Dattijo Peter Godsday Orubebe (an haifeshi ranar 6 ga watan Yuni, 1959). An naɗa shi ministan Neja Delta ranar 6 ga watan Afrilu, 2010 a lokacin da shugaban riƙo Goodluck Jonathan ya sanar da sabon hukuma.[1]

Peter Godsday Orubebe
Minister of Niger Delta (en) Fassara

2011 - 2015
Stephen Oru - Usani Uguru Usani
Rayuwa
Haihuwa Burutu, 6 ga Yuni, 1959 (65 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar jahar Lagos
Jami'ar Ambrose Alli
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Farkon rayuwa da Karatu

gyara sashe

An haifi Orubebe a ranar 6 ga Yuni 1959 a Ogbobagbene, karamar hukumar Burutu a jihar Delta. Shi dan asalin Ijaw ne. Ya halarci Jami'ar Legas, inda ya sami B.Sc. a kimiyyar siyasa a 1985. Daga baya ya sami digiri na biyu a kan alakar kasashen duniya daga Jami'ar Ambrose Alli, Ekpoma a 2005.[2]

Harkar siyasa

gyara sashe

Orubebe ya zama kansila mai kulawa, sannan daga baya ya zama shugaban Karamar Hukumar Burutu. A watan Yulin 2007, Shugaba Umaru 'Yar'Adua ya naɗa shi Ministan Ayyuka na Musamman. Daga baya ya zama karamin Ministan harkokin Neja Delta lokacin da aka kirkiro wannan ma'aikatar a watan Disambar 2008.[3] A watan Janairun 2010, ya ce manufar samar da kashi 10 cikin 100 na raba hannun jari a kan ayyukan raya kasa a yankin Neja Delta zai sa barna da rikici su zama tarihi.[4]

A ranar 31 ga Maris, 2015, Orubebe, a matsayin wakili ga PDP, ya yi yunkurin kawo cikas ga yadda aka gudanar da tattara sakamakon zaben shugaban kasa na shekarar[5] 2015 . Orubebe ya yi zargin cewa Shugaban INEC, Attahiru Jega, ya bi sahun babbar jam’iyyar siyasa ta adawa, APC[6][7] . Amma daga baya ya nemi afuwar 'yan Najeriya game da halinsa ta hanyar ba da uzurin da ba a manta da shi ba yana roƙonsu da kada su bi sawunsa tare da bayyana cewa ya yi nadamar abin da ya yi.[8]

Manazarta

gyara sashe