLC 232270270.

ManazartaGyara

 1. https://rumbunilimi.com.ng
 2. 2.0 2.1 Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute.p. 70
 3. Skimner (1988),(p238,239 and p73)
 4. Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute.p. 73
 5. https://rumbunilimi.com.ng