Anthony Kan Onwordi wanda aka fi sani da Toni Kan (an haife shi 11 ga Yuni 1971) marubuci ɗan Najeriya ne, edita, babban jami'in hulda da jama'a, kuma malami. Shi ne marubucin tarin gajerun labarai, Nights of a Creaking Bed, wanda aka lura da shi don bincika jigogi a kan jima'i na Afirka, kuma Cassava Republic Press suka buga. Shi ne ya lashe kyautar adabin NDDC /Ken Saro Wiwa, wadda kungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA) ta bayar a shekarar 2009. [1]

Toni Kan
Rayuwa
Haihuwa 11 ga Yuni, 1971 (53 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Lagos
Jami'ar Jos
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a marubuci da Malami

Kan ya karanci adabin turanci a jami'ar Jos sannan ya sami digiri na biyu a fannin adabin turanci a jami'ar Legas a shekarar 1999, inda ya kammala a matakin farko. Ya zama editan mujallu yana da shekaru 26. [2]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Toni Kan wins the NDDC/Ken Saro-Wiwa prize" Archived 2016-03-04 at the Wayback Machine, Cassava Republic Press, 2 November 2009.
  2. Admin (26 October 2014). "Toni Kan: I have always wanted to write about Lagos". This Day. Archived from the original on 7 December 2014. Retrieved 5 November 2014.