Stephen Oru
Stephen Orise Oru ɗan siyasan kasar Najeriya ne, kuma tsohon Ministan Neja Delta ne na Tarayyar Najeriya dake Abuja.
Stephen Oru | |||
---|---|---|---|
2010 - 2011 ← Ufot Ekaette (en) - Peter Godsday Orubebe → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Ughelli, | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Ohio State University (en) Jami'ar Ahmadu Bello | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Stephen Oru a Jihar Delta, a karmar hukumar Ughelli North LGA Ya halarci Kwalejin Gwamnati, Ughelli . Ya sami digiri na farko a fannin fasaha a shekarar 1974 sannan ya sami digiri na biyu a fannin ilimi a shekarar 1976 a Jami'ar Ahmadu Bello . Ya ci gaba da karatunsa a Amurka inda ya sami digiri na uku a Jami'ar Jihar Ohio, Columbus, Ohio a shekarar 1978
Sana'a
gyara sasheOru ya fara harkar siyasa ne a shekarar 1982 tare da jam’iyyar National Party of Nigeria (NPN) a matsayin Sakataren Matasa, dake Ughelli LGA, Jihar Bendel. Tun daga lokacin ya rike mukamai daban-daban a fagen siyasar Najeriya; wasu daga cikinsu sun hada da: